A makon jiya, gidan talabijin na CNN ya tambayi ɗaya daga cikin ’ya’yan Shugaba Muammar Gaddafi na ƙasar Libya, wato Saiful-Islam Gaddafi, abin da mahaifin sa da ’yan gidan su za su yi tunda ga shi ’yan ƙasar su na zanga-zangar ƙin amincewa da mulkin su. Shin za su tsere ne kamar yadda shugaban Tunisiya ya yi, ko ƙaƙa? Sai ya amsa da cewa: “Mu na da Dabara ta 1, da Dabara ta 2 da kuma Dabara ta 3. Dabara ta 1 ita ce za mu ci gaba da zama har mu mutu a Libya. Dabara ta 2 ita ce za mu ci gaba da zama har mu mutu a Libya. Dabara ta 3 ita ce za mu ci gaba da zama har mu mutu a Libya.”
Manufar sa dai ita ce ba za su taɓa barin Libya ba, sai dai a mutu!
Akwai mutum huɗu a cikin ’yan kwanakin nan da su ka yi kunnen uwar shegu da buƙatar da ’yan ƙasashen su su ke da ita ta cewa lallai su sauka daga karagar mulki don a fito da tsarin mulki irin na dimokiraɗiyya a ƙasashen nasu. Waɗannan mutane su ne Shugaba Zine El Abidine Ben Ali na ƙasar Tunisiya, da Hosni Mubarak na Masar, da Laurent Gbagbo na Cote d’Ivoire, da kuma na baya-bayan nan, wato Kanar Gaddafi na Jamhuriyar Larabawa ta Libya. Ɓata lokaci ne in tsaya ina faɗa maku cewa tun tuni biyun farko cikin su su ka ari takalmin kare, su ka arce, sannan sauran biyu sun kafe, sun ce ba za su yarda su bar mulki ba ko da kuwa za a yi asarar rayuka ne. Gbagbo ya na tirka-tirka da abokin hamayyar sa na siyasa, wato Malam Alassane Ouattara, wanda shi ne ya lashe babban zaɓen da aka yi a ƙasar amma an hana shi karɓar ragamar mulki, sannan duk ƙasashen duniya sun yi Allah-wadai da ƙeƙasa ƙasar da shi Gbagbo ɗin ya yi. Har yau ɗin nan ana fafatawa a wannan ƙasar da ke yankin Afrika ta Yamma. A ranar Alhamis ta makon jiya, an yi musanyar harsasai tsakanin ɓangarorin biyu a babban birnin ƙasar, wato Yamoussoukro. Hukumar kula da ’yan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNHCR) ta ruwaito cewa aƙalla mutum 20,000 ne su ka tsere daga sassan birnin Abidjan washegari, su ka nemi mafaka a wasu unguwannin.
Babu ruwan waɗannan mutane masu kunnen ƙashi da sauraren wani bahasi ko lalama. Da Ben Ali da Mubarak sun sha alwashin cewa ba za su taɓa sauka daga mulki ba har illa masha Allahu, wai gwamma su yi shahada, to yanzu kuma ga Gaddafi ya na faɗin haka shi ma. Babu shakka, na san akwai ire-iren waɗannan shugabannin da dama a nan Afrika da kuma yankin Gabas ta Tsakiya. To amma mutanen su ba za su sake yarda su na yaudarar su da ƙaryar cewa su ’yan kishin ƙasa ne ko kuma masu ƙin jinin Amurka ba ne. Jama’a sun riga sun ƙyaro su, ba su buƙatar komai sai sauyi daga mulkin danniya zuwa mulkin dimokiraɗiyya Tuni jama’ar ƙasashen Yemen, Bahrain, da Jodan su ka shiga sahun takwarorin su na Tunisiya; dubban mutane sun fito kan tituna su na zanga-zangar buƙatar sauyin siyasa. Mugun martanin da shugabannin su su ke aika masu, sam, bai karya masu lago ba.
A yanzu dai rikicin ƙasar Libya wanda duk duniya ta fi sa wa ido saboda muhimmancin sa, ya fara hawa hanyar da rikice-rikicen Tunisiya da Masar su ka hau tun daga watan Janairu. Don haka za mu iya cewa ramin ƙaryar Gaddafi ƙurarre ne. Duk da irin cika-bakin da ya ke yi, shi da ɗan sa Saiful-Islam, akwai alamun cewa mulki ya soma zaɓuce masa, tunda ga shi ’yan tawaye sun amshe rabin ƙasar daga hannun sa. Gwamnatin sa, kamar ta Mubarak, ta ginu ne bisa ruɓaɓɓen kadarkon da iyalan sa da ’yan ƙabilar sa su ka tallabe. To amma tsawon shekaru 40 da aka yi ana mulkin kama-karya ya sa wannan kadarkon bai da sauran ƙarko a zamanin yau. Tuni duniya ta sauya, amma su waɗannan masu mulkin danniyar da ke Afrika da yankin Gabas ta Tsakiya sun kasa fahimtar hakan. Ba fa zai yiwu ka ci gaba da mulkar jama’a a tsawon lokaci ba tare da ka take haƙƙin ɗan’adam ba. Mutane ba za su ci gaba da buƙatar ka ba ko da kuwa ka cimma nasarorin gina ƙasa kamar yadda Gaddafi ya yi. Za su so su samu sauyi, su ɗan sarara.
Shure-shure bai hana mutuwa, Gaddafi zai faɗi ƙasa warwas domin kuwa dukkan dalilan da su ka sa aka cimma nasara a juyin-juya-hali a Tunisiya da Masar akwai su a wannan kacaniyar ta Libya. Na farko, jama’ar Libya su na zanga-zangar buƙatar ya sauka daga mulki a birane da dama. Na biyu, mutane ’yan asalin wasu ƙasashen su na ta guduwa daga ƙasar a yayin da wutar rikicin ke ƙara ruruwa. Na uku, wasu manyan ƙusoshin gwamnatin sa su na ta yin murabus. Sun haɗa da ’yan Tawagar Libya a Majalisar Ɗinkin Duniya a birnin Jeniba, waɗanda su ka aje aiki a daidai lokacin da ake taron Cibiyar Kare ’Yancin Ɗan’adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya a ran Juma’a ta makon jiya. Sa’annan su ma ’yan tawagar Libya a taron Ƙungiyar Ƙasashen Larabawa (Arab League) sun aje aiki a birnin Alƙahira ran Juma’ar makon jiya, su ka ce su yanzu wakilan talakawan Libya ne ba na Gaddafi ba. Na huɗu, manyan ƙasashen duniya, waɗanda duk mai mulkin danniya zai buƙaci tagomashin su, sun juya wa Gaddafi baya. Akwai ha]in gwiwa a tsakanin su kan yadda za a tunkuɗo da gwamnatin sa, ta hanyar yin amfani da hanyoyin diflomasiyya da na kafafen yaɗa labarai. Shi ya sa a kowane lokaci ba labarin da ake yi a manyan tashoshin talabijin na duniya irin su CNN da Aljazeera da BBC World sai na Libya. Hakan ya taimaka wajen harbo gwamnatocin danniya na Tunisiya da Masar. Ƙasar Faransa ta bayyana ƙaƙaba wa Libya takunkumin karya tattalin arziki. Amerika da Birtaniya sun janye goyon bayan su ga Gaddafi.
Majalisar Ɗinkin Duniya, ta hanyar cibiyoyin ta, ta kafa wa Libya ƙahon zuƙa. Misali, Hukumar Ciyar da Ƙasashe Gaba ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UN Development Programme) ta kori ɗiyar Gaddafi, wato Aisha al-Gaddafi, daga muƙamin jakadar musamman, ba don komai ba sai saboda yaƙar ’yan zanga-zanga da ake yi a Libya. Shi kan sa sakatare-janar na majalisar, wato Mista Ban Ki-moon, ya fito ƙarara ya ragargaji Gaddafi saboda yin watsi da ya yi da kiran da ya yi masa na ya daina harbe masu zanga-zanga. Cibiyar Kare Haƙƙin Ɗan’adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi taro a birnin Janiba na ƙasar Siwizalan inda aka fitar da kakkausar suka kan Libya.
Duk a wannan harƙallar, munafinci da rashin tsare amana na ƙasashen Turai da Amurka sun fito fili. Misali, mun san cewa Amurka da Tarayyar Turai sun sha ɗaure wa azzaluman shugabanni gindi, musamman a Afrika da Gabas ta Tsakiya, ba don komai ba sai don su na biya masu buƙatun su. Buƙatun sun haɗa da ba su damar sayen man fetur arha, da ba su ha]in kai kan matsalar ’yan ci-rani da ke shigar masu ƙasa, da tsaro na yankuna, da yaƙi da ta’addanci da kuma hana bunƙasar addinin Musulunci a faɗin duniya. To amma da zarar sun ci moriyar ganga sai su yada kwauren ta. Da ma Gaddafi ba nasu ba ne, ba kamar Mubarak ba. Da ma su na kallon sa a matsayin ɗan taratsi. To sai ga shi kuma ya shiga uku. Don haka kun ga sun samu damar da za su bi duk hanyar da za su bi don su kakkaɓo shi daga sheƙar sa. Saboda haka dai masassarar da ta ci shugaban Tunisiya da na Masar ba za ta bar shi ba; abin da ya ci Doma, ba ya barin Awai. Ko ya so ko ya ƙi sai mulki ya koma hannun talakawa, wato mulkin dimokiraɗiyya.