Wai wannan shi ne zabe?

BABU shakka, duk wanda ya kalli yadda aka aiwatar da za~en fidda gwani na takarar zama shugaban a jam’iyyar PDP zai ce lallai an yi za~en bisa adalci. Dalili, tun da farko sai da aka tantance dalaget-dalaget ]in da su ka zo domin yin za~en, aka ba su takardu, duk a gaban wakilan ’yan takarar guda uku, wato Shugaban {asa Goodluck Jonathan da tsohon mataimakin shugaban }asa Alhaji Atiku Abubakar da kuma Madam Sarah Jibril; na biyu, a bainar jama’a aka ri}a jefa }uri’a, kuma a cikin akwatin roba wanda kowa na iya ganin abin da ke cikin shi; ita ma }idayar }uri’un a bayyane aka yi ta; sannan a gaban wakilan ’yan takarar aka yi komai, har ma su na da damar tofa albarkacin bakin su idan su ka so yin hakan. Su kan su ’yan takarar, an gayyace su zuwa taron za~en fidda gwanin da aka yi a dandalin Eagle Square, Abuja, inda su ka fa]a wa duniya aikin da za su yi wa jama’a idan an za~e su. Bugu da }ari, an watsa dukkan sha’anonin taron kai-tsaye ta hanyar tashoshin talabijin na NTA da AIT, wa]anda ana kama su a ko’ina a duniya. Hakika, da wuya ka kalli wannan tsari ka ce abin bai burge ka ba.

To amma abin tambaya shi ne: da gaske ne an yi za~en ba tare da magu]i ba? Shin da gaske ne Shugaba Jonathan ya lashe za~en ba wata tantama, kwatankwacin yadda Cif Mashood Abiola ya lashe babban za~en da aka yi a 1993?

In aka ce za~e babu mur]iya, to dole ne ya kasance iyayen jam’iyya ko jami’an gwamnati ba su gitta wa shi mai jefa }uri’a wasu matsaloli ko wasu }ayoyi a kan hanya ba. Misali, ba su yi masa wata barazana ko tilastawa ko wata musgunawa a bayyane ko a kaikaice ba. Tilas ne mai ka]a }uri’a ya zama mai cikakken ’yanci, mai yanke hukunci kan wanda zai za~a bisa dogaro da hujjojin da ya gani na irin aikin ciyar da }asa gaba da ]an takara ya zayyana a kundin }udirin sa. Tilas ne ya kasance }wa}walwar sa ta ba shi cikakkiyar amincewa da cewa lallai wannan ]an takarar zai yi wa jama’a aiki ba tare da son rai ba. Kada ya zamana an takura masa ko an ja ra’ayin sa da wata kyautar ku]i, ko al}awarin samun wani abin duniya ko kuma barazanar wani abu zai same shi idan bai bi sahun da ake so ya bi ba.

Idan mu ka yi amfani da wa]annan bayanai da ke sama a kan abin da ya wakana daga ranar Alhamis zuwa asubahin Juma’a na makon jiya a dandalin Eagle Square, to babu shakka dariya za mu yi kan i}irarin da iyayen PDP ke yi na cewa wai sun gudanar da za~en fidda gwanin ba tare da mur]iya ba. Da farko, idan mun duba da kyau, za mu ga cewa ai tun ma kafin ranar za~en ta zo ne aka shirya wa Jonathan samun nasara, wato tun ma kafin dalaget su zo Abuja, sannan wa]anda su ka yi wannan }ullin ba wasu ba ne illa gwamnonin jihohi wa]anda ke ganin cewa duk abinda su ka zartar shi ne ya dace da al’ummar jihohin su. A wannan za~en fidda gwanin, dalaget ba su da bambanci da tumakai, kuma gwamnoni ne makiyayan su. Kawai gwamna ya ba su umurnin ga wanda za su za~a idan an je Abuja, ko da kuwa su a ran su ba shi su ke so ba.

A wurin yanke wannan shawarar ne aka yi duk wani sa-toka-sa-katsi. A nan aka nuna masu cewa duk wanda ya yi biyayya ga umurni, zai samu kyakkyawar sakayya, yayin da shi kuma wanda ya bi son ran sa, za a kalle shi a matsayin maci-amana, sannan zai ji a jikin sa. A }asa irin tamu inda fatara ta yi katutu, jama’a na bin duk inda su ka ga ya fi mai}o ne, shi ya sa babu wata wahala wajen samun masu biyayya fiye da ‘maciya-mana’. Wannan ne ya sa gwamnoni, wa]anda su ne wu}a da nama a wurin watandar ku]a]en jihohin su, su ke kasancewa uwa da makar~iya a duk wani za~e da za a yi a Nijeriya. Idan kun tuna, tsohon gwamna Donald Duke ya ta~a ba mu labarin duk yadda hakan ke faruwa, a wata hira da jaridar The Guardian ta yi da shi a bara.

Ko a kwanan nan sai da ]aya daga cikin jigajigan PDP, wato Cif Tony Anenih, wanda ya yi }aurin suna wajen shirya duk wata dabara ko ma}ar}ashiya ta samun galaba a jam’iyyar, ya sha wa ’ya’yan jam’iyyar alwashi a wurin babban taron jam’iyyar a Birnin Benin cewa duk wani dalaget da ya yi gigin za~en Atiku, to za a gano shi a hukunta shi. Abin mamaki, babu wanda ya nuna damuwa kan wannan muhimmiyar barazanar daga mutumin da aka san cewa in ya ce zai yi abu, to fa sai ya yi ]in; hatta su kan su ’yan ~angaren Atiku ba su ce komai ba.

Wata hanyar dabara da mashirya za~en fidda gwanin su ka bi don bai wa Jonathan nasara kuma ita ce yadda su ka rarraba masu za~e jiha-jiha. Ga wanda bai gane ba sai ya yi zaton an yi haka ne don a samu sau}in tantance masu za~e da kuma wajen }irga }uri’un da aka ka]a. To amma gaskiyar maganar ita ce an yi wannan shirin ne don masu za~e su ji a ran su cewa idan ba su za~i wanda gwamnan su ya ce su za~a ba, to ana ganin su, kuma za a iya gano su. Shi ya sa yanzu za ka iya gane jihar da “ta fi son” Jonathan da kuma wadda “ta ci amanar shi”. Akwai alamun cewa zufa ta karyo wa Gwamna Isa Yuguda a lokacin da ake }irga }uri’un Jihar Bauchi; dalili shi ne kowa ya san cewa Yuguda ]an ga-ni-kashe-nin shugaban }asa ne, to kuma sai ga shi dalaget ]in jihar sa sun ba Atiku har }uri’u 44. Duk da yake Jonathan ne ya yi kaye da }uri’u 2 kacal, mutane da dama sun fara tambaya kan anya wannan gwamnan ya na da cikakken iko kan dalaget ]in sa da kuma idan ya na ba shugaban }asa cikakken goyon baya? Irin wannan karkasa masu za~en jiha-jiha ya ba Jonathan kyakkyawar dama ta hanayar tilasta masu su daidaita sahun su da nasa. Da gaske, ba sai mun kira hakan da sunan magu]in za~e }arara ba domin inda aka yi magu]in shi ne tun wajen shirya tsarin za~en.

Magana ta gaba ita ce batun ku]i. Mun ga yadda kafafen ya]a labarai su ka dinga samun ku]in shiga ta hanyar tallace-tallacen da ’yan takarar su ka ri}a sakawa kafin a yi za~en. To amma wasu wa]anda su ka ca~a su ne dalaget. Ni ]in nan na zanta da wasu daga cikin dalaget ]in da su ka zo za~en, kuma sun fa]a mani cewa lallai an raba masu ma}udan ku]a]e. Tun a jihohin su an bi su an ba su kyautar ku]i iri-iri. Sannan gwamnoni ne su ka ]auki nauyin tafiyar su, da ba su wurin kwana da ku]in abinci. An yi masu hu]uba mai yawa kan abin da za su yi a Abuja, da kuma abin da ba a yarda su yi ba. Wanin su ya ce mani, “Abin yadda ka san aikin soja. Za a ba ka umarni, sannan ba a yarda ka yi wani abu na kankin kan ka ba.” Wani dalaget ya bayyana mani cewa da su ka zo Abuja, sai ga kyautar ku]in da Atiku ya aiko ta na jiran su – wato dalar Amurka, wuri na gugar wuri har dala 3,000 ga kowane dalaget ]aya, to amma kuma sai wannan ku]i su ka zama kamar wasan yara a lokacin da kyautar da Jonathan ya aiko ta zo – ita kuma dala 7,000 ga kowane dalaget. Idan kai mai wayo ne, sai ka kar~i duka biyun, ka ga ka tashi da dala 10,000 kenan – kuma kusan kowa hakan ya yi. Duk da haka, na fahimci cewa ba wannan ku]in ba ne su ka ja akalar dalaget ]in a }arshen }arshe, a’a, umurnin gwamna ne. Dalaget }alilan ne su ka bau]e, ba su bi umarni ba.

Abin tambaya shi ne: don me gwamnonin su ka mara wa Jonathan baya a wannan za~en? Shin su ba sun ci nasu za~en fidda gwanin ba? E, sun ci, to amma sun san da cewa har yanzu da sauran rina a kaba, wato kujerar su ba ta gama zama daidai ba. Har yanzu Jonathan ya na da iko kan su. Idan har ba su haye sira]in za~en da za a yi a Afrilu ba, to da saura baya – wai an yi fiton mai gwaiwa. Don haka, yawancin su su na ganin gwamma su bi a sannu ta hanyar bin umurnin jam’iyya da na fadar shugaban }asa da kuma na ’yan koren Jonathan. Shi ya sa ba abin mamaki ba ne ganin yadda Jonathan ya doke Atiku a Jihar Abiya inda ya samu }uri’a 80 shi kuma Atiku 1 kacal, ya samu 141 a Akwa Ibom yayin da Atiku bai samu ko ]aya ba; ya samu }uri’a 67 a jihar sa ta Bayelsa yayin da Atiku bai samu ko ]aya ba; ya samu 105 a Kuros Riba yayin da Atiku bai ci ko ]aya ba, kuma ya samu 128 a Ribas yayin da Atiku ya samu 2 kacal.

To, ko an }i ko an so, yanzu ne ya}in ya fara zafi. Ko waye ya shirya za~en fidda gwani na makon jiya, ya yi ne don ya ba Jonathan nasara a babban za~en da za a yi nan da wata biyu. “Da haka mu ka fara” – kuturu ya ga mai }yasfi. Mu dai mun zura na-mujiya mu ga yadda kokowar za ta kaya, musamman yadda Atiku zai yi }o}arin yin ramuwa kan wannan babban kaye da aka yi masa duk da tunatarwar da ya yi wa dalaget.

—-
An buga wannan sharhin a LEADERSHIP HAUSA, a yau Jumma’a

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *