Wani lokaci, ba ka shirya ba sai kawai ka tuno da wani aikin alheri da wani ya yi maka ko wata gudunmawa da ya bayar a rayuwar ka. Wani lokaci gudunmawar ƙanƙanuwa ce idan an auna ta, to amma kuma ta yi babban tasirin da ba ka kula da shi sosai ba, kuma wani wanda ke tare da kai bai sani ba. Abin da ya faɗo mani a rai kenan a rana mai kamar ta yau.
Idan an dubi hotunan da ke tare da wannan rubutun, za a ga shafin littafi a rubutun hannu da na shafin mujalla da na wata mace da kuma guda biyu na bangon littafin ‘Yartsana da aka wallafa.
Hoton farko na shafi na 136 ne na littafi na mai suna ‘Yartsana a lokacin da na rubuta shi da hannu. Na rubuta shi a cikin 1992/93 domin samar da nishali ga masu karatu a cikin mujallar mako biyu-biyu mai suna Rana, ta kamfanin Hotline a Kaduna. A lokacin, ni ne editan mujallar. An riƙa gutsura labarin a duk mako biyu da mujallar ke fitowa; wani lokacin, a ranar da za a tafi buga mujallar na ke rubuta cigaban labarin da za a buga!
Hoto na biyu, shafin mujallar ne kamar yadda ake buga shi.
Hoto na uku, wata matashiya ce mai suna Mary Isah Chonoko. Ba kowa ya san ni da Mary ba a yanzu, amma duk wanda ya san ni daga wajen 1999 zuwa sama da shekara 15, to ya san ni da Mary. Ita ce sakatariya ta bayan na kafa kamfanin wallafa littattafai na Informart a cikin 1995, kamfanin da ya kasance mai wallafa mujallar Fim daga 1999 zuwa yau. Sai da ta kai daga baya har Mary ta zama manajar kasuwanci ta kamfanin.
Mary ce ta buga littafin ‘Yartsana a komfuta, wato ‘typesetting’. Na tattaro mata shafukan da mujallar Rana ta buga, sannan kuma da yake ita Rana ba ta kammala buga littafin ba aka rufe ta (lokacin ina Ingila), sai na ci gaba da rubuta ƙarashen labarin, ina ba Mary, ita kuma ta na bugawa a komfuta.
A lokacin da Mary ta ke wannan aikin ne kuma ta bada wata gagarumar gudunmawa ga littafin wanda ba a sani ba sai a yau – wato sauya sunan tauraruwar labarin littafin daga Balaraba zuwa Asabe! Da farko ma sunan littafin ‘Balaraba’, kuma tauraruwar labarin ma sunan ta kenan. A haka aka buga shi a mujallar Rana tun a 1992/1993 – shekaru da dama kafin haɗuwa ta da Mary.
To, Mary na tsakar wannan aikin na shigar da littafin cikin komfuta sai fitacciyar jarumar finafinai ɗin nan Balaraba Mohammed ta rasu a ranar da aka ɗaura mata aure, a wani haɗarin mota a kan hanyar kai ta gidan miji daga Kaduna zuwa Kano. Duk da yake labarin littafin bai da wata alaƙa da marigayiyar (domin an buga shi a Rana tun ma kafin Balaraba ta shiga harkar fim har duniya ta san ta), Mary ta hango cewa fito da littafin da sunan Balaraba zai iya damun wasu, su ce ai saboda ficen jarumar ne aka raɗa wa tauraruwar littafin sunan ta, musamman ma dai tunda an san alaƙar mu da harkar fim. Mary ta ce mani lallai in sauya sunan tauraruwar daga Balaraba zuwa wani sunan.
Shi kenan, na tafi na shiga kogin tunani ina ninƙaya. Can sai na sanya mata sunan rana, Asabe. Dalili shi ne a ranar Asabar na sauya sunan. Sai na koma cikin littafin na sauya wani waje a labarin inda ake alaƙanta sunan “Balaraba” da kyawun fuskar ta, na alaƙanta shi da sunan rana na Asabe, wadda sunan ta na yanka Zainab.

Na tabbatar marubutan ƙirƙira da dama za su tuna yadda irin hakan ta faru da su, wato na wani dalili da ya saka tilas su ka sauya wani suna a cikin labarin da su ke rubutawa, ko ma su ka sauya sunan littafi baki ɗaya.
Hoto na huɗu, bangon littafin ne a yadda ya fara fitowa. Hoto na biyar kuma bangon bugu na uku ne na littafin.
A yau, Ranar Littafi Da Kare Haƙƙin Mallaka ta Duniya (World Book and Copyright Day), na ga ya dace in yi wa Mary godiya kan wannan gudunmawa da ta bayar, da sauran ƙwazon da ta nuna a wajen aiki. Duk wanda ya san Mary, irin su Aliyu A. Gora II (wanda ya taɓa zama Editan mujallar Fim a wancan lokaci), to ya san ta da sauƙin kai da girmama jama’a da aiki tuƙuru, sannan da bada kyakkyawar shawara ga duk wanda ya dace. Mary, sarauniyar Zuru komai nama, na gode! Da fatan komai naki na tafiya daidai a jihar ku ta Kebbi, inda ki ke da zama a yanzu.
BAYANIN KARSHE:
Hukumar UNESCO ta Majalisar Ɗinkin Duniya ce ta ware 23 ga Afrilun kowace shekara a matsayin Ranar Littafi ta Duniya. An fara a ranar 23 ga Afrilu, 1995. An zaɓi wannan ranar ne domin ta yi daidai da ranar mutuwar shahararren marubucin Ingila William Shakespeare da fitaccen marubucin ƙasar Spain mai suna Inca Garcilaso de la Vega.