Wakar “Ranar Kilishi Jikar Dikko” ta Mamman Shata Katsina

Hajiya Kilishi Usman Nagogo

Wannan waka, mai amshin “Ranar Kilishi Jikar Dikko”, Mamman Shata ya rera ta ne ga Hajiya Kilishi, matar Sarkin Daura Muhammadu Bashar (Allah ya jikan shi). Jigon wakar shi ne kambamawa da yabo. A wakar, Shata ya tuno da yadda aka yi bikin auren Kilishi (diyar Sarkin Katsina Usman Nagogo) da Bashar lokacin ya na Wamban Daura.

Wannan wakar, gajera ce, to amma ta kunshi abubuwa da yawa. 1. Ta nuna cewa sarakuna a kasar Hausa na auratayya tsakanin su; 2. ta nuna kasaitar wannan bikin aure, wato irin babban taron da aka yi na jama’a da motoci da babura da kekuna, da kuma yadda sarakai ke yin babbar kyauta ga maroka ko mawakan su; 3. ta taskace mana tarihin al’adar “durbar” da Turawa su ka kawo mana, wato hawan dawakai domin nuna al’adun mu; 5. wakar ta bada tarihin ita Kilishi a takaice, wato Shata ya nuna mana cewa ita ‘yar Sarki ce jikar Sarki; 6. a wakar akwai nason addinin Musulunci, musamman bangaren karatu da kuma tarihi. Misali, mun fahimci cewa Shata ya san wani abu game da wasu wakokin Larabci, wato irin “Alburda”, da mawakan Larabci irin su Alfazazi.
Na rubuta wakar ne daga wani faifan Shata da na saurara.
Na alamta inda aka yi amshi da alamar tauraro, wato *. Bismilla.

SHATA: Ranar Kilishi jikar Dikko.

AMSHI (*)

Ranar Kilishi jikar Dikko.
*

Bukin Kilishi jikar Dikko,
Taron ta sai ka ce an Durbar:
Mota dubu ta je tarbar ta,
Doki dubu ya je tarbar ta,
Dike dubu ya je tarbar ta,
Ba sa’ikul ba, ba ‘yan ƙas ba,
Tarbar Kilishi jikar Dikko.
*

Rad da Wamban Daura jikan Abdu,
Mamman jikan Sarki Musa,
Jikan Muska da Sarkin Fada,
Jikan Muska da Sarkin Fada,
Ran nan Wambai yab ban mota,
Yac ce don darajar ɗan Hamza,
Sardo Amadu jikan Shehu,
Sai ko Kilishi ta ce ita ta ba ni domin Amadu jikan Shehu.
*

Daidai, Kilishi jikar Dikko!
*

Kilishi Allah ya ba ki ladan aure,
Da ma ki san gidan Aljanna.
*

Da sauya waƙar Kilishi jikar Dikko,
Yara su na ta dukan fata,
Kiɗan sai ka ce fitah harsashi!
*

Zuba waƙa ni kai,
Ni sai zuba waƙa ni kai kama da ta Alfazazi,
Kamar ana tamsiri.
*

Zuba waƙa ni kai kama da ta Alfazazi,
Kamar ana Alburda.
*

Ta Tatsumburum garin Ɗanyaro,
Waccan Kilishi jikar Mamman,
Waccan Kilishi jikar Mamman,
Wannan Kilishi birnin Dikko,
Wannan Kilishi birnin Dikko,
Kakan ta Shehu ne Usumanu,
Baban ta Shehu ne Usumanu,
Kakan ta kau Muhamman Dikko.
*

Kilishi kakan ta kau Muhamman Dikko.

*

Kilishi kakan ta kau Muhamman Dikko.
*

Allah ya ba ki ladar aure,
Da ma ki san gidan Aljanna.
*

Daidai, Kilishi jikar Dikko.
*

Taron Daura ya kai taro,
Taron Daura ya kai taro,
Bukin Kilishi jikar Dikko.

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *