DA ƙarfe 6:43 na yamma a birnin Alƙahira a ranar Juma’a ta makon jiya, wani jagoran masu zanga-zangar ƙin amincewa da mulkin Shugaba Hosni Mubarak mai suna Wael Ghonim ya tura saƙo a dandalin Twitter da ke intanet, ya na faɗin: “Mu na taya ki murna, Masar, babban mai laifin nan ya arce daga fadar sa.” Ya na nufin Mubarak wani babban ɓarawo ne ko mai kisan kai da sauran manyan laifuffuka wanda mulkin sa ya zo ƙarshe har ya gudu daga fadar shugaban ƙasa. Hakan ya biyo bayan tumbuɗin da al’ummar ƙasar su ka shafe kwana 18 su na yi, inda a ƙarshe, ran Juma’a da ta wuce, zamanin Muhammad Hosni Mubarak a karagar Jamhuriyar Larabawa ta Masar ya kawo ƙarshe. Ƙarfin jama’a ya tabbata. Idan kun tuna, a rubutun da na yi a wannan shafin a makon jiya mai taken, “Fir’auna Na Ƙarshe Ya Faɗi!” na bayyana cewa, “Tuni muguwar gwamnatin sa ta shiga garari, ta fara tarwatsewa, domin kuwa iyalan sa da manyan jami’an gwamnatin sa tuni su ka fara arar takalmin kare su na arcewa.”
Tarin jama’ar da ta taru a Dandalin Tahrir ta wuce maridan gwamnati su maida ita abar wasa ko su yi mata riƙon sakainar kashi, domin jama’a ce wadda ta san ciwon kan ta kuma ta ke da zummar lallai sai an biya mata buƙatar ta. Yawancin mutanen da ke cikin taron matasa ne waɗanda ba su gama ko ta-ta-ta ba lokacin da Mubarak ya ɗare karagar mulki a 1981. To amma mutane ne masu ilimi, wayayyu a lamurran duniyar mu ta yau, masana intanet, masu fushi da gurɓacewar mulki, waɗanda su ka gaji da salon tafiyar hawainiyar mulki, kuma sun gaji da salon mulkin mutum ɗaya, sannan su na son canji ko ta halin ƙaƙa. Matasa ne ’yan Facebook waɗanda su ka san yadda za su yi amfani da intanet da kuma tashoshin talabijin na satalayit don cimma buƙatun su. Duk wani mai baƙin mulki da ya yi kunnen uwar shegu da irin waɗannan ’yan taratsin, to jiki magayi.
Mubarak ya yi duk wasu kame-kame don ya liƙe a jikin sheƙar sa. Saboda lallai ya san tsiyar waɗannan nau’urorin yaɗa labarai da Turawa su ka ƙirƙira, ya dakatar da Facebook da gidan talabijin na Aljazeera na wani ɗan lokaci, amma duk a banza. Babu abin da ya yi masa amfani; misali barazanar da kwamandojin sa na soja su ka yi wa masu zanga-zangar, da soki-burutsun da Mataimakin Shugaban Ƙasa Omar Suleiman (mutumin da shugaban ’yan zanga-zanga Mohammed El-Baradei ya kira da “abokin tagwaicin” Mubarak) ya yi masu, da hare-haren da magoya bayan Mubarak su ka kai wa ’yan zanga-zangar ko kuma jawaban yaudara da shi Mubarak ɗin ya yi wa jama’ar ƙasar a ran 1 da ran 10 ga Fabrairu, inda ya sha alwashin wai zai ci gaba da mulki har na tsawon watanni bakwai masu zuwa. Da alama, bai gane zurfin tsanar da mutane su ka yi wa azzalumar gwamnatin sa ba. Tunda dai duk ƙasar ta na kuka da shi, sannan dubban mutane sun shiga yajin aiki, inda su ka ja wa ƙasar birki, don haka bai fi awoyi kaɗan – ba ma kwanaki ba – kafin ƙarshen sa ya zo.
Aje aikin da ya yi ran Juma’a wata shaida ce da ke ƙara gabbata da ƙarfin ikon jama’a. Irin haka ta taba faruwa a ƙasar Filifins a 1986, wanda ya sa aka dinga yin juyin juya hali a ƙasashe da dama a Gabashin Turai a 1989, ana rusa gwamnatocin gurguzu. Amma an jima irin hakan ba ta faru a nahiyar Larabawa ko ta Afrika ba ma, inda masu mulki ke kallon kan su a matsayin wani abin bauta. To amma yanzu ta fara sauya zani. A yau, Larabawa su na yin tambaya kan halin da rayuwar su ta ke ciki, kuma su na yunƙurin kifar da azzaluman shugabannin su. A watan jiya, hakan ta faru a ƙasar Tunisiya inda jama’a su ka yi zanga-zanga su ka hamɓarar da shugaban ƙasar, har sai da ya tsere zuwa gudun hijira. To amma fa ba wanda ya taɓa tunanin cewa irin wannan za ta iya faruwa a Masar, ƙasar da ke kan gaba wajen yin alaƙa da Yammacin Turai a ƙasashen Labarawa duka, musamman ma da yake Mubarak ne shugaban ƙasar, mutumin da ake ganin ya na da ƙarfin mulki tamkar Fir’auna, wanda sai dai a kwatanta shi da shugaban Iraƙi na da, wato marigayi Saddam Hussein. To, duk da haka sai da ta faru ta ƙare, wai an yi wa mai zani ɗaya sata! Jama’a sun faɗi abin da su ke so, kuma sun samu.
To amma fa tsugune ba ta ƙare ba, an sayar da kare an sayi biri. An dai fidda Mubarak, amma kuma ginshiƙin gwamnatin sa – wato sojojin da su ka ɗaure masa gindi – har yanzu su na nan daram damdam, sun maida ƙasar maras dimokiraɗiyya. Har yanzu za a iya ci gaba da cin mutuncin jama’a. Za a iya murƙushe duk wani ɗan adawa.
Na biyu, tsoron da gwamnatocin Yammaci su ke yi na cewa wai babbar jam’iyyar adawar ƙasar, wato Muslim Brotherhood, za ta hau kujerar mulkin ƙasar wata babbar barazana ce ga abin muradin jama’ar Masar. Turawa da Yahudawa su na so Masar ta ci gaba da kasancewa a tafin hannun su saboda kawai ta na dakushe abin da su ke kira da tsattsauran ra’ayin addini. A ranar da Mubarak ya faɗi, Firayim Ministar ƙasar Jamus, wato Angela Markel, ta yi gargaɗin cewa tilas ne Masar ta ci gaba da yin abokantaka da Isra’ila. Sannan wani fitaccen ɗan jaridar Amurka wai shi Glenn Beck, wanda tsattsauran ra’ayin sa bai da bambanci da na ’yan Alƙa’ida wajen tada hankalin jama’a, ya bayyana cewa yunƙurin fidda Mubarak wani babban gangamin haɓaka addinin Islama ne na duniya wanda ya taso tun daga nahiyar Asiya har zuwa Ingila. Beck, wanda ke da ɗimbin mabiya shirin sa na talabijin a Amurka, ya ce, “Wannan ba zancen Masar ba ne. Wannan magana ce ta dukkan wani mutum da ya taɓa yin shiri, ko ya ke so, ya canza ainihin rayuwar Turawa da Yahudawa baki ɗayan ta.” Manyan masu faɗa a ji a Amurka da dama su na da wannan ra’ayi, ciki kuwa har da babban ɗan jam’iyyar Republican ɗin nan mai suna Newt Gingrich, wanda ya furta cewa, “’Yan Muslim Brotherhood su ne manyan maƙiyan rayuwar mu da jinsin mu.”
Shin wai ba abin mamaki ba ne kuwa a ce ’yan ra’ayin riƙau na Yammacin Turai ba su son ganin mulkin dimokiraɗiyya ya wanzu a yankin Gabas ta Tsakiya don kawai irin shugabannin da talakawan Larabawa ke so ba su ba ne Turawa da Yahudawa ke so, sun ɗauke su masu tsattsauran ra’ayi? ’Yan riƙau ɗin Yammaci sun fi son shugabannin Larabawa masu ƙaryar son jama’ar su sun ci gaba da mulki, a yayin da su ke kau da kai daga matsalolin rayuwa da su ka addabi jama’ar su saboda kawai shugabannin duk ’yan koren su ne.
Sa’annan sai maganar tattalin arziki, wanda Mubarak ya kasa gyarawa domin ya fi maida hankali ga harkar tsaro. Shi kullum abin da ya fi damun sa shi ne dangantakar ƙasashe, wadda ta haɗa da shiri da Isra’ila da kuma yaƙar ’yan kishin Islama. Saboda haka, duk wanda ya zama sabon shugaban ƙasar Masar ya na da babban aikin gyaran komaɗar tattalin arziki a ƙasar sa. Bayan haka, wani abu mai muhimmanci kuma shi ne batun yadda za a gina ingantaccen tsarin mulkin dimokiraɗiyya bisa ginshiƙin addinin jama’ar ƙasa. Hujjoji da dama sun nuna cewa tsarin mulkin dimokiraɗiyya ya na iya ginuwa a ƙasashen Musulmi. Shugaban Amurka, Barack Obama, ya fara amincewa da bin hanyar da gwamnatocin Amurka da dama su ka ƙi aminta da ita, wato buƙatar gina tsarin mulkin dimokiraɗiyya a ƙasashen Larabawa.
Idan an bi wannan hanyar bil haƙƙi da gaskiya, to za a ga ci-gaba sosai. Domin fa rashin samun zaɓi, da kuma cusa wa jama’a shugabannin da ba su so ta hangar ci da addini ko batun tsaro ya na taimakawa wajen sa wasu su ɗauki tsattsauran mataki, wanda ya haɗa da tada bam a cikin jirgin sama ko kuma fasa motar safa da gurnati. Don a cimma nasara, tilas ne Turawa da Yahudawa su ƙyale Larabawa su zaɓa wa kan su shugabannin kan su ta hanyar zaɓe na fisabilillahi. Juyin juya hali da aka yi a Masar ya nuna cewa zamanin da Turawa su ke cusa wa Larabawa shugabanni don biyan buƙatar su ta son rai ya shuɗe. A yau, matasa za su riƙa bin bahasi da babbar murya.
Mu ma a nan Afrika ya kamata mu farka daga barci. Don me? Dalili shi ne mu na da masu mulkin murɗiya amma masu kiran kan su da sunan masoya dimokiraɗiyya. Wasu ma su na ta ƙara ɓullowa a fagen. Ya kamata matasan Afrika, Baƙar Fata, su yi koyi da takwarorin su da ke arewacin nahiyar mu; kada a manta, su ma ’yan Tunisiya da ’yan Masar duk ’yan Afrika ne. Ya kamata su farka daga gyangyaɗi, su yi bin bahasi ga shugabannin su, su buƙaci sauyi a duk inda hakan ya dace.
Ku kuma ’yan Masar mu na taya ku murna. Fir’auna ya faɗi.
—
An buga a LEADERSHIP HAUSA ta ranar Juma’a da ta ga bat