{"id":5726,"date":"2026-03-29T14:01:14","date_gmt":"2026-03-29T14:01:14","guid":{"rendered":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5726"},"modified":"2026-05-11T15:59:16","modified_gmt":"2026-05-11T15:59:16","slug":"5726","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5726","title":{"rendered":"Tuna Baya: Yadda Ha\u0257arin Jirgin \u0198asa Na Langa-langa Ya Faru A 1970"},"content":{"rendered":"<p>Ha\u0257arin jirgin \u0199asa na Langa-langa yana \u0257aya daga cikin ha\u0257urra mafi muni a tarihin safarar jiragen \u0199asa a Afrika. Ha\u0257arin Langa-langa ya faru ne a ranar 16 ga Fabrairu, 1970 kusa da \u0199auyen Langa-langa da ke \u0198aramar Hukumar Akwanga a Jihar Nasarawa ta yanzu, jim ka\u0257an bayan kammala Ya\u0199in Basasar Nijeriya.<\/p>\n<p>A wancan lokaci, Hukumar Jiragen \u0198asa ta Nijeriya (NRC) tana gudanar da jiragen fasinja da na jigilar kaya tsakanin Arewacin Nijeriya da yankin Gabas. Tafiya ta jirgin \u0199asa ta bun\u0199asa sosai domin tana da arha kuma ana ganin ta fi ta mota aminci.<\/p>\n<h4>BALA&#8217;I A LANGA-LANGA<\/h4>\n<p>Jirgi ne ya tashi daga Jos a kan hanyar sa ta zuwa Lafiya, hedikwatar Jihar Nasarawa a yau. Daga Lafiya, zai zarce ne zuwa Makur\u0257i sannan ya gangara zuwa Gabashin Nijeriya. Da ya zo tashar garin Gudi, ya \u0257an yada zango domin masu sauka a nan su sauka, wasu fasinjojin kuma su hau.<\/p>\n<p>Jirgin, mai amfani da man dizal, ya cika ma\u0199il da fasinjoji, saboda an ba da hutun Babbar Sallah, mutane suna hanyar zuwa bikin Sallah.<\/p>\n<p>Jim ka\u0257an bayan jirgin ya bar Gudi, sai ya isa wata muguwar kwana kusa da \u0199auyen Langa-langa. Kwatsam, sai kan jirgin, ya goce daga kan layin dogo a daidai kan kwanar. Kafin ka ce kwabo, gaba \u0257aya kan jirgin tare da taragai hu\u0257u na farko suka antaya cikin rami mai zurfin kusan mita 25.<\/p>\n<p>Ha\u0257arin ya haddasa mummunar \u0253arna, inda wasu taragai suka mur\u0257e gaba \u0257aya, wasu kuma suka kama da wuta. Fasinjoji da dama suka mutu nan take, wasu suka ji mugun rauni. Da yawa suka ma\u0199ale cikin \u0199arafan da suka mur\u0257e, ga kuma kaya sun danne wasu.<\/p>\n<p>Har yau babu tabbacin adadin mutanen da suka mutu, saboda bayanan lokacin ba su cika ba. Yawancin rahotanni sun yi hasashen cewa a\u0199alla mutum 150 ne suka mutu, wasu bayanan kuma suka ce mutum 80, har ma 400 ko fiye ne suka mutu.<\/p>\n<h4>LABARIN BAN-TAUSAYI<\/h4>\n<p>\u018aaya daga cikin labarai masu ban-al&#8217;ajabi da ta\u0253a zuciya game da ha\u0257arin shi ne abin da wasu fasinjoji suka ji bayan jirgin ya fa\u0257i. A cewar su, abin da ya fi firgita su shi ne a cikin duhun daren, sun ri\u0199a jin hargowar wa\u0257anda suka samu munanan raunuka suna ro\u0199on don Allah a kawo masu taimakon gaggawa. Muryoyin mutanen suna raguwa a hankali yayin da lokaci ke tafiya, wasu kuma suna daina magana gaba \u0257aya.<\/p>\n<p>Wani da ya tsira daga ha\u0257arin ya ba da labarin cewa: \u201cA cikin duhu muna jin mutane suna kiran \u2018ku taimake mu!\u2019 daga cikin taragogin da suka mur\u0257e. Wasu suna addu\u2019a, wasu suna kuka.\u201d Wani wanda ya tsira ya ce wannan shi ne abin da ya fi tsoratar da shi a rayuwar sa, domin ba zai ta\u0253a mantawa da muryoyin wa\u0257anda suka ma\u0199ale suna ro\u0199on a agaje su ba.<\/p>\n<h4>MUHIMMANCI A TARIHI<\/h4>\n<p>A duk Afrika, ana kwatanta fa\u0257uwar jirgi ta Langa-langa da wadda ta ya fi shi muni, wato wadda ta faru daga baya a ranar 10 ga Yuni, 2001, a yankin Uige na \u0199asar Angola. A ha\u0257arin, bam ne jirgin ya taka, irin wanda ake dasawa a \u0199asa a lokacin ya\u0199in basasar Angola. Bam \u0257in ya fashe, wanda ya sa jirgin ya fa\u0257i, ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 250 tare da raunata wasu da dama.<\/p>\n<p>Dangane da ha\u0257arin Langa-langa, an ri\u0199a yin zargi iri-iri. Wasu sun ce ma\u0199ar\u0199ashiya ce wasu &#8216;yan Biyafra suka shirya, wai yana da ala\u0199a da Ya\u0199in Basasa da aka yi. Jim ka\u0257an da faruwar ha\u0257arin, Gwamnatin Tarayya ta kafa kwamitin bincike na musamman kan ha\u0257arin da kuma bayar da shawarwari kan yadda za a inganta tsaron jiragen \u0199asa a Nijeriya.<\/p>\n<h4>RASHIN ISASSHEN AGAJI KO CETO<\/h4>\n<p>Ayyukan ceto sun kasance masu matu\u0199ar wahala a wurin ha\u0257arin saboda \u0199arancin kayan aiki, ga shi kuma wurin yana da nisan gaske da gari, kuma jirgin ya ragargaje \u0199warai.<\/p>\n<p>An ce likitoci sun ri\u0199a yanke wasu sassan jikin fasinjoji &#8211; kamar \u0199afafu ko hannaye &#8211; domin su samu damar fito da su daga cikin mushen jirgin. An kwashi wasu daga cikin wa\u0257anda suka tsira zuwa asibiti a mota, amma \u0257aya daga cikin motocin ta fa\u0257a cikin wani kogi, wanda hakan ya haddasa \u0199arin mutuwar wasu mutane. Hakan ya sa abin da ya faru ya zama bala\u2019i sau biyu, wanda ya \u0199ara yawan wa\u0257anda suka mutu.<\/p>\n<p>Wasu ganau sun ce ma\u2019aikatan ceto sun kasa fitar da mutane da dama da suka ma\u0199ale a cikin ramin da jirgin ya fa\u0257a. A wasu rahotanni da aka fitar daga baya, an ce wasu jami\u2019ai sun yanke shawarar a \u0199ona jirgin ma kawai, wai saboda kada wa\u0257anda suka ma\u0199ale su ci gaba da azabtuwa tunda ba zai yiwu a ceto su ba. Wannan zargin ya jawo fushin jama\u2019ar Nijeriya sosai a lokacin.<\/p>\n<p>An ce wannan yanayin ya \u0257auki sa\u2019o\u2019i da dama saboda rashin isassun kayan aikin ceto kuma wurin da aka yi ha\u0257arin yana da nisa.<\/p>\n<p>Wasu shaidu sun ce akwai mutane da \u0199afafun su suka ma\u0199ale a \u0199ar\u0199ashin \u0199arfe, wasu kuma kaya sun danne su.<\/p>\n<h4>LABARIN MAI RABON GANIN BA\u018aI<\/h4>\n<p>\u018aaya daga cikin labarai da aka ri\u0199a yawan ambato game da ha\u0257arin shi ne labarin wani fasinja da ya tsira. Mutumin yana cikin jirgin daga Jos zuwa Gudi. Da aka tsaya, sai ya sauka domin ya sayi ruwa ko abin sha, ko kuma ya \u0257an mi\u0199e \u0199afafun sa saboda gajiyar zama cikin jirgin mai cunkoso.<\/p>\n<p>Lokacin da yake waje, sai aka buga \u0199ararrawar tashin jirgin. Kafin mutumin nan ya ankara, jirgi ya motsa. Da ma Shata ya fa\u0257a a wa\u0199ar Ummaru \u0257an \u018aanduna cewa, &#8220;Jirgi ba ya jiran uban wani.&#8221; Mutumin nan ya yi \u0199o\u0199arin sake komawa jirgin, amma ya kasa. Haka aka tafi aka bar shi a tasha, ya tsaya yana jiran jirgi na gaba. Bayan wani lokaci, labarin fa\u0257uwar jirgin kusa da Langa-langa ya zo.<\/p>\n<p>Da mutumin nan ya ji labarin, ya ka\u0257u matu\u0199a. Ya gode wa Allah da ya hana shi sake hawa jirgin, domin kuwa da ya hau \u0257in, to wata\u0199ila shi ma da sai buzun sa. Ya ri\u0199a fa\u0257in: \u201cAllah ne ya sa na sauka a tashar a lokacin.\u201d<\/p>\n<p>Da ma Hausawa suna cewa mai rabon ganin ba\u0257i, ko ana mazuru ana shaho sai ya kai.<\/p>\n<h4>WANI ABU MAI BAN-MAMAKI DA AKA SAMU BAYAN HA\u018aARIN<\/h4>\n<p>Shekaru da dama bayan ha\u0257arin, mutanen da suka ziyarci wurin sun ri\u0199a hango wasu sassa na mushen jirgin a cikin ramin da ya fa\u0257a. Rahotanni daga wasu \u2018yan jarida da suka je wurin shekaru bayan ha\u0257arin sun ce sun ga wasu manyan sassan \u0199arafunan jirgin da suka kasance a wurin a tsawon lokaci. Sai dai kuma yanzu duk &#8216;yan gwangwan sun yashe su sun sayar. Yanzu wurin ya cika da ciyawa da bishiyoyi saboda an bar shi babu wani gyara.<\/p>\n<p>A tsawon lokaci, mutanen \u0199auyukan da ke yankin sukan je kallon wurin ha\u0257arin. Wurin ya zama wani \u0253angare na tarihin su.<\/p>\n<h4>MURYOYIN FATALWA KO SHACI-FA\u018aI?<\/h4>\n<p>Wasu mazauna yankin sun ce har yau ana jin muryoyi kamar na mutane suna magana ko kuka daga cikin dajin da aka yi ha\u0257arin. Wasu kuma sun ce wai ana jin sautin \u0199arfe kamar ana bugun jirgi a wurin.<\/p>\n<p>Hakan ya sa mutane dama suna guje wa wucewa ta kusa da wurin da dare, musamman a shekarun farko bayan ha\u0257arin.<\/p>\n<p>An kuma ce wasu makiyaya ko matafiya da ke bi ta yankin sukan guji yin zango kusa da wurin ha\u0257arin, ko wucewa ta wurin da dare. Wasu sun ce suna jin tsoro ko wani yanayi na damuwa idan har sun bi ta wurin.<\/p>\n<p>Sai dai kuma wasu na ganin cewa duk wa\u0257annan labarai shaci-fa\u0257i ne ko ji-ta-ji-ta kawai, kuma suna faruwa ne saboda girman bala\u2019in da ya faru.<\/p>\n<p>Sau da yawa, idan wani babban bala\u2019i ya faru a wuri, mutane sukan \u0199ir\u0199iri labaran al\u2019ajabi su li\u0199a wa wurin, su camfa shi.<\/p>\n<p>Ha\u0257arin Langa-Langa yana da muhimmanci a tarihin Nijeriya saboda yana \u0257aya daga cikin mafi muni a harkar sufuri a \u0199asar. Bugu da \u0199ari, ya hasko tulin matsalolin tsaro a tsarin sufurin jiragen \u0199asa na \u0199asar nan, sannan ya kasance wata alama ta yadda bun\u0199asar layukan jirgin \u0199asa ta Nijeriya ta fara raguwa, wa\u0257anda a da suka kasance masu matu\u0199ar aiki. Fasinjoji sun ri\u0199a fargabar shiga jirgin \u0199asa.<\/p>\n<h4>HA\u018aARIN LANGA-LANGA A ADABIN HAUSA<\/h4>\n<p>Sakamakon ha\u0257arin jirgi na Langa-langa, Alhaji Ahmadu Doka mai kukuma ya yi wa\u0199a mai taken &#8216;Ta Cinye Maza Sai Toka Langa-langa&#8217;.<\/p>\n<p>Ya yi wa\u0199o\u0199i biyu a kan ha\u0257arin. Ta farkon, ya yi ta shi ka\u0257ai, ta biyun kuwa tare da &#8216;yan amshi.<\/p>\n<p>Wannan ya sa ha\u0257arin ya shiga kundin adabin baka na Hausa.<\/p>\n<h4>KAMMALAWA<\/h4>\n<p>An tabbatar da cewa wannan ha\u0257ari ya kasance babban ibtila\u2019i a tarihin Nijeriya. Girman sa ya sa mutane suka dinga ba da labarai barkatai game da shi, kuma har yau ana tunawa da shi a tarihin jiragen \u0199asa na \u0199asar nan.<\/p>\n<p>Sai dai kuma babu tabbacin idan gwamnati ta bayyana rahoton kwamitin bincike da ta kafa kan ha\u0257arin. Sannan babu tabbacin idan ta biya diyya ga iyalan wa\u0257anda suka mutu da wa\u0257anda suka ji rauni tare da asarar dukiya a ha\u0257arin. Idan kuwa haka ne, to fatalwar ha\u0257arin Langa-langa tana nan tana yawo a cikin tarihin safarar jiragen \u0199asa ta Nijeriya kenan.<\/p>\n<p>To, Allah ya kiyaye gaba, amin.<\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div>\n<p id=\"pvc_stats_5726\" class=\"pvc_stats total_only  \" data-element-id=\"5726\" style=\"\"><i class=\"pvc-stats-icon medium\" aria-hidden=\"true\"><svg xmlns=\"http:\/\/www.w3.org\/2000\/svg\" version=\"1.0\" viewBox=\"0 0 502 315\" preserveAspectRatio=\"xMidYMid meet\"><g transform=\"translate(0,332) scale(0.1,-0.1)\" fill=\"\" stroke=\"none\"><path d=\"M2394 3279 l-29 -30 -3 -207 c-2 -182 0 -211 15 -242 39 -76 157 -76 196 0 15 31 17 60 15 243 l-3 209 -33 29 c-26 23 -41 29 -80 29 -41 0 -53 -5 -78 -31z\"\/><path d=\"M3085 3251 c-45 -19 -58 -50 -96 -229 -47 -217 -49 -260 -13 -295 52 -53 146 -42 177 20 16 31 87 366 87 410 0 70 -86 122 -155 94z\"\/><path d=\"M1751 3234 c-13 -9 -29 -31 -37 -50 -12 -29 -10 -49 21 -204 19 -94 39 -189 45 -210 14 -50 54 -80 110 -80 34 0 48 6 76 34 21 21 34 44 34 59 0 14 -18 113 -40 219 -37 178 -43 195 -70 221 -36 32 -101 37 -139 11z\"\/><path d=\"M1163 3073 c-36 -7 -73 -59 -73 -102 0 -56 133 -378 171 -413 34 -32 83 -37 129 -13 70 36 67 87 -16 290 -86 209 -89 214 -129 231 -35 14 -42 15 -82 7z\"\/><path d=\"M3689 3066 c-15 -9 -33 -30 -42 -48 -48 -103 -147 -355 -147 -375 0 -98 131 -148 192 -74 13 15 57 108 97 206 80 196 84 226 37 273 -30 30 -99 39 -137 18z\"\/><path d=\"M583 2784 c-38 -19 -67 -74 -58 -113 9 -42 211 -354 242 -373 16 -10 45 -18 66 -18 51 0 107 52 107 100 0 39 -1 41 -124 234 -80 126 -108 162 -133 173 -41 17 -61 16 -100 -3z\"\/><path d=\"M4250 2784 c-14 -9 -74 -91 -133 -183 -95 -150 -107 -173 -107 -213 0 -55 33 -94 87 -104 67 -13 90 8 211 198 130 202 137 225 78 284 -27 27 -42 34 -72 34 -22 0 -50 -8 -64 -16z\"\/><path d=\"M2275 2693 c-553 -48 -1095 -270 -1585 -649 -135 -104 -459 -423 -483 -476 -23 -49 -22 -139 2 -186 73 -142 361 -457 571 -626 285 -228 642 -407 990 -497 242 -63 336 -73 660 -74 310 0 370 5 595 52 535 111 1045 392 1455 803 122 121 250 273 275 326 19 41 19 137 0 174 -41 79 -309 363 -465 492 -447 370 -946 591 -1479 653 -113 14 -422 18 -536 8z m395 -428 c171 -34 330 -124 456 -258 112 -119 167 -219 211 -378 27 -96 24 -300 -5 -401 -72 -255 -236 -447 -474 -557 -132 -62 -201 -76 -368 -76 -167 0 -236 14 -368 76 -213 98 -373 271 -451 485 -162 444 86 934 547 1084 153 49 292 57 452 25z m909 -232 c222 -123 408 -262 593 -441 76 -74 138 -139 138 -144 0 -16 -233 -242 -330 -319 -155 -123 -309 -223 -461 -299 l-81 -41 32 46 c18 26 49 83 70 128 143 306 141 649 -6 957 -25 52 -61 116 -79 142 l-34 47 45 -20 c26 -10 76 -36 113 -56z m-2057 25 c-40 -58 -105 -190 -130 -263 -110 -324 -59 -707 132 -981 25 -35 42 -64 37 -64 -19 0 -241 119 -326 174 -188 122 -406 314 -532 468 l-58 71 108 103 c185 178 428 349 672 473 66 33 121 60 123 61 2 0 -10 -19 -26 -42z\"\/><path d=\"M2375 1950 c-198 -44 -350 -190 -395 -379 -18 -76 -8 -221 19 -290 114 -284 457 -406 731 -260 98 52 188 154 231 260 27 69 37 214 19 290 -38 163 -166 304 -326 360 -67 23 -215 33 -279 19z\"\/><\/g><\/svg><\/i> <img data-recalc-dims=\"1\" loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"16\" height=\"16\" alt=\"Loading\" src=\"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/plugins\/page-views-count\/ajax-loader-2x.gif?resize=16%2C16&#038;ssl=1\" border=0 \/><\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Ha\u0257arin jirgin \u0199asa na Langa-langa yana \u0257aya daga cikin ha\u0257urra mafi muni a tarihin safarar jiragen \u0199asa a Afrika. Ha\u0257arin Langa-langa ya faru ne a ranar 16 ga Fabrairu, 1970 kusa da \u0199auyen Langa-langa da ke \u0198aramar Hukumar Akwanga a Jihar Nasarawa ta yanzu, jim ka\u0257an bayan kammala Ya\u0199in Basasar Nijeriya. A wancan lokaci, Hukumar [&hellip;]<\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div>\n<p id=\"pvc_stats_5726\" class=\"pvc_stats total_only  \" data-element-id=\"5726\" style=\"\"><i class=\"pvc-stats-icon medium\" aria-hidden=\"true\"><svg xmlns=\"http:\/\/www.w3.org\/2000\/svg\" version=\"1.0\" viewBox=\"0 0 502 315\" preserveAspectRatio=\"xMidYMid meet\"><g transform=\"translate(0,332) scale(0.1,-0.1)\" fill=\"\" stroke=\"none\"><path d=\"M2394 3279 l-29 -30 -3 -207 c-2 -182 0 -211 15 -242 39 -76 157 -76 196 0 15 31 17 60 15 243 l-3 209 -33 29 c-26 23 -41 29 -80 29 -41 0 -53 -5 -78 -31z\"\/><path d=\"M3085 3251 c-45 -19 -58 -50 -96 -229 -47 -217 -49 -260 -13 -295 52 -53 146 -42 177 20 16 31 87 366 87 410 0 70 -86 122 -155 94z\"\/><path d=\"M1751 3234 c-13 -9 -29 -31 -37 -50 -12 -29 -10 -49 21 -204 19 -94 39 -189 45 -210 14 -50 54 -80 110 -80 34 0 48 6 76 34 21 21 34 44 34 59 0 14 -18 113 -40 219 -37 178 -43 195 -70 221 -36 32 -101 37 -139 11z\"\/><path d=\"M1163 3073 c-36 -7 -73 -59 -73 -102 0 -56 133 -378 171 -413 34 -32 83 -37 129 -13 70 36 67 87 -16 290 -86 209 -89 214 -129 231 -35 14 -42 15 -82 7z\"\/><path d=\"M3689 3066 c-15 -9 -33 -30 -42 -48 -48 -103 -147 -355 -147 -375 0 -98 131 -148 192 -74 13 15 57 108 97 206 80 196 84 226 37 273 -30 30 -99 39 -137 18z\"\/><path d=\"M583 2784 c-38 -19 -67 -74 -58 -113 9 -42 211 -354 242 -373 16 -10 45 -18 66 -18 51 0 107 52 107 100 0 39 -1 41 -124 234 -80 126 -108 162 -133 173 -41 17 -61 16 -100 -3z\"\/><path d=\"M4250 2784 c-14 -9 -74 -91 -133 -183 -95 -150 -107 -173 -107 -213 0 -55 33 -94 87 -104 67 -13 90 8 211 198 130 202 137 225 78 284 -27 27 -42 34 -72 34 -22 0 -50 -8 -64 -16z\"\/><path d=\"M2275 2693 c-553 -48 -1095 -270 -1585 -649 -135 -104 -459 -423 -483 -476 -23 -49 -22 -139 2 -186 73 -142 361 -457 571 -626 285 -228 642 -407 990 -497 242 -63 336 -73 660 -74 310 0 370 5 595 52 535 111 1045 392 1455 803 122 121 250 273 275 326 19 41 19 137 0 174 -41 79 -309 363 -465 492 -447 370 -946 591 -1479 653 -113 14 -422 18 -536 8z m395 -428 c171 -34 330 -124 456 -258 112 -119 167 -219 211 -378 27 -96 24 -300 -5 -401 -72 -255 -236 -447 -474 -557 -132 -62 -201 -76 -368 -76 -167 0 -236 14 -368 76 -213 98 -373 271 -451 485 -162 444 86 934 547 1084 153 49 292 57 452 25z m909 -232 c222 -123 408 -262 593 -441 76 -74 138 -139 138 -144 0 -16 -233 -242 -330 -319 -155 -123 -309 -223 -461 -299 l-81 -41 32 46 c18 26 49 83 70 128 143 306 141 649 -6 957 -25 52 -61 116 -79 142 l-34 47 45 -20 c26 -10 76 -36 113 -56z m-2057 25 c-40 -58 -105 -190 -130 -263 -110 -324 -59 -707 132 -981 25 -35 42 -64 37 -64 -19 0 -241 119 -326 174 -188 122 -406 314 -532 468 l-58 71 108 103 c185 178 428 349 672 473 66 33 121 60 123 61 2 0 -10 -19 -26 -42z\"\/><path d=\"M2375 1950 c-198 -44 -350 -190 -395 -379 -18 -76 -8 -221 19 -290 114 -284 457 -406 731 -260 98 52 188 154 231 260 27 69 37 214 19 290 -38 163 -166 304 -326 360 -67 23 -215 33 -279 19z\"\/><\/g><\/svg><\/i> <img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"16\" height=\"16\" alt=\"Loading\" src=\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/plugins\/page-views-count\/ajax-loader-2x.gif\" border=0 \/><\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div>\n","protected":false},"author":5,"featured_media":5728,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_FSMCFIC_featured_image_caption":"","_FSMCFIC_featured_image_nocaption":"","_FSMCFIC_featured_image_hide":"","_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[7],"tags":[510,508,511,512,509],"class_list":["post-5726","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-hausa","tag-fauwar-jirgi","tag-langa-langa","tag-nasarawa","tag-nrc","tag-train-accident"],"yoast_head":"<!-- This site is optimized with the Yoast SEO plugin v26.9 - https:\/\/yoast.com\/product\/yoast-seo-wordpress\/ -->\n<title>Tuna Baya: Yadda Ha\u0257arin Jirgin \u0198asa Na Langa-langa Ya Faru A 1970 - Ibrahim Sheme<\/title>\n<meta name=\"robots\" content=\"index, follow, max-snippet:-1, max-image-preview:large, max-video-preview:-1\" \/>\n<link rel=\"canonical\" href=\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5726\" \/>\n<meta property=\"og:locale\" content=\"en_GB\" \/>\n<meta property=\"og:type\" content=\"article\" \/>\n<meta property=\"og:title\" content=\"Tuna Baya: Yadda Ha\u0257arin Jirgin \u0198asa Na Langa-langa Ya Faru A 1970 - Ibrahim Sheme\" \/>\n<meta property=\"og:description\" content=\"Ha\u0257arin jirgin \u0199asa na Langa-langa yana \u0257aya daga cikin ha\u0257urra mafi muni a tarihin safarar jiragen \u0199asa a Afrika. Ha\u0257arin Langa-langa ya faru ne a ranar 16 ga Fabrairu, 1970 kusa da \u0199auyen Langa-langa da ke \u0198aramar Hukumar Akwanga a Jihar Nasarawa ta yanzu, jim ka\u0257an bayan kammala Ya\u0199in Basasar Nijeriya. A wancan lokaci, Hukumar [&hellip;]\" \/>\n<meta property=\"og:url\" content=\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5726\" \/>\n<meta property=\"og:site_name\" content=\"Ibrahim Sheme\" \/>\n<meta property=\"article:published_time\" content=\"2026-03-29T14:01:14+00:00\" \/>\n<meta property=\"article:modified_time\" content=\"2026-05-11T15:59:16+00:00\" \/>\n<meta property=\"og:image\" content=\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2026\/05\/20260511_145857.jpg\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:width\" content=\"1024\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:height\" content=\"553\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:type\" content=\"image\/jpeg\" \/>\n<meta name=\"author\" content=\"Nafisat@ibrahimsheme.com\" \/>\n<meta name=\"twitter:card\" content=\"summary_large_image\" \/>\n<meta name=\"twitter:label1\" content=\"Written by\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data1\" content=\"IBRAHIM SHEME\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:label2\" content=\"Estimated reading time\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data2\" content=\"7 minutes\" \/>\n<script type=\"application\/ld+json\" class=\"yoast-schema-graph\">{\"@context\":\"https:\/\/schema.org\",\"@graph\":[{\"@type\":\"Article\",\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5726#article\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5726\"},\"author\":{\"name\":\"Nafisat@ibrahimsheme.com\",\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#\/schema\/person\/75c95be2f573872fa0335010b9a5e74f\"},\"headline\":\"Tuna Baya: Yadda Ha\u0257arin Jirgin \u0198asa Na Langa-langa Ya Faru A 1970\",\"datePublished\":\"2026-03-29T14:01:14+00:00\",\"dateModified\":\"2026-05-11T15:59:16+00:00\",\"mainEntityOfPage\":{\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5726\"},\"wordCount\":1635,\"commentCount\":0,\"publisher\":{\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#organization\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5726#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2026\/05\/20260511_145857.jpg?fit=1024%2C553&ssl=1\",\"keywords\":[\"fa\u0257uwar jirgi\",\"Langa-langa\",\"Nasarawa\",\"NRC\",\"train accident\"],\"articleSection\":[\"Da Hausa\"],\"inLanguage\":\"en-GB\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"CommentAction\",\"name\":\"Comment\",\"target\":[\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5726#respond\"]}]},{\"@type\":\"WebPage\",\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5726\",\"url\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5726\",\"name\":\"Tuna Baya: Yadda Ha\u0257arin Jirgin \u0198asa Na Langa-langa Ya Faru A 1970 - Ibrahim Sheme\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#website\"},\"primaryImageOfPage\":{\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5726#primaryimage\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5726#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2026\/05\/20260511_145857.jpg?fit=1024%2C553&ssl=1\",\"datePublished\":\"2026-03-29T14:01:14+00:00\",\"dateModified\":\"2026-05-11T15:59:16+00:00\",\"breadcrumb\":{\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5726#breadcrumb\"},\"inLanguage\":\"en-GB\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"ReadAction\",\"target\":[\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5726\"]}]},{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-GB\",\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5726#primaryimage\",\"url\":\"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2026\/05\/20260511_145857.jpg?fit=1024%2C553&ssl=1\",\"contentUrl\":\"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2026\/05\/20260511_145857.jpg?fit=1024%2C553&ssl=1\",\"width\":1024,\"height\":553,\"caption\":\"Hoton wurin da jirgin \u0199asa ya fa\u0257i a Kwanar Langa-langa a cikin 1970\"},{\"@type\":\"BreadcrumbList\",\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5726#breadcrumb\",\"itemListElement\":[{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":1,\"name\":\"Home\",\"item\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/\"},{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":2,\"name\":\"Tuna Baya: Yadda Ha\u0257arin Jirgin \u0198asa Na Langa-langa Ya Faru A 1970\"}]},{\"@type\":\"WebSite\",\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#website\",\"url\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/\",\"name\":\"Ibrahim Sheme\",\"description\":\"\",\"publisher\":{\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#organization\"},\"potentialAction\":[{\"@type\":\"SearchAction\",\"target\":{\"@type\":\"EntryPoint\",\"urlTemplate\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?s={search_term_string}\"},\"query-input\":{\"@type\":\"PropertyValueSpecification\",\"valueRequired\":true,\"valueName\":\"search_term_string\"}}],\"inLanguage\":\"en-GB\"},{\"@type\":\"Organization\",\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#organization\",\"name\":\"Ibrahim Sheme\",\"url\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/\",\"logo\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-GB\",\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#\/schema\/logo\/image\/\",\"url\":\"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1\",\"contentUrl\":\"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1\",\"width\":512,\"height\":512,\"caption\":\"Ibrahim Sheme\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#\/schema\/logo\/image\/\"}},{\"@type\":\"Person\",\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#\/schema\/person\/75c95be2f573872fa0335010b9a5e74f\",\"name\":\"Nafisat@ibrahimsheme.com\",\"image\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-GB\",\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#\/schema\/person\/image\/\",\"url\":\"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/f15431c84219439c4441de28a5ea621c90236e7dc8a8934db0967eeaf5f7382a?s=96&d=mm&r=g\",\"contentUrl\":\"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/f15431c84219439c4441de28a5ea621c90236e7dc8a8934db0967eeaf5f7382a?s=96&d=mm&r=g\",\"caption\":\"Nafisat@ibrahimsheme.com\"},\"sameAs\":[\"https:\/\/ibrahimsheme.com\"],\"url\":\"\"}]}<\/script>\n<!-- \/ Yoast SEO plugin. -->","yoast_head_json":{"title":"Tuna Baya: Yadda Ha\u0257arin Jirgin \u0198asa Na Langa-langa Ya Faru A 1970 - Ibrahim Sheme","robots":{"index":"index","follow":"follow","max-snippet":"max-snippet:-1","max-image-preview":"max-image-preview:large","max-video-preview":"max-video-preview:-1"},"canonical":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5726","og_locale":"en_GB","og_type":"article","og_title":"Tuna Baya: Yadda Ha\u0257arin Jirgin \u0198asa Na Langa-langa Ya Faru A 1970 - Ibrahim Sheme","og_description":"Ha\u0257arin jirgin \u0199asa na Langa-langa yana \u0257aya daga cikin ha\u0257urra mafi muni a tarihin safarar jiragen \u0199asa a Afrika. Ha\u0257arin Langa-langa ya faru ne a ranar 16 ga Fabrairu, 1970 kusa da \u0199auyen Langa-langa da ke \u0198aramar Hukumar Akwanga a Jihar Nasarawa ta yanzu, jim ka\u0257an bayan kammala Ya\u0199in Basasar Nijeriya. A wancan lokaci, Hukumar [&hellip;]","og_url":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5726","og_site_name":"Ibrahim Sheme","article_published_time":"2026-03-29T14:01:14+00:00","article_modified_time":"2026-05-11T15:59:16+00:00","og_image":[{"width":1024,"height":553,"url":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2026\/05\/20260511_145857.jpg","type":"image\/jpeg"}],"author":"Nafisat@ibrahimsheme.com","twitter_card":"summary_large_image","twitter_misc":{"Written by":"IBRAHIM SHEME","Estimated reading time":"7 minutes"},"schema":{"@context":"https:\/\/schema.org","@graph":[{"@type":"Article","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5726#article","isPartOf":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5726"},"author":{"name":"Nafisat@ibrahimsheme.com","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#\/schema\/person\/75c95be2f573872fa0335010b9a5e74f"},"headline":"Tuna Baya: Yadda Ha\u0257arin Jirgin \u0198asa Na Langa-langa Ya Faru A 1970","datePublished":"2026-03-29T14:01:14+00:00","dateModified":"2026-05-11T15:59:16+00:00","mainEntityOfPage":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5726"},"wordCount":1635,"commentCount":0,"publisher":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#organization"},"image":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5726#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2026\/05\/20260511_145857.jpg?fit=1024%2C553&ssl=1","keywords":["fa\u0257uwar jirgi","Langa-langa","Nasarawa","NRC","train accident"],"articleSection":["Da Hausa"],"inLanguage":"en-GB","potentialAction":[{"@type":"CommentAction","name":"Comment","target":["https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5726#respond"]}]},{"@type":"WebPage","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5726","url":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5726","name":"Tuna Baya: Yadda Ha\u0257arin Jirgin \u0198asa Na Langa-langa Ya Faru A 1970 - Ibrahim Sheme","isPartOf":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#website"},"primaryImageOfPage":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5726#primaryimage"},"image":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5726#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2026\/05\/20260511_145857.jpg?fit=1024%2C553&ssl=1","datePublished":"2026-03-29T14:01:14+00:00","dateModified":"2026-05-11T15:59:16+00:00","breadcrumb":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5726#breadcrumb"},"inLanguage":"en-GB","potentialAction":[{"@type":"ReadAction","target":["https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5726"]}]},{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-GB","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5726#primaryimage","url":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2026\/05\/20260511_145857.jpg?fit=1024%2C553&ssl=1","contentUrl":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2026\/05\/20260511_145857.jpg?fit=1024%2C553&ssl=1","width":1024,"height":553,"caption":"Hoton wurin da jirgin \u0199asa ya fa\u0257i a Kwanar Langa-langa a cikin 1970"},{"@type":"BreadcrumbList","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5726#breadcrumb","itemListElement":[{"@type":"ListItem","position":1,"name":"Home","item":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/"},{"@type":"ListItem","position":2,"name":"Tuna Baya: Yadda Ha\u0257arin Jirgin \u0198asa Na Langa-langa Ya Faru A 1970"}]},{"@type":"WebSite","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#website","url":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/","name":"Ibrahim Sheme","description":"","publisher":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#organization"},"potentialAction":[{"@type":"SearchAction","target":{"@type":"EntryPoint","urlTemplate":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?s={search_term_string}"},"query-input":{"@type":"PropertyValueSpecification","valueRequired":true,"valueName":"search_term_string"}}],"inLanguage":"en-GB"},{"@type":"Organization","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#organization","name":"Ibrahim Sheme","url":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/","logo":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-GB","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#\/schema\/logo\/image\/","url":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1","contentUrl":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1","width":512,"height":512,"caption":"Ibrahim Sheme"},"image":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#\/schema\/logo\/image\/"}},{"@type":"Person","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#\/schema\/person\/75c95be2f573872fa0335010b9a5e74f","name":"Nafisat@ibrahimsheme.com","image":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-GB","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#\/schema\/person\/image\/","url":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/f15431c84219439c4441de28a5ea621c90236e7dc8a8934db0967eeaf5f7382a?s=96&d=mm&r=g","contentUrl":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/f15431c84219439c4441de28a5ea621c90236e7dc8a8934db0967eeaf5f7382a?s=96&d=mm&r=g","caption":"Nafisat@ibrahimsheme.com"},"sameAs":["https:\/\/ibrahimsheme.com"],"url":""}]}},"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2026\/05\/20260511_145857.jpg?fit=1024%2C553&ssl=1","jetpack_likes_enabled":true,"jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/5726","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/5"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=5726"}],"version-history":[{"count":6,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/5726\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":5734,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/5726\/revisions\/5734"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/5728"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=5726"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=5726"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=5726"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}