Sashen Hausa na rediyon Faransa

Mahamane Salisu Elh Hamissou, dan jarida mazaunin birnin Yamai na kasar Nijar, ya ba mu labarin cewa a ranar Talata mai zuwa, 15 ga Mayu 2007, da misalin karfe 7: 30 agogon Nijeria da Nijar (bai fadi ba ko na dare ko na safe) sashen Hausa na rediyon kasar Faransa (Radio France International) zai fara watso shirye-shiryen sa kai-tsaye daga birnin Ikko na tarayyar Nijeria. Shi Salisu ya na daya daga cikin ma’aikatan da aka dauka su yi aiki a wannan sabon sashe.

A gaskiya na yi murnar jin wannan albishir da aka yi mana. A gani na, bude sashen Hausa a RFI ya k’ara nuna mana muhimmancin wannan harshe a fagen watsa labarai a duniya. Alhamdu lillahi. Allah ya ba su sa’a amin.

To amma ina da tambayoyi:

1. Salisu ya ce karfe 7:30 ne za a fara shirin, amma bai ce na SAFE ba ne
ko na DARE.
2. Bai fad’i a wace mita da kuma wane zango (wato SW ko MW ko FM)
za a kama rediyon ba.

Ina ba da shawara ga shugabannin gidan rediyon da su saka
talla a kafafen watsa labarai da ke akwai don su sanar da jama’a
labarin kafa wannan sashe na Hausa. Ina nufin kafafe na Hausa kamar
Gaskiya Ta Fi Kwabo, Aminiya, Leadership Hausa, Rediyon Nijeriya
Kaduna, Nagarta Radio, Freedom Radio, da sauran su.

Bayan haka, yaya na ji wai a Legas su ke, maimakon Paris? Wani sabon
salo ne? Anya ba su gudun kada wata rana jami’an tsaron Nijeriya su
kai musu ziyara idan su ka watsa wani labari da jami’an ba su so? Ka san fa daya daga cikin dalilan ‘yancin da BBC Hausa da VOA Hausa su ka samu shi ne saboda sun yi wa jami’an Nijeriya nisa! Hattara!

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *