Tunawa da Shehu Maigidaje Funtuwa bayan shekara 20

“Shi Shehu Maigidaje kamar Bahillace can daji,

A wurin kiwon shanu nai,

In ya koro za su yi ɓarna,

Sai ka ga matar shi na tare mai.

To haka nan Shehu Maigidaje,

In ya ɗauko waƙa tai a rubuce,

Sai ka ga matash shi na taya shi.”

– Shata a waƙar ‘Na Gode Shehu Maigidaje’

 

A YAU Laraba, 23 ga Disamba, 2020 ne Alhaji Shehu Maigidaje Funtuwa ya cika shekara ashirin cur da rasuwa. Mutane sun fi saurin tunawa da Alhaji Shehu ne saboda waƙar da Alhaji Mamman Shata ya yi masa mai taken ‘Na Gode Shehu Maigidaje,’ amma ni na fi saurin tunawa da mu’amalar da mu ka yi ni da shi daga farkon shekarun 1990 har zuwa ƙarshen rayuwar sa.

Idan na waiga, sai in ga ba ma wata daɗewa mu ka yi ba a mu’amalar mu, domin kuwa mun fara haɗuwa a cikin 1992, mu ka rabu bayan shekara takwas, to amma irin zumunci da mu ka yi sai in ga kamar mun shekara ashirin tare. Mun haɗu a lokacin da na fara fafutikar tattara tarihin rayuwar Alhaji Mamman Shata, a gidan Shatan a Funtuwa. Na je ne domin in ga mawaƙin kamar yadda na kan yi jefi-jefi, shi kuma ya je wajen Shatan kamar yadda ya saba yi, sai Alhaji Ya’u Wazirin Shata ya gabatar da mu ga juna.

Da na ji cewa shi ne wanda Shata ya waƙe ɗin nan, shi kuma da ya ji ni ɗan jarida ne – kuma wanda Shata ya amince wa ya rubuta tarihin sa – shi kenan, sai mu ka ɗinke. Ya ɗauke ni a motar sa, zuwa gidan sa a nan cikin Funtuwa, ya kai ni har cikin gida ya gabatar da ni ga iyalin sa. Bayan mun ci abinci mun sha labari, sai ya kai ni tasha, ya sanya ni a mota, na koma Kaduna. A lokacin ina aiki a matsayin Mataimakin Editan jaridar Nasiha (wadda kamfanin jaridar The Reporter ta Janar Shehu Musa Yar’Adua ke bugawa).

Da farko dai, ni ba tsaran Alhaji Shehu ba ne, amma ya ɗauke ni a matsayin amini, abokin sirrin sa. Ya sha ba ni labaran da na fi so in ji, wato game da Shata. Ban da aikin Nasiha da na yi, daga baya na zama Editan mujallar mako biyu-biyu mai suna Rana (wadda kamfanin mujallar Hotline ke bugawa). Ya zuwa lokacin, na fahimci cewa Alhaji Shehu haziƙi ne, domin kuwa marubucin waƙoƙin Hausa ne, har ana sako waƙoƙin sa a Rediyon Nijeriya na Kaduna. Hasali ma dai, shi ne jami’in yaɗa labarai na ƙungiyar sha’irai ta ƙasa wadda ta ƙunshi shahararrun mawaƙa irin su Malam Mudi Sipikin, Malam Aƙilu Aliyu, Alhaji Baba Maigyaɗa Agege, Alhaji Garba ABCD Funtuwa, Malam Salihu Kwantagora, da sauran su da dama.

Akwai wata hira mai tsawo da na taɓa yi da shi, aka buga ta a cikin mujallar Rana, wadda ta ƙunshi tarihin rayuwar sa, da batun waƙar da Shata ya yi masa, da batun nasa waƙoƙin. Duk wanda ya karanta hirar, zai ƙara fahimtar wanene Maigidaje, musamman ra’ayoyin sa game da rayuwa.

Maigidaje mutum ne wanda ya iya hulɗa da jama’a. Mutum ne mai haba-haba da kowa, mai barkwanci, kuma mai zumunci. 

Daɗaɗɗiyar ƙungiya ce mai manufar kawo cigaba tare da haɗin kai tsakanin al’ummar Funtuwa da kewaye.  

Ya kamata a sani cewa a da shi ne shugaban ƙungiyar matasa ta tsohuwar Ƙaramar Hukumar Funtuwa (tun ta na haɗe da su Bakori, Ɗandume, Faskari da Sabuwa). Wani abu kuma shi ne yawancin ma’aikatan rediyo da ke zuwa Funtuwa domin su yi hira da Shata ko su ɗauki waƙoƙin sa, wato irin su marigayi Khalifa Baba-Ahmed, marigayi Yaya Abubakar, su Halilu Ahmed Getso, to Shehu Maigidaje ne mai masaukin su, kuma shi ne zai yi jagora a je wajen Shata a tara masa ƙasa har ya amince a je inda za a ɗauki waƙoƙin, a ɗauka.

Duk wannan mu’amala ta sa Shata ya ɗauki Maigidaje kamar ɗan sa, domin a cikin gidan mawaƙin babu inda ba ya shiga. Haka kuma da yake ya iya karatu da rubutu (ta hanyar yaƙi da jahilci), Shata kan kira shi ya rubuta masa wasiƙa, ko ya aike shi wani waje ya kai masa saƙo.

A dalilin kasancewar Maigidaje jagora a ƙungiyar matasan Funtuwa ne Shata ya yi masa waƙa. Yadda abin ya faru shi ne da ma can ƙungiyar kan roƙi Shata ya yi mata wasa a gidan wasa domin ta samu kuɗin shiga. Alhaji Shehu ne ke jagorantar zuwa gayyato shi har gida. Idan sun je, Shata ba ya ƙin zuwa; ya kan ce, “To ai ku ‘ya’ya na ne.”

Wata rana a cikin 1972, ana irin wasannin nan na ƙungiya a Funtuwa, Shata na waƙa, Shehu kuma na ta giggilmiyawa a matsayin shugaba, an ɗan tsaya ana hutawa, can da maroƙin Shata, Alhaji Lawal Tsangaya, ya ga Maigidaje ya gitta, sai ya ce, “Alhaji Shehu mun gode da alherin da ka ke yi mana ba sai ka ga idon Shata ba. Idan ya yi tafiya ba ya Funtuwa, kai ke riƙe da mu!”

Shata ya yi kamar bai ji ba. Can da zai koma waƙa, ya na riƙe da makirfo, sai aka ji ya ce, “Na gode Shehu Maigidaje!”

Shi kenan, ‘yan amshi su ka karɓe, ‘yan kallo kuma sai sowa da tafi raf-raf-raf! Asalin waƙar ‘Na Gode Shehu Maigidaje’ kenan. Ƙwaya ɗaya ce rak ya yi masa, sai dai maimaici idan an je wani wurin; wato ta kasance irin waƙoƙin da Shata ya yi wa wasu mutanen masu waƙa ɗaya kacal amma karɓaɓɓiya ga jama’a, irin su: ‘Na Gode Goshi Ta Ɗangude’, ‘Ƙusoshin Birni Uwawu’, ‘Malam Muɗɗaha Ɗanraka’, ‘Habu Na Habu’, ‘Alhaji Sani Zangon Daura’, ‘Magaji Mai Ido Ɗaya’, ‘Bahillace Ja’e Ɗan Ali’, ‘Wamban Kano Habu Ɗan Maje’, ‘Na Gode Sarkin Fada Alex’, waƙar Indon Musawa da ta Kyauta Uwar Gajeje, da sauran su.

Wannan waƙa ta yi farin jini matuƙa. Ta fito da ainihin wanene Shehu Maigidaje, musamman fiƙirar sa da zumuncin sa da tawakkalin sa da tawali’un sa da dangantakar sa da iyalin sa. A cikin ta, Shata ya kwatanta kan sa da Shehu a fagen waƙa, amma fa kowanne akwai nasa fagen – wannan a fagen kiɗa da waƙa, wannan kuma a filin rubutun waƙa – ya nuna kowa gwani ne a inda Allah ya aje shi.

Waƙar ta yi wa Maigidaje alfanu matuƙa. Kamar yadda ya faɗa mani, ko taron suna ko ɗaurin aure ya je, aka ce Shehu Maigidaje ya zo, to mutane na so su gan shi ba domin saboda waƙoƙin sa da ake sakawa a rediyo ba (waɗanda sun girma wadda Shata ya yi masa), a’a, sai saboda “wannan wanda Shata ya waƙe”! Ya ce ‘yan sanda ma sun taɓa tare shi domin bincikar takardun mota, amma su na ganin an rubuta ‘Maigidaje’ sai su ka ce, “Ko kai ne Shata ya yi wa waƙa?” Da ya ce shi ne, sai abin ya koma na raha. Kai, ba ma shi Alhaji Shehu da ya mutu yau shekara 20 ba, hatta iyalin sa duk inda su ka shiga aka ji inkiyar sunan su, za a ce ai ‘ya’yan wanda Shata ya yi wa waƙa ɗin nan ne.

Wannan ya yi daidai da faɗar da maroƙi Tsangaya ya yi a kirarin Shata, wato da ya ce duk wanda Shata ya yi wa waƙa ba ya taɓewa har abada. Manufa dai, sunan sa ba zai gushe ba, kuma duk inda ya shiga sai ya ga haske saboda tauraron sa da waƙar Shata ta haskake.

Wani abu game da Maigidaje shi ne, ban da harkar kasuwanci da ya ke yi, kamar dillanci da saye da sayarwa, babban ɗan siyasa ne. Mu’amalar sa da mutane ta ce ta sa tilas ya zama ɗan siyasa. A lokacin da mu ke abota ne aka naɗa shi Daraktan Yaɗa Labarai na rundunar yaƙin neman zaɓen Alhaji Mahmuda Waziri a matsayin shugaban ƙasa. Hakan ya ƙara kusanta shi da jama’a. 

Na kan yi mamakin yadda a duk lokacin da ya shiga garin Kaduna sai ya je waje na, ko a gida ko ofis, mun gana. Kuma ya kan so in raka shi wurare, mu je nan mu je can a motar sa. Ta dalilin sa na san wasu garuruwa da dama na ƙasar Katsina, irin su Bindawa da Mani da Mashi. Ta dalilin sa na taɓa zuwa gaban Sarkin Daura Alhaji Muhammadu Bashar, mu ka yi gaisuwa. Ta dalilin sa na san hakimai irin su Alhaji Tukur Nadabo, Hakimin Bakori, har na yi hira da shi kan waƙoƙin da Shata ya yi masa da mahaifin sa.

Akwai wasu abubuwan ma waɗanda ke alamta kusanci na da Maigidaje. Misali, lokacin da na yi auren fari, Alhaji Shehu ne ya ɗauko amaryar tawa tare da ƙawayen ta daga gidan su a motar sa, ya kai ta gida na. Wani misalin shi ne lokacin da zan tafi ƙaro karatu a Birtaniya a cikin 1993, Shehu Maigidaje ya bugo mota da sassafe daga Funtuwa, ya zo Kaduna ya ɗauke ni ya kai ni Kano, inda na hau jirgin sama. Haka kuma lokacin da na gama karatu na na digiri na biyu a Birtaniya, Alhaji Shehu ne ya tafi Kano daga Funtuwa shi kaɗai, ya tarbe ni a filin jirgin sama, ya ɗauko ni zuwa gida Kaduna.

Irin waɗannan misalan su na da yawa, na dai taƙaita ne. Na ƙarshen wanda ba zan tsallake ba shi ne wani yunƙuri da mu ka taɓa yi, ni da Maigidaje, na sasanta Shata da wata matar sa da su ka daɗe da rabuwa, wadda kuma Shatan ke so kamar me. Yunƙurin dai ya ci tura, amma ya nuna irin kusanci na ni da Maigidaje da kuma wanda mu ke da shi da Alhaji Shata.

Alhaji Shehu ya rasu ne a Funtuwa a ranar Asabar, 23 ga Disamba, 2000 bayan ya yi rashin lafiya, ya na da shekaru 51 kacal a duniya. Ba wani tsufa ya yi ba, amma ya shuka alheri mai yawa. 

A duk lokacin da na tuno da shi, sai na tuno da wani bashi da ya ke bi na, wato na in taimaka in buga masa littafin rubutattun waƙoƙin sa. A kullum ina addu’ar Allah ya ba ni damar ida nufi, shi kuma ina masa addu’ar Allah ya rahamshe shi, ya sa mutuwar sa hutu ce, kuma ya albarkaci abin da ya bari, amin.

 

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *