Irin ‘ya’yan wannan zamanin

Wai waɗanne irin ‘ya’ya ne mu iyaye mu ke haifa a wannan zamanin? Shin mun yarda haƙƙin mu ne ko me su ka zama da kuma ko me su ke aikatawa a cikin al’umma? Idan su ka zama na kirki ko kuma su ka lalace, shin za mu ce a dalilin tarbiyyar da mu ka yi masu ne? Waɗannan tambayoyin sun yi ta walankeluwa a rai na a tsawon lokaci. Sun fara yawo a zuciya ta, tare da yin ƙalubale ga tunani na, tun lokacin da aka ce an kama wani matashi ɗan babban gida, wato Umar Faruk Abdulmutallab, da laifin wai ya yi ƙoƙarin tada bam a cikin jirgin sama lokacin da su ka ƙaraci birnin Detroit na ƙasar Amurka, a ranar 25 ga Disamban da ya wuce. Tambayar da jama’a su ka yi ta yi a lokacin ita ce: don me zai yi hakan? Me ya ke buƙata a rayuwa? Masu zargin sa da aikata laifi dai sun ce wai ƙungiyar Alƙa’ida ce ta sa shi.

Babbar tambayar da ta dugunzuma ni, ta faru ne a makon jiya lokacin da labari ya ɓulla cewa wani matashin ya yi wa uwar sa da uban sa da ƙannen sa uku kisan gilla a Kano. Kisan gillar, wadda aka yi a daren Lahadi, ta sa na ɗau alƙalami da nufin yin sharhi kan yadda aikata muggan laifuka a ƙasar nan ya ke ƙara yawaita. Shi magidancin da aka kashe a Kano ɗin, kamar yadda ku ka ji a labarai, jami’in hukumar tsaron ƙasa ta SSS ne, wato Alhaji Garba Bello. An kashe shi ta hanyar yanka da wuƙar ɗakin girki shi da kusan dukkan iyalin sa in ban da mutum biyu. Jini ya kwarara a gidan, abin ba kyan gani.

Da farko, tun kafin a ce ɗan mutumin ne ya yi kisan, na yi matuƙar girgiza kan rashin tausayin da aka nuna wajen kisan. Wane irin laifi ne wannan bawan Allah ya yi da har za a ce an shafe shi daga doron ƙasa tare da duk iyalin sa a irin wannan mugun yanayi? Wane mara imani ne zai ma yi tunanin aikata hakan a matsayin ramuwa? A rai na, na ce tilas ne duk wani mai ɗaukar albashi da sunan aikin tabbatar da tsaro da zaman lafiya a ƙasar nan ya tabbatar da cewa an gano makisan waɗannan mutanen. Kada ‘yan sanda su yi ƙasa a gwiwa wajen gano waɗannan makisan marasa imani!

To amma kaɗuwar da na yi ta farko kan kisan ba ta kai ko cikin cokalin wadda na yi ba washegari da sabon labari ya ɓulla: wai Bello ne, wato babban ɗan marigayin da marigayiyar, ya kashe su! Inna lillahi wa inna ilaihir raji’un! A cewar kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Kano, Alhaji Mohammed J. Gana, wai Bello (wanda aka fi sani da suna Baba) shi ne ya tafka wannan ta’asa saboda ya yi imani da cewa mutan gidan su za su shiga halin ha’ula’i idan mahaifin sa, wanda ba shi da lafiya, ya rasu.

Wannan abu ya fi ba ni mamaki fiye da ainihin kisan domin kuwa ya jefa ni a kogin tunani kan makomar mu ta kiran kan mu da sunan bil’adama da mu ke yi, wato masu hankali da sanin ya-kamata da kuma karɓar ƙaddara ko wace iri ce. Tambayoyin da ake ta yi a ƙasar nan su ne: wane irin abu ne zai sa ɗa ya halaka uwar sa da uban sa da ƙanne uku – biyu mata, namiji ɗaya? Shin ya haukace ne baki ɗaya a lokacin? A gaskiya, ba a taɓa aikata mugun abu irin wannan a Kano ba tun cikin 2006 lokacin da wani matashin ya kashe Hajiya Sa’adatu Rimi, wadda matar uban sa ce, wato tsohon gwamnan jihar, Alhaji Abubakar Rimi.

Wannan kisan gilla da aka yi ya fita daga cikin da’irar hankali, kai ka ce ba a nan ƙasar ya faru ba. Mu dai mu kan karanta a jarida ko mu gani a talbijin cewa an yi irin wannan kisan kiyashin a wata ƙasar Turawa, inda da ma son abin duniya, da zaman ‘yan marina da kuma yin watsi da ƙa’idojin addini sun sa an yi fatali da kyakkyawar tarbiyya. Mu a nan Nijeriya, sai a daɗe ba ka ji wani ya kashe mahaifin sa ko uwar sa ko kuma shi kan sa ba, kuma idan har irin hakan ya faru mutane su kan yi matuƙar al’ajabi tare da tsananin fargaba. A kan dubi wanda ya aikata irin wannan ta’asar a matsayin dabba mai sunan mutum.

Dalilin da aka ce Bello ya bayar na yin kisan duk shirme ne, kuma kame-kame ne na mutumin da ƙwaƙwalwar sa ta taɓu. Don an kore shi daga jami’a inda ya ke karatu ba hujja ba ce da ke nuna cewa rayuwar sa ta zo ƙarshe daga nan; akwai matasa da yawa irin sa, ko ma waɗanda ba su kai shi galihu ba, kuma su kan ci gaba da yin rayuwar su har su more ta a wasu sassan na rayuwar ɗan’adam. Haka kuma, ci gaba da rayuwar iyayen sa da ‘yan’uwan sa ba haƙƙin sa ba ne. Abincin su da sauran buƙatun su na rayuwa duk su na hannun Maiduka. Tunanin da aka ce ya yi na aikawa da su barzahu don kautar da su daga faɗawa cikin fatara da yunwa, sam, ba ya cikin tunani nagari.

Da farko, Bello ya amince da aikata laifin, domin an gabatar da shi a gaban manema labarai inda ya amince ɗin. To amma daga bisani dai labarin ya fara sauyawa. Ran Alhamis ta makon jiya, wani kawun Bello ya yi iƙirarin cewa ba Bellon ba ne ya aikata ta’asar, wai jami’an tsaro ne su ka tilasta masa har ya yi wancan furucin. Sannan shi ma Bello, da aka kai shi kotu ran Litinin da ta wuce, ya musanta zargin cewa shi ne ya yi kisan. To yanzu dai ya rage ruwan kotu ta yanke hukunci kan wannan sabon zancen. To amma mu a namu ɓangaren, maganar farko da aka yi ta sa tilas mu tsaya tsayin daka, mu sake duban irin riƙon da mu ke yi wa matasan mu. Irin wannan ta’asar fa ta na faruwa a ƙasar nan, ko da ba ta kai zurfin wannan ta Kanon da ake magana ba: sai ka ji an ce wani yaro ya kashe uban sa ko uwar sa a kan wani ɗan saɓani da bai taka kara ya karya ba. Ko kwanan nan, irin haka ta faru a Jihar Katsina, inda wani ya daɓa wa uban sa wuƙa, ya aika da shi lahira. A makon jiya ma, a Legas, an kwata irin wannan, inda wani ya kashe uban sa. A yau Juma’ar nan ma da mu ke magana, jaridar Aminiya ta ruwaito yadda wani ma’aikacin kurkuku ya kashe ‘ya’yan sa tagwaye.

Sau da yawa, ba mu damu ba idan mun ji an yi irin wannan ta’asar, a tunanin mu ai ba mu abin ya shafa kai-tsaye ba. Mun manta da cewa a gidan wasu ko gidan maƙwabtan su, abu ne mai ciwo ya faru. A ko yaushe fa ana yin kisan gilla a ƙasar nan, wanda ya kan haifar da ciwo a zukata da dama. Rayuwa su na ta salwanta a yayin da rigingimu ke ƙaruwa. Ga dai fashi da makami da kuma rikicin addini, wanda duk su na cin rayuka masu yawa. Ana kisan kai ma a harkar siyasa, inda wasu ‘yan siyasar da ke gaba da junan su su kan yi hayar ‘yan iskan gari, waɗanda yawanci matasa ne, don su halaka abokan gabar su. Wata sa’a, jami’in gwamnati za ka ji an kashe, wato kamar jami’in EFCC ɗin nan da aka bindige a gidan sa a Kaduna a ran Litinin ta makon jiya. Wata sa’a kuma, ‘yan jarida ake kashewa, kamar dai Bayo Ohu na jaridar The Guardian.

Dole ne mu tashi tsaye cikin hanzari mu samo maganin matsalar. Iyaye ne ya kamata su fara ɗaukar mataki na farko wajen cusa tarbiyya a rayuwar ‘ya’yan su tun su na ƙanana. Tarbiyya daga gida ta kan fara. Hausawa dai na cewa icce tun ya na ƙarami ake tanƙwara shi. A wannan zamanin, sai ka ga iyaye da dama – musamman ma mazan – ba su da lokacin kula da abin da ke faruwa a gidajen su, su na can su na neman abinci ko ƙarin dukiya. Na biyu, tilas ne gwamnati ta riƙa sauke nauyin da ya rataya a wuyan ta na samar da ilimi mai nagarta da kuma aikin yi ga matasa. Tun tuni harkar ilimi ta zaganye, makarantu sun zama abin da su ka zama, ba su iya amfanar da al’umma kamar yadda ya kamata, domin ko da yaro ya gama karatun sai ka ga zuƙu ne kawai ya yi ko mu ce karatun aku. Don haka sai ya kasa samun aiki. Idan kuwa har babu nagartaccen ilimi, sai matasan mu su kasance ba su ɗaukuwa a wuraren aiki, wanda hakan kan sa su zama abin nema ga muggan mutane masu baƙar niyya.

A yau, matasan mu sun raja’a ga bin munanan halaye, ciki kuwa har da shaye-shaye ko kallon hotuna da finafinan batsa. Kuma a ƙoƙarin su na samun abin sakawa a bakin salati, sai su koma su na aikata laifuffuka da kuma nau’o’in karuwanci. Ba mu damu da abin da su ke karantawa a wasu littattafai da mujallu ko intanet ba, ko abin da su ke gani a cikin wasu finafinan, ko kuma abin da su ke saurare a wasu waƙoƙin.

A yayin da hakan ke faruwa, shugabannin mu su na can su kuma su na wawure dukiyar ƙasar. Sai ka ga fatara da yunwa na ƙaruwa a yayin da ake tafka cin hanci da rashawa. Hakan na ƙara haifar da yawaitar muggan laifuffuka. Sakamakon duk wannan su ne irin munanan abubuwan da ba mu so mu gani da idon mu ko mu ji da kunnen mu. Abin takaicin ma shi ne, ba mu so a ɗora mana laifin kasawar da mu ka yi. To amma ita gaskiya, gaskiya ce, kuma dole mu fuskance ta. Sannan idan mun dubi fuskar ta, sai mu kau da kai domin babu kyakkyawar sura gare ta saboda yadda mu ka bari ta munana. Da ma Hausawa sun ce wanda bai ƙi ji ba, ba zai ƙi gani ba.

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *