Korar Shaidan daga Filato

Shai]an ya samu mafaka a Jihar Filato. Ya na amfani da gazawar bil’adama ya na shuka shakku da rashin yarda, da gaba da kuma son ramuwa a zukatan mutane. Idan ya samu zuciyoyin da son rai ya cika su, sai ya antaya gaba a cikin su. Daga nan sai ka ga ya kambama fushin da ya yi katutu a zukata, ya zuga mutane, wanda hakan kan haifar da kashe-kashen rayuka ba }a}}autawa. Shai]an ya na jin da]i a duk lokacin da ya ga mun yi fatali da }aunar junan mu, mun shiga rikicin da zai iya ruguza zamantakewar mu. Ya kan yaudari mutane don su yi fa]a da junan su, su ragargaza al’ummar su. Ha}i}a, Shai]an abokin gabar bil’adama ne.

Jos ta zama lahirar makwa]aita a yau saboda Shai]an ya tare a can. Kusan a ce Jos ta zama garin da ba garin zama ba. Gari ne na ya}i, inda mutane ke zaman ]ar ]ar. Rai ba bakin komai ba ne a Jos. Mutuwa ce kawai ke ratsawa, ta na shan jini. A yau, hatta ’yan sanda da sojoji, wa]anda farar hula su ka dogara gare su don samun tsaro, tsoron aiki a Jos su ke. Wani rahoto da jaridar Leadership ta buga a ran Juma’a ta makon jiya ya nuna cewa ’yan sanda 52 ne su ka rasa rayukan su a rikice-rikicen da aka dinga yi a Jos daga shekarar 2002 zuwa yau.

Abin ba}in ciki ne a ce Shai]an ya samu gindin zama a Jos domin kuwa, na farko dai, birni ne mai kyan gani; kamata ya yi a ce Shai]an ya tafi can wani mummunan wuri. Na biyu, a da can Jos gari ne inda ake zaman lafiya, shi ya sa ma mutane daga sassa daban-daban na duniya su ka koma can su ka zauna, wanda hakan ya sa Jos ta kasance al}aryar da ta fi kowace tara }abilu a duk arewacin Nijeriya. A da, in aka yi rikici a Kano ko Kaduna, sai ka ga mutane su na guduwa zuwa Jos. Na uku, bai kamata Shai]an ya zauna a Jos ba domin kuwa akwai ]imbin mabiya addini sau da }afa a garin. Gari ne na masu da’awar ya]a addini tun a zamanin Turawa. Shugabannin Kirista da malaman Musulunci sun ]auki garin a matsayin babbar cibiyar aikin su na ya]a addini, ba ma a lardin Binuwai-Filato ka]ai ba, har ma a duk fa]in Arewa.

To, ya aka yi har Shai]an, wannan bawa abin }i, ya samu mafaka a wannan kyakkyawan birni, al}aryar fastoci da rabaran-rabaran da malamai da shaihunnai? Wanene ya ba shi masauki a can, inda daga nan mutane kan yi amfani da gariyo da wu}a}e da takubba da gorori – yanzu ma har da bamabamai – su na aikawa da junan su barzahu? Wa ya ba shi gidan haya a Filato? ’Yan siyasa su na cewa wai ’yan siyasa ne ke jawo rikicin Filato. Zan iya yarda da haka domin kuwa idan ka duba baya da kyau, kafin a yi amfani da siyasa a raba kan garin, ai jama’a su na zaman lafiya da junan su, su ci abinci tare, su yi biki tare, kuma su kwanta tare. Da yawan sun yi auratayya da junan su.

Idan har za a kori Shai]an daga Jos, tilas ne sai shugabannin mu sun gano ‘yan siyasar da ke jawo wannan mummunar fitinar. Kowa ya yarda da cewa wasu manyan mutane ne ke haddasa ta. To, wai su waye su? A fa]i sunan su mana, kuma a yi masu hukuncin ba-sani-ba-sabo, tare da ’yan koren su da su ke turawa don kai hare-hare.

Wani batun da kowa ya yi amanna da shi kuma shi ne, akwai kasawa a ~angaren shugabanni. Wannan ma ta ba da gudunmawa wajen faruwar rikicin. Me ake nufi da hakan? Kawai ana nufin cewa gwamnatin tarayayya a }ar}ashin Jonathan ta gaza kafa dokar ta-~aci a jihar. Kullum sai cacar baki ta ke yi. Ita ma gwamnatin jihar ta kasa ]aukar kowa da kowa a matsayin ]an Nijeriya, ta maida wasu ’ya’yan bora. Sai ka ji ana fa]in “’yan }asa” da kuma “’ya’yan ba}i.” Shin wa ya san wa]annan kalaman a da can lokacin da mutane ke zaune tare a matsayin ‘yan’uwan juna? An yi ittifa}i da cewa wannan gazawar ta shugabanci ta faru ne a sanadiyyar salon mulkin Gwamna Jonah David Jang. Mutane da dama a ciki da wajen Jihar Filato sun yarda da abu ]aya: cewa Jang wani ~angare ne na yadda aka kasa samun maslaha a matsalar Filato, ko ma a ce SHI NE matsalar. Gazawar da ya yi wajen yin mulki bisa adalci a }asar sa, ko dai ta hanyar }ara iza wutar rikicin da gangan ko kuma ta hanyar rashin iya shugabanci, ta kasance ala}a}ai }ashin bakin tulu wajen samun tabbataccen zaman lumana. Shugabannin Kirista da dama wa]anda ba su jin tsoron su fa]i gaskiya sun yi amanna da cewa, sam, shi wannan gwamnan ba zai iya magance wannan matsala mai sar}a}iya ba; maimakon haka, ya ~ige kawai ga kame-kamen iska – misali ya na zargin abokan adawar sa a jam’iyyar sa cewa su na so su ga bayan sa. Wannan babbar gazawar ita ce }ashin bayan kiraye-kirayen da ake ta yi a ~angaren Kirista da na Musulmi cewa ya kamata a kafa dokar ta-~aci a jihar.

In da a }asashen da su ka ci gaba ne, to, da tuni Jang ya aje aiki da kan sa. Amma abin mamaki, a maimakon hakan, wai so ya ke ma ya }ara tsayawa za~e don ya sake mulki na shekara hu]u! Amma a gaskiya kamata ya yi ya gaggauta barin Gidan Gwamnati da ke unguwar Rayfield a }arshen wannan wa’adin na shekara hu]u da ya ke a kai yanzu, kada ya tsaya za~e. Dalili shi ne duk mai hankali zai iya fahimtar cewa idan har Jang ya }ara yin shekara hu]u a karagar mulkin Filato, to za a iya ci gaba da samun tashin hankali a jihar har na tsawon shekara hu]u; za a iya ci gaba da asarar ]aruruwa ko dubban rayuka, sa’annan za a iya ci gaba da harbin iskar da ake ta yi a yun}urin magance rikice-rikicen }abilanci da na addini a jihar.

Ya kamata Jang ya nuna kamala, kamar yadda ya kamata duk wani adalin shugaba ya nuna, kada ya ]auki kan sa a matsayin shugaban wani ~angare. Ya kamata ya san cewa shekaru hu]u da ya yi ya na mulki ba su haifar da komai ba sai mace-mace da ~arna, kuma ci gaba da mulkin sa ba zai haifar da ]a mai ido ba; zai haifar da matsaloli masu yawa a zamantakewa tsakanin addinai, ba kawai a Filato ba har ma a sauran jihohin }asar nan. Zai iya shafar zamantakewa ma baki ]ayan ta a }asar nan. Duk }asashen da su ka ci gaba, a yau sun kasance mazaunin jinsina da addinai mabambanta, ban da Filato. Kamata ya yi Jang kar~i }addara ya ce ya gaji da wannan haukan, ya bar wani mutum ya zama gwamna, ko da kuwa daga }auyen su mutumin zai fito, ko da za a samu dacen samun sabon sauyi.

Wannan muhimmin mataki da ya kamata a ]auka, za ta yiwu ba Jang ka]ai ba ne zai yanke shawarar ]aukar sa; ya kamata shugabannin }asar nan a ko’ina su ke su taimaka wajen ]aukar sa. Domin dai abu ne da ya shafi kowa da kowa, don haka su tabbatar da cewa Jang ya fahimci bu}atar da ke akwai ta samun sabon gwamna a Filato wanda zai fuskanci wannan abin ba}in ciki kai-tsaye, shugaba wanda zai zo da sabon tunani kan hanyar da za a bi a samu zaman lumana; shugaba wanda mugunyar siyasar da ake tafkawa yanzu ba ta ~ata masa suna ba. Duk gwamnan da za a ]ora a Filato sai ya fi Jang daraja a idon jama’a. Ya kamata a fahimci cewa shi fa Jang ba zai iya kare kowa daga mutuwa ko asara ba; shin ba shi ba ne gwamna, mai ri}e da cikakken iko da kuma ]imbin ku]i, amma an kashe ]aruruwan Kirista da Musulmi kuma aka ragargaza dukiya sai ka ce a Beirut ne ko Bagadaza ko kuma Zirin Gaza?

Idan har Jang ya }i yarda da shawarar da aka kawo, ya finjire kan sai ya ci gaba da mulki ko da me ko don me, to ha}}i ya rataya a wuyan jama’ar Jihar Filato na su kada shi a za~en da za a yi a bana. Da ma mulkin dimokira]iyya ya ba jama’a damar su yi waje-rod da duk wani shugaba da ya kangare masu. Duk wanda ya za~i Jang, to ya za~i ci gaba da rikicin shekara hu]u a Filato. Hakan zai kasance an ba Shai]an lassi kenan na ci gaba da zama a wannan kyakkyawar jiha, ya na jawo tashin-tashina da kisan kiyashi kan jama’a. Ya kamata Jang ya taimaki jama’ar sa – walau Kirista ne ko Musulmi, ko Birom ko kuma Hausawa – ya zo a taru a kori Shai]an daga Filato.


An buga wannan makalar a jaridar LEADERSHIP HAUSA ta ranar Juma’a da ta gabata

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *