Kangararre

Guntun labari

Su uku aka kawo daga k’auyensu, to amma yanzu su biyu ne suka rage a makarantar. Gudan, wato Rabeh, tuni aka maida shi gida bayan ya k’i zama a makarantar; kuka ya dinga yi a kullum, har ya fara ramewa, ya kod’e sai ka ce mai ciwon yunwa. Tun su Malam Mai Dorina su na dukan sa har su ka gaji suka koma suna rarrashin sa, amma duk a banza. Da alama dai Rabeh ya saba da dukan, domin kullum abin nasa k’ara ci gaba yake yi. Ran nan dai Alaramma Malam Usman ya ce wa su Malam Mai Dorina, “Kai, ni na gaji da fitinar yaron nan! Ku shirya gobe ku maida shi gidan uban sa.”

Haka kuwa aka yi. Su Mai Dorina suka shirya, suka d’auki Rabeh a motar haya, suka maida shi k’auyen su D’anrafi, can cikin k’asar Katsina. Shi ke nan, aka bar Khalid da D’ankawu su su yi karatun allo da aka kawo su su yi a unguwar Gama Tudu, a birnin Kano. Haka kuma aka bar su da kewar Rabeh, har suna ganin kamar ya fi su morewa. Hasali ma dai sai D’ankawu ya sa rigima shi ma, wato ya ce shi ma ya na son a kai shi gida, wai ba zai iya zama a Kano ba. Amma ina! da su Malam Mai Dorina suka fara jibgar sa, ai sai kawai ya karyo, ya ce ya tuba! Alaramma ya ce, “Wad’d’aren gulya’e! Da, mu za ka yi wa shashanci? Wato kai ganin cewa Rabeh ya sha, shi ne ka ke ganin kai ma za ka iya latsa mu, ko? To, ahir d’in ka!”

Shi ke nan fa, D’ankawu ya nabba’a, suka duk’ufa karatu shi da Khalid da sauran yara.

Makarantar tasu babba ce, domin za a samu yara sama da sittin a cikin ta. Alaramma Malam Usman ne ya ke da ita, to amma shi ma ya gaje ta ne a gun mahaifin sa Alhaji Namakka, wanda aka ce bai dad’e da mutuwa ba. Amma su su Khalid, Alaramma suka sani, domin lokacin da suka zo Kano shi Alhaji Namakka ya dad’e da kwanta dama.

A makarantar akwai yara iri-iri, kuma an kawo su ne daga garuruwa daban-daban. Wasu daga wajen Sakkwato suka zo, wasu kuma daga can wajen Bauchi suka zo. Wasu iyayen su ne suka kawo su da kan su, wasu yayyen su, wasu malaman wad’ansu makarantun ne suka kawo su, wasu kuma ganin su kawai aka yi a makarantar.

Tun da Khalid yake bai tab’a zaton zai shiga rayuwa irin wannan ba. Shi da ya d’auka a boko za a sa shi, kamar yadda aka sa abokin sa Murtala a can D’anrafi. Amma lokacin da malaman boko suka zo d’aukar yara tare da Mai Unguwa, shi Khalid b’oye shi aka yi a k’ark’ashin gado, kakar sa ta wajen uba tana ta cewa, “Wa zai yarda a sa d’an shi a makarantar mishan, inda ba a koyar da addinin Allah? Sam, Haladu dai Gabas za shi!”

Yana ji yana gani aka gama d’aukar ’yan makaranta, shi ko ba a sa shi ba. Ran nan sai ya ji baban sa na gaya wa k’anen shi baban nasa cewa, “Su Malam Ayuba sun zo daga Kano za su yi Babbar Sallah a nan. Idan za su koma zan ba su Haladu su tafi da shi, ya je can ya yi karatu.”

Malam Ayuba dai shi ne Malam Mai Dorina a yanzu; su Khalid ba su san shi da wannan sunan ba sai da suka iso Kano. Kuma ba su san cewa mutum ne mai tsanani ba sai da suka zo makarantar. Ranar da ya fara hora su, ai sai suka ga kamar ya manta da cewa shi fa D’an garin su ne! Ya nuna musu cewa ba sani ba sabo! Don haka suka shiga taitayin su. Khalid yana jin cewa k’ila ma hakan ne ya sa Rabeh ya tubure, ya ce shi tilas ne a maida shi gida.

*

“Daga yau sunan ka Khalid, ba Haladu ba.”

Abin da Alaramma ya gaya wa Khalid kenan kwana biyu bayan isowar su Kano. Amma bai gaya masa dalili ba. Kuma Khalid bai san abin da ya sa aka bar Rabeh da D’ankawu da sunan su na asali ba.

Mahaifiyar sa ta gaya masa, ana kamar gobe za su baro D’anrafi, cewa, “Duk abin da malaman ku suka ce ka yi, ka ce masu To kawai. Yi na yi, bari na bari – ta raba da kowa.”

Don haka sai ya ce, “To,” a lokacin da aka sauya masa suna.

Irin wannan biyayyar tasa ta sa ba a jima ba ya yi farin jini a wurin malamai da manyan ’yan makarantar, wato gardawan da ke kula da yaran. Kowa shi yake son ya aika sawo wani abu ko yin wani aiki. Ya kasance yaro mara k’yuya. Amma kuma wad’ansu sun yi amfani da wannan damar wajen musguna masa, suna d’ibga masa aiki mai yawa a yayin da suka bar wasu tsararrakin nasa suna hutawar su.

D’aya daga cikin masu irin wannan hutawar shi ne D’ankawu. Shi D’ankawu, tuni ya zama wani irin yaro, har ana ganin kamar shi daban yake da sauran almajirai. Na farko dai, shi duk irin barar da ya yi, a cikin sa take k’arewa; ba ya ba kowa abin hannun sa. Ko me ya samu sai ya b’oye abin sa. Idan an ce, “D’ankawu, me ka samo ne yau?”

Sai ya amsa, “Ba komai. Ni ma da yunwa na wuni.”

Akwai wani harajin ranar Laraba da Mai Dorina ya sa a kan kowane yaro, cewa a duk Laraba kowa ya kawo masa naira biyar, idan ba haka ba kuwa jiki magayi. Khalid ya kan kasance na d’aya wurin kawo wad’annan kud’i. Yadda yake samun su shi ne ta hanyar yin dako ko sharar shaguna a bakin kasuwa. Haka kuma wasu bayin Allah kan ba shi sadaka idan ya je bara. Hasali ma dai ya fi kowane yaro samun sadakar kud’i da ta abinci a duk sa’ilin da suka fita. Shi ya sa ma maimakon ya rik’a kawo naira biyar, har naira goma ya kan kawo wa su Malam. Ya kan sha yabo a kan haka.

Shi kuwa D’ankawu, ya tsani yadda ake nuna wa Khalid k’auna a fili, ya manta karin maganar da ke cewa duk irin shimfid’ar da mutum ya yi a kan ta zai kwanta. A gaskiya, shi yana ganin cewa ya fi sauran yara wayo. Bai damu da kirarin da Malam Mai Dorina ya ke yi masa ba, wato da ya ke ce masa, “D’antsako samu ka k’i dangi!” Tuni ya samu wata uward’aki wai ita Ladi Lallausa, wadda ke da rumfar saida abinci a bakin kasuwa. Ita dai matashiyar karuwa ce. Jinin su ya had’u da na D’ankawu tun a ranar da ta lura da shi idan yana yi mata wanke-wanke. Duk da yake dai yaro ne, amma kuma k’ato ne, dogo, mai alamun k’arfi. Ko wani aike za ta yi, shi za ta tura. Daga baya ma sai ta k’ara masa girma, maimakon ya rik’a wanke mata kwanonin da mutane suka ci abinci a ciki sai ya koma yana taya ta mik’a wa mutane abincin. A kan haka ma ta d’inka masa kayan aiki, riga da wando da hula ‘yan kanti masu kyau, wad’anda yakan sa idan ya zo aiki kuma ya tub’e su idan zai tafi gida.

Malam Mai Dorina ya yi ya yi ya hana D’ankawu yin wannan aikin, amma a banza. Har bulala ashirin ya tab’a ba shi, duk a wofi. Ya kan ce, “Mu ba mu hana ku bara ba, amma ba mu yarda ku je kuna yi wa karuwai hidima ba.”

Habawa, ai wannan maganar ta bayan kunnen D’ankawu ta bi ta wuce. Kafin a ankara, sai ya b’ace daga makarantar, aka neme shi aka rasa.

*

Sai da aka yi ak’alla mako biyu ana cigiyar D’ankawu sa’annan aka zo aka ce wa Alaramma ai Ladi Lallausa ce ta tafi da shi ganin gida can cikin k’asar Bendel, wai yana rik’e mata jaka. A ranar, Alaramma da kan sa ne ya yi wa D’ankawu bulala har ana rik’e shi. Alaramma ya harzuk’a, yana ta cewa, “Allah wadaran ka D’ankawu! A ce ka zo karatun Muhammadiyya amma ka b’ige ga bin karuwa yawon banza! Sai na aika an gaya wa uban ka!”

Ashe shi ma Alaramma aikin banza ya yi. Domin kuwa D’ankawu ya zama kangararre. Tun daga wannan ranar, bai ma k’ara kwana a makarantar ba. Ya kwashe inasa-inasa ya koma gidan Ladi. Da ma akwai wata k’awar ta da ke ta hak’on sa, don haka shi da ita suka bud’e sabon shafin rayuwa, suka shiga karatun shed’an. Alaramma ya aika da sak’o D’anrafi, aka fad’a wa mahaifin D’ankawu. Shi kuma ya garzayo wai ya tafi da d’an sa. Ina! Ai wanda ya yi nisa ba ya jin kira. Haka nan ya koma gida shi kad’ai, domin D’ankawu ya nuna masa cewa shi fa ya samu aikin yi yanzu. Ya zama karen mota.

*

D’ankawu dai bai koyi wani abin kirki a makaranta ba saboda bai zauna ba. D’an karatun da ya iya bai fi cikin cokali ba. Ya kan ce, “Na dai samu na sallah, don haka me ake bid’a kuma?”
To amma da wuya ka ga ya yi sallar. Tuni ya iya shan taba da giya, da zuwa silima, ban da neman mata da ya gwanance a kai. Ya kan bi ubangidan sa har cikin Kurmi, suna safarar kayayyaki. Ya aje wata k’asumba babu ko kyan gani, idanun sa sun ja jawur sai ka ce wanda ya fito daga cikin gobara. Haka dai ya ci gaba da rayuwa har aka yi shekaru masu yawa. Ko ganin gida bai damu ya je ba, yana cewa wai sai ranar da ya mallaki tasa motar ta kan sa sannan zai je gida. Har uban sa ya mutu, aka dad’e bai sani ba.

*

A cikin wad’annan shekaru, Khalid ya yi saukar karatu har ya shiga littattafai, ya yi zurfin gaske. Ban da karatun da ya yi a makarantar Alaramma Malam Usman, ya rik’a zuwa wasu makarantu biyu – d’aya a kusa da gidan Sarki, d’aya kuma a Gwammaja – inda ya koyi karatu mai zurfi a wurin wasu shaihunnai. Daga bisani ma Gwamnati ta biya masa kud’in zuwa k’aro karatu a Alk’ahira, ya je ya yiwo ya dawo. Larabci a bakin sa sai ka ce rak’umin Madina. Kai, har Turanci ma yana ji rad’au, domin ya tsaya ya koya. Sunan sa na da ya fara b’acewa, sai dai Ustaz Khalid. Bai jima da dawowa ba sai Alaramma Usman (wanda tuni tsufa ya lank’wasar da shi) ya fitar da shi daga gandu, ya ce shi ma ya tafi ya nemi rabon sa. Kamar an yi shiri, sai Alhaji Murtala D’anrafi, wannan wanda aka sa a makarantar boko a D’anrafi lokacin da aka b’oye su Khalid, wanda kuma ya zo Kano har ya bunk’asa, ya sa aka kira shi, ya nad’a shi shugaban wata sabuwar kwalejin Arabiyya da ya kafa a unguwar su. Kuma ya ba shi gida da mota, kuma ya had’a shi da wata d’iyar abokin sa mai ilimi mai kunya, aka d’aura musu aure. Ai fa shi ke nan, Khalid ya zama d’aya daga cikin manyan garin. Cikin k’ank’anen lokaci sunan sa ya koma Shehi Khalid. Kuma duk wani taro na malamai sai ka gan shi a wurin, kuma su ne suke zama a kujerun gaba-gaba. Ya aje gemu da saje mai kyau, jikin sa ya yi sumul ba k’urarraji, kuma ya kan sakaya idanun sa cikin wani farin gilashi wanda ke k’ara masa kwarjini. Ga shi dai matashi mai matsakaitan shekaru, amma idan ya shige cikin manyan shaihunnai da k’yar ake iya bambance shi. Da ma an ce yaro da gari abokin tafiyar manya.

*

Wata rana wajen goshin la’asar, Shehi Khalid yana tafiya a motar sa, shi da d’an sa d’an shekara uku mai suna Adamu, daidai wani gosulo sai ya ji an tunkuyar masa mota daga baya. Ya waiga sai ya ga wata mummunar tifa ce ta kusa markad’e su yayin da burki ya shanye mata. Ya tsaya ya fito domin ya duba irin b’arnar da aka yi masa. Shi ma mai tifar ya fito.

Malamin ya fito kenan sai mai tifar ya shiga yarfa masa bak’ar magana, yana cewa, “Malaman nan ba ku iya mota ba sai fitinar son yin tuk’i. Rik’e sikiyari fa ba jan carbi ba ne! Wallahi ka taki sa’a, da tuni na bi ta kan ku na wuce!”

Shehi Khalid ya dubi direban ya ce, “Maigida, ai kai ne ka tunkuye ni ba tare da ka tsaya ba. Tun d’azun na lura ka na ta bi na a gindi a gindi a guje. Don haka kai ne za a ce ba ka iya tuk’i ba!”

Jin haka sai direban nan ya hassala, ya shiga kwarfa wa Shehi zagi. Jama’a ta taru, ana ta ba su magana, kuma ana mamakin yadda direban ke zagin malami haka.

Shehi kuwa ya ma kasa magana. Can da direban nan ya sauko daga kujerar fushin sa, ya kama motar sa zai hau, sai Shehi ya ce ya dakata tukuna. Ya dube shi ya ce, “Ka san ni?”

Direban ya ce, “Na san ka kamar yaya? Ina ruwa na da in san ka? Kud’i na ke nema, ka ji, ba lada ba!”

Shehi ya yi kamar bai ji abin da direban ya ce ba, ya ce masa, “Ba kai ba ne D’ankawu yaron Alhaji Inusa Sarkin Taya? To, idan ka kasa gane ni, ni ne D’an’uwan ka Khalid, wanda ku ka zo karatu tare daga D’anrafi. Allah ya ba ka hak’uri! Ka ga tafiya ta.”

Da fad’in haka, sai Shehi ya hau motar sa ya yi gaba, ya bar D’ankawu a nan bakin sa a bud’e galala, mutane na ta yi masa dariya. Bayan kamar minti d’aya sai D’ankawu ya yi wuf ya d’are kan motar sa, ya shek’a a guje ya bi hanyar da Shehi ya bi.

*

A gidan Shehi, D’ankawu ya yi ta ba malamin hak’uri, ya na cewa wallahi bai san shi ba ne. Almajirai da gardaye suka yi ta dariya.

Shehi Khalid ya yi murmushi ya ce, “Maganar ita ce, ba lallai ba ne sai idan wanda ka sani ne za ka raga masa.” Nan take ya kawo masa ayoyi da hadisai don nuna masa kuskuren sa tare da neman gyara su. Kuma ya ce ya yafe wa D’ankawu.

Gogan naka bai san lokacin da hawaye suka zubo masa ba. Kuma nan take ya shiga nadamar irin rayuwar da yake yi irin ta ashararai. Ya tuno da yadda suka zo birnin Kano, har ana ganin kamar zai fi Khalid samun karatu. Ga shi nan ya zama bankaura kawai, ko izifi d’aya bai iya kawowa da ka. Ya yanke shawarar cewa daga yau ya tuba, ba zai k’ara neman mata ko shan giya ba. Kuma ba zai k’ara zagin kowa ba. Ya yanke shawarar cewa daga yau ya sauya rayuwar sa baki d’ayan ta, don yin koyi da halayen mutanen kirki. Wato dai mutane irin su Shehi Alhaji Khalid.

TAMAT

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *