Musulmi ne abokin gabar Musulmi

A cikin wannan makon, labari ya bazu a Kano cewa wai an samu wani sabon bulufim kuma na wata ‘yar fim ɗin, wato bayan na Maryam Hiyana da ya bazu a gari. Wai wata wadda sunan ta ya fara da suna “M” ce ita ma ta yi majigin batsa.

To a gaskiya na yi cikakken bincike, na gano cewa sam, labarin ba gaskiya ba ne.

Abin da ya faru shi ne, wasu shaƙiyyai (ko wani shaƙiyyi) ne su ka ɗauki wani bulufim na Amerika, su ka saka a cikin wayar GSM, su ka ba shi sunan ita wannan “M” ɗin, su ka kuma yaɗa a garin Kano cewa wai ita ma ta yi bulufim.

Inda za ka san cewa ana bin ‘yan fim da sharri da gangan shi ne yadda su kan su Turawan da ke cikin wannan fim, ba ma bakar fata ba ne, a’a, jajaye ne su ke yin lalatar, to amma don sharri sai aka ba fim ɗin sunan “M” ɗin.

Don haka don Allah mu daina saurin yaɗa ji-ta-ji-ta. Sai ka ga mutum bai yi wani bincike ba, amma da jin cewa an yi kaza sai ya shiga yaɗawa, wani har a intanet (wataƙila don kada a riga shi!). Don Allah mu daina yaɗa ji-ta-ji-ta. Mu tuna, a yau Musulmi shi ne babban abokin gabar Musulmi; Musulmi ne ke ɗaukar wuƙa ya daɓa wa cikin sa. Mun ga haka a al’amarin Hiyana.

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *