Wannan waƙa na ɗaya daga cikin waƙoƙin Ɗan’anace waɗanda su ka sa na haƙƙaƙe da cewa har ƙasa ta naɗe babu makaɗin dambe irin shi. Ko ita kaɗai ya rera, ta isa ta ɗar ma sa’a! Saboda ita kaɗai, ni idan mutum ya ce akwai makaɗin dambe da ya zarce Ɗan’anace sai in ji kamar zagi na ya ke yi!
Ga waƙar na yi karambanin rubutawa. Amma na haɗe kalaman jagoran da na ‘yan amshin domin kusan tare su ke tafiya a waƙar sau da yawa. A taimaka da gyara inda na yi kuskure:
Taho Na-Bakura ɗan Abdu gazaguru.
To bahago,
Ina mazan da ka i ma?
Ɓaleri sannu mai hana ƙarya!
Ka nai da wa ka nai da aboki,
Kuma ka nai da ɗa ka nai da uba nai.
Ɗan Audu gazaguru,
Kai ji duna ya tare hanyab Bakura ya tare Mafara,
Ɗan Audu ya tare Rini,
Kowaz zo Kufoji ya ishe bayi wa’anda ba a wa takakka,
Wandara kai dai ka wa mutum takakka,
In ka zo ka ko buge shi ka dawo!
In ka zo ka ko buge su ka dawo!
Arne ka biya na Mande na sarkin ɗiya,
Tafo na Kallamu Musa,
Ina arne mai halin Hasau na Maraɗi?
Shago irin kiɗin ga da ni ma duk da Hasau ga su Ɗanwaire ba a yi ma haka nan ba.
Ɗa ya tuna da lahira ya ka kwana,
Bale zuwa gidan alƙali.
Gabas da yamma, dama da hauni, kudu da arewa,
Wandara ka dai hana ma runji suna,
Yanzu mutum ko ya yi dambe ba shi da suna,
In dai ina buga kawo.
Bari mu hwaɗa masu runjin ga masu tsafin dambe saboda bawan Sarki:
Maza ka cin ƙurungun kura,
Wandara sai jan karen da yay yi zagogi.
Duna ga wanga zamani ba wani ba,
Mutum ko ya kashe ka ba shi da suna,
In kau ka kashe su ka yi gaba ɗai.
To ko an kashe ka ban jin komi,
Ɓarnad da ka yi shi su ka ranko!
Yaƙi ya ci annabawa Shago,
Bale Ɓaleri mai naɗe hannu.
Yaƙi ya kashe talaka da barde,
…
Daɗa fa ga kare ga kura ɗan Abdu gazaguru,
Ga kare ga kura,
Wandara mi ka kai da rai ga arna?
Gama na san halin maso rai wawa.
Duna, maso rai wawa,
Tafi a kashe ka gaba ɗai na Ɗan’anace Shagon Mafara,