Sabuwar Dokar Cire Ko Saka Kuɗi A Banki

Babban Bankin Nijeriya (CBN)

Na lura akwai rashin fahimta game da sabuwar ƙa’idar cire kuɗi ko saka kuɗi a banki wadda Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya fito da ita kwanaki kaɗan da su ka gabata. Mutane sun yi ta yaɗa labarin ƙanzon kurege game da dokar.

To, Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya yi bayani a Twitter kan sabon tsarin cajin kuɗi da su ka haura rabin miliyan. Ga abin da bankin ya ce da Turanci: “The Cash-less Policy deposit/withdrawal charge is only on the amount in excess of the limit. For instance, if you deposit a cash of N501,000.00, N1,000.00 is in excess of the limit. The bank will charge you 2% of N1,000.00 which is N20.00.” 

Fassarar wannan magana a taƙaice ita ce za a caji mutum kashi 2 cikin ɗari ne kurum idan kuɗin SUN HAURA rabin miliyan. Misali, idan ka kai kuɗin da su ka haura N500,000 da N1,000, to a kan ita wannan naira dubu ɗayan kaɗai za a caje ka kashi 2 cikin ɗari, wanda ya kama naira ashirin (N20) kenan. Ba za a caje ka komai a kan N500,000 ɗin ba.

Saboda haka, idan mun lura, dokar ba ta ce idan ka kai ajiyar kuɗi ko ka ciri kuɗi rabin miliyan za a caje ka wani abu ba. Har fa sai kuɗin sun haura N500,000. Don haka masu cewa wai mutum ya rage N1,000 ko N500 wajen zuba kuɗi ko cire kuɗi a banki, su na yaudarar mutane ne waɗanda ba su fahimci sabon tsarin ba.

Mu kula, idan ka saka N500,000 ko ka cire N500,000 a banki, to ba za a caje ka ko kwabo ba. Sai idan kuɗin sun haura N500,000 ne sannan za a caje ka kashi 2 cikin ɗari na abin da ya haura ɗin.

Wannan bayani da na yi, don wayar da kai kaɗai na yi shi, ba domin nuna goyon baya ko rashin goyon bayan sabon tsarin ba.

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *