Muryoyin Zuciyar Sa’adatu Baba

Fitacciyar marubuciyar nan Malama Sa’adatu Baba Ahmad ta wallafa sabon littafi na waƙoƙin Hausa mai suna ‘Muryoyin Zuci.’ Littafin, mai shafi 80, ya na ɗauke da rubutattun waƙoƙi har guda 30. An kasa su zuwa gida uku, inda kashi na 1 ya ke ɗauke da waƙoƙi shida, shi ma kashi na 2 waƙoƙi shida, sai kashi na 3 mai waƙoƙi 18.

Waɗannan waƙoƙi, kamar yadda za mu kawo maku nazari a kan su nan gaba kaɗan, sun ginu ne bisa jigogi daban-daban na rayuwar mu ta yau. Amma sun fi karkata ne ga faɗakarwa kan rayuwar duniya da buƙatar yin tanaji don rayuwar gobe ƙiyama. Akwai wasu da aka yi su kan wasu mutane da marubuciyar ta sani ko ta ji labarin su, kamar marigayi Sarkin Kano Muhammadu Sanusi, da ƙawar ta, Talatu (Carmen McCain), da wata Halima, da Farfesa Attahiru Jega, da wasu ’yan unguwar su marubuciyar, wato Fagge, waɗanda su ka riga mu gidan gaskiya, da dai sauran su. Shi ma gidan Rediyon Freedom na Kano ba a bar shi a baya ba, an waƙe shi.

Masana biyu sun yi gabatarwar littafin. Na farkon su shi ne Dakta Yusuf M. Adamu, sai kuma Farfesa Abdulƙadir Ɗangambo, dukkan su malamai a Jami’ar Bayero, Kano. A gabatarwar sa, Dakta Yusuf ya faɗa wa mai karatu abin da kowane kashi na littafin ya ƙunsa. Ya yi nuni da cewa kashi na 1 ya ƙunshi waƙoƙi ne da su ka shafi Musulunci da gargaɗi da kuma ta’aziyya da abokantaka. Waƙoƙin kashi na biyu sun maida hankali ne a kan matsalolin Nijeriya kamar na zaɓe. Kashi na 3 kuma ya ƙunshi waƙoƙi ne da su ka shafi soyayya da mutuwa da rubutu da hassada.

Dukkan masu gabatarwar, wato Yusuf da Ɗangambo, sun yi la’akari da hikimar marubuciyar da irin basirar ta, musamman wajen amfani da kalmomi da kuma salon waƙoƙi masu ƙwar ɗaya, wanda ba a cika samu ba a fagen rubutun Hausa a yau.

A littafin, har wa yau, wasu masanan guda uku – wato Malam Isma’il Garba, Malam Zulƙifil Adam Garba Dakata da Malam Bala Muhammad – su ma sun yi sharhi, inda su ka yaba da wannan gagarumin aikin.

Ita dai Sa’adatu Baba Ahmad, wadda mata ce ga Alhaji Shehu Sunusi Bayero, sananniyar marubuciya ce. Ta rubuta littattafan Hausa sama da 20. An haife ta a Kano a ranar 27 ga Yuli, 1984. Ta yi karatun addini da na boko duk a Kano, inda a yanzu haka ɗaliba ce a Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya a Jami’ar Bayero. Memba ce kuma a Ƙungiyar Marubuta ta Nijeriya (ANA), reshen Jihar Kano.

An buga a LEADERSHIP HAUSA ta ranar Juma’ar makon jiya

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *