Juyin zamani: Tsakanin gaɗa, Asauwara, Mamman Shata da ‘yan fiyano

Waƙoƙin gaɗa su ne a wani zamani a ƙasar Katsina da wasu yankunan Kano irin su Bichi, Tofa da Gwarzo ake kira “Asauwara”. Da farko ana kiran su “Takojilo” ne, amma daga baya sai aka “sauwara” su, wato aka juya su ta yadda samari ma za su iya shiga a yi da su maimakon ‘yan mata kaɗai.

A daidai lokacin yarintar Mamman Shata, wato a wajajen farko zuwa tsakiyar shekarun 1930s, waƙoƙin Asauwara ake yi, inda mace za ta shiga fage a gaban mai ganga ta yi waƙa a amsa, sannan namiji ma ya shiga ya rera a amsa. Wani lokaci kuma namiji da mace za su iya shiga tare su rera, sauran samari da ‘yanmata na amsawa. Mawaƙan ne ke ƙirƙirar waƙa, ko kuma su ɗauko daga waƙoƙin gaɗa da aka gada kunne-ya-girmi-kaka.

Asauwara gasa ce, domin so ake a ga wanda ya fi iya waƙa. Saboda yadda ake gasar, akan kuma kira ta da “wasan sauri”, don haka ba za ka shiga fage ka je ka na wata in’ina ba; yanzu alƙalan gasar sa fitar da kai!

An fi yin gasar Asauwara da kaka, lokacin ba a zuwa aiki gona.

Duk wanda ya yi zarra a gari ko ƙauye, to ana ba shi muƙamin Joji. To kuma sai a haɗa gasa tsakanin Jojin wannan gari da na wancan gari, a ga wanda zai yi zarra, kamar yadda ake haɗa wasan ƙwallo tsakanin garuruwa a yanzu. An sha samun joji mace ko namiji a gari kaza.

Idan za a yi gasar, su matasan da aka zo garin su su ne za su ba baƙi abinci da wurin kwana.

Shata na daga cikin matasan da ke shiga gasar Asauwara. Kuma ba da jimawa ba ya yi zarra, aka naɗa shi Joji na Musawa. Kuma an tabbatar da cewa babu wani joji da ya taɓa buge shi tun daga lokacin da ya hau muƙamin.

Wasan gaɗa na Asauwara ba sana’a ba ce. Wargi ne kurum na yara. Don haka iyaye ba su damu ba, tunda sun san cewa da yaro ya girma ya zama mutum, misali a ce ya yi aure, to tilas ya daina domin ga surukai ya yi a gari, kuma ƙannen sa sun data. Idan mace ce ma, ta tafi gidan miji.

A wancan lokacin, akwai makaɗa na daban, ‘ya’yan gado, masu kiɗa don a ba su kuɗi. Waɗannan su ne masu sana’ar roƙo. Su kan yi a gidan mutum idan ya na da wani sha’ani, misali suna ko aure ko naɗin sarauta, ko su yi a dandali a taru a kalla. Duk yaron da ya ce zai zama mawaƙin da za a ba wata kyauta, in dai ba gado ya yi ba, to iyayen sa ba za su amince ba. Wasu iyayen ma, musamman Fulani, su na kallon kiɗan roƙo a ƙasƙance.

Hakan ce ta sa lokacin da Jojin Musawa, wato Shata, ya fara karɓar kyauta sai ran mahaifin shi ya ɓaci. Ya za a ce ɗan cikin sa, Bafillace, ya zama maroƙi? Abin kamar saɓo! Akwai ma lokacin da ya je ƙofar gidan Malam Inde (Magajin Gari) da ya ji ga Shata can ya na waƙa, ya lafta masa duka da igiyar ɗaure awaki da ya riƙo, ya kore shi. Ya zuwa lokacin, har Shata ya fara fita zuwa wasu garuruwa don yin waƙa. Bakin alƙalami ya riga ya bushe!

Daga baya dai, waƙa ta zame wa Shata babbar sana’a. Har sai da ya bar garin su kwata-kwata, ya kutsa duniya a matsayin maroƙi, har ta kai babu kamar shi a ƙasar Hausa duka.

Da yawa daga cikin waƙoƙin Shata da mu ke ji a yau (ko wasu kalmomin su ko amshin su) daga Asauwara su ka fito. Misali, waƙar Ayuba Mainama, waƙar Inyonyore, waƙar Gulbin Karaɗuwa, waƙar “Ayyaraye Duniya Labari”, waƙar “Ahayye Alewa!” waƙar “Ke Bushiya!” da sauran su.

To amma akwai lokacin da yayin Asauwara ya wuce, aka ci gaba da wasannin gaɗa na ‘yanmata, wato samari su ka janye. Idan ka ga namiji na waƙa, to ko dai gado ya yi ko kuma “haye” ya yi saboda wani dalili.

A lurar da na yi, su ma wasannin gaɗar sun ja baya yanzu. Ko a karkara ba a kowane ƙauye ne ‘yanmata ke zuwa dandali su yi rawa da waƙa ba.

Waƙoƙin gargajiya baki ɗaya ma sun ja baya sosai. Ga shi dai akwai ɗaiɗaikun mawaƙan gargajiyan, irin su Surajo Mai Asharalle, Shehu Ajilo Ɗanguziri, Musa Ɗanbade, Aminu Shatan Zazzau, iyalan Ɗanƙwairo, Nasiru Garba Supa, Babangida Kakadawa, Sanusi Shata, da sauran su, to amma ba a cika neman su ba. Ko biki ya tashi sai ka ga an gayyato mawaƙan fiyano irin su Fati Nijar, Maryam Fantimoti, Adam A. Zango, Ali Jita ko Ado Gwanja su ci bikin. Wasu ma ‘yan Kudu irin su Korede Bello ko D’Banj za ka ga sun kira. Idan ba a iya ɗauko irin su, sai a saka faifan su na sidi ko dibidi, kiɗan na fita daga lasifika. Da haka mata za su tiƙi rawa, su gwangwaje abin su.

Zamani kenan, telan kowane lokaci mai ɗinka wa kowa riga da bante daidai da shi!

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *