
A yau ne Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero, ya cika shekara huɗu da rasuwa. Allahu Akbar! Allah ya jiƙan maza! Ba za mu gaji da tuno da ayyukan sa na alheri ba. Haka kuma ba za mu gaji da sauraren yadda mawaƙa su ka kambama shi ba, su ka fito da martabar shi. Cikin su har da Alh. Mamman Shata da waƙar sa ta “Don Darajar Ado Ɗan Bayero”. Ga ta:
AMSHI: “Don Darajar Ado Ɗan Bayero” –
Don darajar Ado ɗan Bayero (2x)
–
Alhaji Shata zai tafi Birnin Kano,
Ni dai zan tafi Birnin Kano,
Don in gano Ado ɗan Bayero.
–
A yanzu kowa ya sauka Birnin Kano,
Kowa ya kwana Birnin Kano,
Ya san an yi sarauta daidai,
In ya ishe Ado ɗan Bayero.
–
Ya yi hawa uku ɗan Bayero,
Cikon huɗu shi ya ka yi yanzu nan:
Farko yaz zama Ado Midil,
Kana ya yi Wakilin Gadi,
Ado ya zama Embasada,
A yanzun ya zama Sarkin Kano.
–
Mai daraja Ado ɗan Bayero.
–
Tsofaffin birni na faɗi,
Dattawan birni na faɗi,
Ran nan ina ta yawo birni,
Na’ ishe tsofaffi na fira,
Dattawan Birni na faɗi,
Tsofaffin Birni na faɗi:
“Mu dai tun daga Dabo na farko,
Hay yaz zo ga Ado ɗan Bayero,
Hay yau ba ai ba yaron Sarki,
Tun lokacin Alu Mai Saje,
Sai kai Ado ɗan Bayero.”
–
Shi dai Ado ɗan Bayero,
Adalcin shi kamar Bayero,
In yai hawa, kamar Bayero,
In yai zaune, kamar Bayero,
Hawan motas sa kamar Bayero,
Hat tahiyas sa kamar Bayero,
Amma halin sa halin Alu ne,
Halin yaƙi tamkar kakan sa.
–
Mai daraja Ado ɗan Bayero.