Sannu da zuwa, Talatu Danny!

A makon jiya na samu wasiƙar i-mel daga Malama Talatu Danny, inda ta gaya mani (tare da sauran abokan ta a Nijeriya) cewa ta iso Nijeriya daga Amurka. Talatu, wadda sunan ta na yanka Carmen McCain, ta ce a yanzu ta na hutawa a gidan mahaifin ta a Jos kafin ta fantsama zuwa Kano da sauran garuruwa.

Talatu dai ƙawar mu ce ‘yar ƙasar Amurka da ke koyon Hausa da al’adun Hausawa, musamman a ɓangaren littattafai da finafinai. Ta kan kira kan ta ɗaliba (ko da yake mu a wurin mu malama mu ka ɗauke ta!) a wata jami’a a Amurka.

Ta na da fitaccen gidan yana a intanet mai sunan ta, inda ta kan bayyana tunanin ta kan al’amura daban-daban da su ka shafi al’adun Afrika kamar yadda ake nuna su a hanyoyin sadarwa na zamani. Ta kan kuma bayyana labarai da tunani a kan rayuwar ita kan ta.

Talatu, ina yi maki barka da zuwa (ko in ce barka da dawowa) Nijeriya. Tare da fatan za ki ji daɗin wannan zaman, kuma ya kasance kin ci moriyar wannan balaguro da ki ka yi.

Lale marhabin!

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *