Tudu Tsoho: Tunawa da Gambu Mai Waƙar Ɓarayi

A yau ne Alhaji Muhammadu Gambo Fagada (wanda ake kira Gambu Mai Waƙar Ɓarayi) ya cika shekara biyar da rasuwa. Ya rasu a ranar 18/8/2016 ya na da shekara 67 a duniya.

Domin tunawa da shi a daidai wannan rana, na rubuto baitukan farko na ɗaya daga cikin manyan waƙoƙin sa daga faifai, wato waƙar Tudu Tsoho, kamar yadda za a gani a nan ƙasa.

Haka kuma ga wani hoto nan da aka ɗauke shi lokacin da na ke tattaunawa da shi a ofishi na a Kaduna a ranar Talata, 21 ga Janairu, 1997 (yau shekara 24 da rabi kenan). Allah ya rahamshe shi, amin.

*

Waƙar Tudu Tsoho
ta marigayi Alh. Muhammadu Gambo Fagada (Gambu Mai Waƙar Ɓarayi)
 

Rubutawa daga faifai: Ibrahim Sheme

(Tsakuren waƙar)

Mu na a kan Tudu,
Ba kuma hurcewa ni kai ba,
Sai na kashe tsohon zan wucewa,
Don ko tsoho yat taɓa ni.
 
Sai niz zabura nish sheƙa da keke.

Rage kiɗin nan!

Kwab bi dare in duniya ya ke, ko kura ta san Muhammadu,

Baba na gadi ‘yar gaton uwa!

Bakin garka ni ishe shi,
Yac ce min, “Wat taɓa ka?”
Nic ce mai, “Tudu Tsoho yat taɓa ni.”
Yac ce, “Maganab banza da yohi,
Ai ba a zuwa yawo gidan Tudu,

Duw wani ƙwaro aƙ ƙasag ga kwat tahi kolo na gwadi nai!”

Na zabura na haura da keke na ishe Ɗanzaga Dodo Halilu Shugaba,
Tsoho Baban ya hi burgu.
Nic ce mai, “Mi kah hi burgu?”

Yac ce sata yah hi burgu.

Yac ce min, “Tudu Tsoho ba a son taɓa shi,
Kwat taɓa Tsoho ya yi wauta,

Ya san kolo na gwadi nai!”

Sai ni ishe ma Dahin Gumbiru take,
Don na san ko bataliyas soja tah hita daji in gaya ma,

Manu Dahi na ɗan taya ta!

Sai yac ce, “Mis samu Gambo?”

Nic ce, “Tudu Tsoho yat taɓa ni.”
Yac ce, “Maganab banza da yohi,
In akwai ta da daɗi, ka tai da kan ka,

Ai ba mu tsar ma tambaya ba.”

Da niz zabura nish sheƙa da keke,
Na ishe ma Abadaji na Ambursa,
Mamman Ba’iska da gaske.
Yac ce min, “Mas samu Gambo?”
Na ce mai, “Tudu Tsoho yat taɓa ni.”
Yac ce, “Maganab banza da yohi!
Ai ba a zuwa yawo gidan Tudu,

Kwat tahi, kolo na gwadi nai!”

Dan nan nah hurce ban tsaya ba,
Na iske Adon Ƙashin-Zama,
Lokacin da ya na nan bai mace ba.
Yac ce min, “Mis samu Gambo?”
Nac ce mai, “Tudu Tsoho yat taɓa ni.”
Ya ce, “Maganab banza da yohi,
Ai ba a zuwa yawo gidan Tudu,

Kwat tahi, kolo na gwadi nai.”

Sai dan nan niy yi Jega,
Nan niy yini nan ni ka kwana Jega,
Nis sake yini haz zan wucewa sai nit tuna Inuwa Ɗanmaɗotcchi,
Wawilon-wawilon baƙin gona,
Kaicon ni kai na Gambo,
Ya katakoron kusu na Gambo,

Bawa mai hwama da hurji!

Bakin garka nig ga yara,
Nac ce masu, “Kai mugu ya na nan?”

Sun ka ce mini, “Ai mugu ya na ciki, ba shi zuwa yawon marece.”

Da an ka jinjina ganga,
Niz zuga shi, nij ji awa dub bai kula ba,
Sai nah hwasa kuka niy yi zamne,
Ɗiyan shi gaba ɗai an ka yo wuri,
Yara su na ludda ƙahwa ta,
Su na ta hwaɗin, “Gambo mijin Kulu, mai guma cuta an guma mai,
Kila kunama ta haɗa mai.”

Lahiya ni ke!

Sai Bawa yaz zo da kai nai,
Yac ce min, “Tashi zamne.”
Yac ce, “Najeriya duka kaf wanne shege yat taɓa ka?
In alƙali yat taɓa ka hwaɗa mani Gambo Maikalangu;
Sai ya shiga ɗaki ya yi rairan, in tuma in zamne ciki nai,
In kama wuya nai, ban saki nai,

Sai ya ƙare shure-shure, na ga alamun ba ya sheɗa,

In je ka gida can in hwaɗa maka: wannan shegen na kashe shi!

Sai yac ce, “Ruma bari kuka, ina mu ka cim mai yanzu-yanzu?

Kai, ina mu ka cim mai in buge shi?”

Sai nac ce mashi, “Ba sauri akai ba,
Ka san dai yat gobe Larba, sai kau Tsoho ya ci Romo.”
Yac ce mini, “In kau yac ci Romo gobe ba mu gamawa lahiya lau,

Don in ga tukunya, in ga tulu sai wani ya tchaye ka na nan!”

Nig ga dare ya daɗe, swahiya ba ta waye ba rannan;
In dai ga hayagaga ina tsaye,

In wuce gawa ɗanya-ɗanya.

Kukan zakaran hwari ina zamne,
Nig ga swahiya ta daɗe ba ta waye ba,
Niy yi kiran sallah da daddare,

Ni dai a dai yi ta waye in ga ɓanna.

Nid dai matsu ba a waye ba rannan,
Tun da subahi nic ce, “Tashi!”
Yac ce, “Ai ba sauri akai ba,

Tsaya mu karya kumallo Maikalangu.”

Da mun ka karya kumallo,
Ɗanmaɗotcchi nig goya baƙin mugu ga keke.
Mu na tahiya sai ga mu Romo mun ishe Tudu,
Nic ce, “Inuwa, ga Tudun can,
Cikin ƙohwa hakan ga.”
Sai nic ce, “Amma ka tsaya in wasa Baba,

Don ba a yi wa Tsoho ƙuƙuwa ba.”

Sai nik koma ga kan Tudu,
Nic ce, “Tsohon kolo, kai kad daɗe Tudu,
Mai hana maiki cin idanu,
Gaban ka gabas, sau ya yi yamma,
Yara ba su ganin takin ƙafar ka!”
Sai yac cire hulla yak kihe ƙasa;

Hullas saƙi ag ga Baba, duk kau layu sun cika ta.

Sai yac ce min, “Ga ɗan gaton uwa!
Sai yaya ta yi yaya, ba nan Najeriya ba, haƙ ƙasaw waje ba ka da mugu mai iyawa,
Kowa ka iyawa ga ni ga shi mu gangara daji in buge shi,

In bash shi ga kolaye su canye!”

Kan da in dawo inda Ɗanmaɗotcchi,
Bawa na cizon hwarutta, mugu na murza idanu.
Nic ce, “Ka jiya hwa!”
Yac ce, “Mu je Kamajiɗi,
Kak ka damu,
Wancan shege ni ka bi nai,

Yau ba mu gamawa lahiya lau!”

Sai don ɗai in ɓata ran su,
Don duk in zuga su,
Su su zunduma rame, in tumaye,
Don su aka ɗauri, ni kam ina sake,
Kayan kowa ban taɓawa,
Ba ni shiga shagon uban wani,
Ba ni da ko sisin kwabo ciki,
Ba ni da ko ƙyallen atanhwa,
Wannan rikici ba ni yarda.
In mai shiga ciki yaz zo, tare za mu,
In bi shi ƙwahwa tai in zura mu,
Sai ni ga awa zai buɗe kanti in dawo in tsaya ƙauye.
In an koro, sai in tara masu,
In ɗora hwaɗin, “Ar! Ga shi, ga shi!
Ku dahe ɓarawo ɗan gaton uwa!”
In yaɗ ɗakko ba a sani ba,
Nig ga gasassa arha-arha,
Sai in ɗora hwaɗin, “Ka ga zuwa na.”
Ni ka yanga, sai an sam man tawa maula tunda ba harakab banza ni kai ba!
Da mu ka je Kamajiɗi,
Tun zuwan mu nig ga ɓarayi ga su birjit, an yi naɗin Sarkin Ɓarayi.
Sai nij ji awa na taki Arhwa,

Cikin jama’a ta, ga su birjit, da ba a barin kayan mutane.

Sai Bawa mijin ‘Yaryari yaz zaka yac ce, “Ah, wai ya hakan ga?
Allah wadan harakak ka,

Ga shi an yi naɗin Sarkin Ɓarayi ka zaka duk ka ɓata ran ka.”

Nic ce, “Mi ranar in kiɗin ku,
Mi ar ranaw waƙak ku shaggu?
Ga ni ina waƙaɓ ɓarayi, ga mai kuɗɗi ya taɓa ni,

Ba a samu ɓarawo yat taɓa ba.”

Sai yac cira tsaye, nag ga jiki nai na kaɗawa,
Haw wani daɗi ya ƙume ni,
Na aza dan nan zai wucewa,

Su tai su yi gomozon da Baba.

Yac ce, “Nijeriya duka…”

Na ce, “Tudu Tsoho yat taɓa ni.”

Sai yay yi kwashashat yah hwaɗi zamne.

Nac ce, “Babbar bura’ uban nan! Sarki ka ji tsoro, mi ar ranay yaƙin talakka?”

Sai yac ce, “Ba tsoro na ba Gambo. 
Duw wani mugu aƙ ƙasag ga,
Na ce maka dud duniya duka, 
Ba ka da ɗa nan mai biyat Tudu,
Kowab biyat ta Tsoho wallai kolo na gwadi nai!”
 
 
 

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *