MACE MUTUM!

A yau Alhamis (ko in ce jiya, tunda karfe 1 ta haura) na shiga kasuwar Wuse, Abuja, inda na samu sayen littafin Mace Mutum na Rahma A. Majid. N820 na saye shi. Littafin ya ɗan yi kwana biyu da fitowa ban gan shi ba, ga shi kuwa wai ni ma ɗan gida ne (tunda “ƙanen” marubuciyar ne!). Hasali ma dai na aika wa da wasu littafin, ciki har da Amina Abdulmalik (mai ‘Ruwan Raina’), wadda ta na Katsina yanzu, na sa Ɗanjuma Katsina ya kai mata kwafe har gida, kuma ta karanta har ta gama cikin ƙanƙanen lokaci!

Na aje littafin a kan teburi na a ofis. Duk wanda ya shigo sai ya ɗauka, ya yi mamakin girman sa, har wasu na cewa, “Wannan tarihin waye?” Ba su ga hoton Yar’Adua ko Babangida a bangon ba! Sai na ke ce musu, “Ai novel ne.”

“Novel? Da ma ana yin novel da Hausa haka?”

Mutane sun saba da ganin littafi mai shafi 40 zuwa 70 na Hausa. Shi ‘Mace’Mutum’, shafi 520 ne. Wane yaro?!

Kai, lallai Rahma ta ciri tuta! Mace mai kamar maza, kwari ne babu! Matar soja kin fi ƙarfin yaro!

Allah ya sa sauran marubuta za su ɗauki hannu, su yi koyi da ita. Ni da ma na shafe shekaru ina yekuwar cewa ya kamata marubutan mu su riƙa yin rubutu mai inganci, kuma su riƙa yin littafi mai kauri-kauri. Su yi ƙoƙarin ficewa daga ƙangin ‘Adabin Kasuwar Kano.’ To, Rahma dai ta fara. Allah ya ƙara mata basira, da ƙwarin gwiwa.

Gobe (ko kuwa dai a yau!) zan fara karanta shi in-sha Allahu.

Kuma na ƙudiri aniyar saya wa marubuciya Sa’adatu Baba Ahmad Fagge kwafe ɗaya in kai mata a gidan su a nan Abuja (domin fa ta na gari yau mako biyu, kuma na ziyarce ta sau biyu, gobe ma zan koma). Zan ba ta mamaki da kyautar littafin, domin ita ma har yanzu labarin sa kawai ta ke ji. Za mu yi tseren gama shi kenan.

Sallaman ku!

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *