{"id":5285,"date":"2013-01-19T13:38:03","date_gmt":"2013-01-19T13:38:03","guid":{"rendered":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5285"},"modified":"2024-01-20T07:44:35","modified_gmt":"2024-01-20T07:44:35","slug":"alamomi-40-na-dairar-adabin-kasuwar-kano","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5285","title":{"rendered":"Alamomi 40 na da&#8217;irar Adabin Kasuwar Kano"},"content":{"rendered":"<p>IBRAHIM Malumfashi ne ya \u0199ir\u0199iro\u00a0 kalmar &#8220;Adabin Kasuwar Kano&#8221;, wanda da yawan marubuta da manazarta (ciki har da ni) su ka \u0257auka \u0199as\u0199antarwa ce. Mun shafe shekaru mu na ya\u0199i da Malumfashi kan wannan kalmar, kafin kowannen mu ya aje makamin sa (wato biro) a gefe \u0257aya, domin duk abin da za a ce, an ce, kuma duk abin da za a yi, an yi.<\/p>\n<p>Na jima ina tunanin menene alamomin littafin irin wannan adabin? To, bayan na gama tunani na, sai na lissafa su. Wani abu da na gano shi ne, yawancin alamomin Adabin Kasuwar Kano akwai su a finafinan Hausa, to amma &#8216;yan fim sun fi marubuta \u0257aukar aikin su a matsayin sana&#8217;a, kuma sun fi cin moriyar gumin su.<\/p>\n<p>Ga yawancin alamomin (amma akwai wasu daban):<\/p>\n<p>1. Littafin na Hausa ne ko Turanci. Kuskure ne a \u0257auka cewa sai littafin Hausa ne kan fa\u0257a a farfajiyar wannan kalma. To amma na Hausan sun fi yawa.<\/p>\n<p>2. Marubuci kan \u0257auki nauyin buga littafin shi, ba kamfani ba.<\/p>\n<p>3. Babu lambar ISBN a yawancin littattafan.<\/p>\n<p>4. Babu kyakkyawan nahawu. Saboda haka za a ga \u0257imbin kurakurai a littafin, daga raba kalma ko ha\u0257e kalma har zuwa bin \u0199a&#8217;idojin rubutu kamar su saka aya, wa\u0199afi, alamar motsin rai, ayar tambaya, alamomin fara magana da rufe ta, ds. Kai, hatta sunayen mutane da na garuruwa akwai wa\u0257anda ba daidai ba a littafin.<\/p>\n<p>5. Marubuci bai bayar da littafi wani ya gyara masa kafin a buga. Gyara ya ha\u0257a da nahawu da kuma sukar labarin. Wani marubucin ya na tsoron kada ya ba \u0257an&#8217;uwan sa marubuci a sace masa labari! Da ya gama sai ya kai wurin \u0257ab&#8217;i.<\/p>\n<p>6. Rarraba littafi zuwa na 2, 3, 4 ko ma fiye. Ana yin haka domin riba, kuma domin masu karatu kan dinga tambayar ina na 2 ko ina na 3. Abin mamaki, masu karatu ba su cewa ina na biyun &#8216;Gan\u0257oki,&#8217; &#8216;Karshen Alewa \u0198asa&#8217;, &#8216;Mace Mutum&#8217; ko &#8221;Yartsana.&#8217; Dalili shi ne sun san labarin ya \u0199are, ko kuma su na ganin wa\u0257annan marubutan ba masu karkasa labari ba ne.<\/p>\n<p>7. Saka lambar wayar marubuci ko adireshin i-mel, wasu ma har da BB Pin, a cikin littafi, saboda masu karatu su bugo waya su fa\u0257i ra&#8217;ayin su kan littafin, kuma su kambama marubuci. Ta wannan hanyar, wasu matan aure marubuta sun sha samun \u0199alubale daga mazajen su.<\/p>\n<p>8. \u0198ulla hul\u0257a tsakanin marubuci da mai karatu har ta kai ga ana ziyartar juna, ko ka ga yarinya ta sauka a gidan marubuciya wai ta na neman shawara kan wani abu (misali aure). Wani matashin marubucin ma kan samu \u0199ulla soyayya da &#8216;yan mata ta wannan hanyar.<\/p>\n<p>9. Duk tunanin marubuci game da kasuwancin littafi bai wuce garin Kano. A nan manyan dillalan littafi su ke. Marubuci bai tunanin ya kai littafin sa Kaduna ko Abuja ko Sakkwato; ya dogara kan dillali ya yi masa wannan, ko kuma dillalan da ke can su zo Kano su saya su tafi.<\/p>\n<p>10. Yawaitar \u0199ungiyoyin marubuta, kuma da yawa ba su jituwa da juna.<\/p>\n<p>11. Rashin ingancin littafi wajen tsara shafukan sa, da takarda, da \u0257ab&#8217;i (a Turance, &#8220;final finishing&#8221;).<\/p>\n<p>12. Doguwar sadaukarwa a littafi, tare da godiya ga &#8216;yan&#8217;uwa da masoya da makaranta da &#8216;ya&#8217;ya.<\/p>\n<p>13. Rige-rigen fito da littafi a tsakanin marubuta, wanda gasa ko gaba ke haifarwa. A mako \u0257aya sai littafi biyar su fito.<\/p>\n<p>14. Maimaita labarin wani littafin ta hanyar sauya masa siga.<\/p>\n<p>15. Rashin shirya babbar gasa ta rubutu, ko bajekolin littattafai.<\/p>\n<p>16. Kwaikwayon yadda wani ya yi nasa labarin ta fuskar tsarin da ya bi, maimakon kai ma ka fito da naka.<\/p>\n<p>17. Samun marubuta &#8216;yan kasuwa, wa\u0257anda ke da &#8220;kamfanonin&#8221; buga wa sauran marubuta littafi, wata sa&#8217;a har da tallata musu littafin. Wata sa&#8217;a kashe- mu-raba su ke yi wajen buga littafin.<\/p>\n<p>18. Juya labarin fim \u0257in Indiya ko na Turawa ko na Canis ko na Larabawa zuwa littafi.<\/p>\n<p>19. Rige-rigen rubuta labari a Facebook (musamman a Duniyar Marubuta ko Dandalin Marubuta). Tsarin wannan shi ne sai a fara labari ko da she\u0257ara \u0257aya ce, sai kuma a bari sai &#8216;yan guruf sun fa\u0257i ra&#8217;ayin su sannan a ci gaba. Sau da yawa ma babu labarin a aje, a lokacin ne ake rubuta shi.<\/p>\n<p>20. Rashin \u0199o\u0199arin a fassara littafi zuwa wasu harsunan na duniya wanda ba su jin Hausa, kamar yadda aka yi wa &#8216;Alhaki Kwikuyo&#8217; na Balaraba Ramat Yakubu kwanan baya.<\/p>\n<p>21. Rashin damuwar gwamnati ga harkar rubutun littafi. Gwamnati ta fi damuwa da &#8216;yan fim, shi ya sa ta kafa masu hukuma, kuma ta na shirya masu bitoci da bukukuwan baje-kolin finafinai. Bugu da \u0199ari, ofisoshin jakadun \u0199asashen waje da \u0199ungiyoyi masu zaman kan su (NGOs) kan kira &#8216;yan fim su ba su tallafi, ciki har da kai su \u0199asashen su domin su \u0199ara wayewa kan harkar. A lura, marubutan Ingilishi ma kan samu wannan tagomashin.<\/p>\n<p>22. Rashin zurfin hikima wajen ba da labari, wajen wasa da harshe ko sar\u0199a\u0199iyar labari.<\/p>\n<p>23. Shaida wa mai karatu a cikin littafi cewa ana nan ana aiki kan wani littafin wanda zai fito nan gaba, ko kuma ba da ha\u0199uri kan wani littafi ko rashin amsa waya, ds.<\/p>\n<p>24. Yawanci jigon littafi bai wuce soyayyar matasa ko matsalar aure ko kasuwanci.<\/p>\n<p>25. Saka Ingilishi a cikin labari ba don ya zama tilas ba sai don a burge mai karatu.<\/p>\n<p>26. Yawanci mata ne ke yin rubutun. Kai, har ta kai maza kan yi rubutu da sunan mace don kiran kasuwa.<\/p>\n<p>27. Saka hoton kyakkyawar fuskar mace a bangon littafi. Yanzu har matan Indiya da Larabawa da Turawa ake \u0257aukowa daga intanet a saka; wasu har hijabi ake yi masu da Photoshop. Wannan kan nuna kamar Bahaushe bai da mummunar mace ko tsaka-tsaki. Wani lokaci kuma hoton katafaren gida ake sakawa.<\/p>\n<p>28. Ba a cika ba da labarin talakawa ba, sai &#8216;yan boko da manyan &#8216;yan kasuwa. Ko da labarin talaka aka faro, to sai ya riki\u0257e ya zama na masu ku\u0257i, masu fita zuwa \u0199asar waje.<\/p>\n<p>29. Idan za a nuna an fita waje a labari, to tafiyar ba ta wuce Ingila, Amerika, Saudiyya, Dubai ko Indiya.<\/p>\n<p>30. Sayar da littafi \u0257ungurungum ga \u0257an kasuwa, shi ya buga ya samu ku\u0257i. Yawanci babu rubutacciyar yarjejeniya ta wannan cinikin.<\/p>\n<p>31. Amsar kwangilar rubuta littafi daga wurin \u0257an kasuwa. &#8220;Nawa zan ba ki, ki rubuta mani littafi mai shafi saba&#8217;in?&#8221; Idan ta rubuta ta ba shi, sai ya saka sunan da ya ga dama.<\/p>\n<p>32. Gamewar marubuta biyu ko uku su yi littafi guda \u0257aya.<\/p>\n<p>33. Rashin da\u0257ewar littafi a kasuwa. Idan littafi ya ci kasuwa wata shida, shi kenan ba ka \u0199ara jin \u0257uriyar sa. A lura, har yanzu ana buga &#8216;Gan\u0257oki,&#8217; wanda ya fara fitowa a 1934.<\/p>\n<p>34. Da wuya ka ga an yi sharhi kan littafin a wata jarida ko mujalla, duk da yake akwai jaridun Hausa da yawa.<\/p>\n<p>35. Kafafen ya\u0257a labarai sun fi damuwa da rayuwar &#8216;yan fim. Misali, idan Fauziyya D. Sulaiman ta haihu, ba labari ba ne, to amma idan Ru\u0199ayya Dawayya ta haihu, labari ne. Amma a marubutan Turanci na Nijeriya, idan Chimamanda Ngozi Adichie ta yi aure ko ta haihu, babban labari ne!<\/p>\n<p>36. Da wuya ka ga an yi nazarin littafin a matakin digiri ko difiloma, ko a yi \u0199asida a kan sa a cikin wata mujalla ta masu bincike, ko a gabatar da lacca a kan sa a wani taro a jami&#8217;a ko babbar makaranta.<\/p>\n<p>37. Da wuya ka ga an yi littafin nazari kan marubucin wannan adabin.<\/p>\n<p>38. Saurin shu\u0257ewar zamanin marubuci, har ka ji an daina maganar sa, sai ta wanda ake yayi a yanzu. Misali, \u018aan&#8217;azimi Baba, Bilkisu Salisu Ahmed Funtua, Ado Gidan Dabino.<\/p>\n<p>39. Kallon rainin da ake wa littattafan wannan adabi ya sa a yau ko da wani ya yi littafi mai inganci sai a jefa shi cikin kwandon sharar irin wa\u0257annan littattafan.<\/p>\n<p>40. Ana kallon marubuci kusan \u0257aya da \u0257an fim ta fuskar darajar su. Wasu ma sun fi ganin girman darajar mai yin fim.<\/p>\n<p>Wa\u0257annan alamomin sun taimaka wajen bun\u0199asar &#8221;adabin kasuwar Kano,&#8221; to amma kuma su na taimakawa gaya wajen dakusar da cigaban adabin Hausa na sashen rubutun littafi.<\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div>\n<p id=\"pvc_stats_5285\" class=\"pvc_stats total_only  \" data-element-id=\"5285\" style=\"\"><i class=\"pvc-stats-icon medium\" aria-hidden=\"true\"><svg xmlns=\"http:\/\/www.w3.org\/2000\/svg\" version=\"1.0\" viewBox=\"0 0 502 315\" preserveAspectRatio=\"xMidYMid meet\"><g transform=\"translate(0,332) scale(0.1,-0.1)\" fill=\"\" stroke=\"none\"><path d=\"M2394 3279 l-29 -30 -3 -207 c-2 -182 0 -211 15 -242 39 -76 157 -76 196 0 15 31 17 60 15 243 l-3 209 -33 29 c-26 23 -41 29 -80 29 -41 0 -53 -5 -78 -31z\"\/><path d=\"M3085 3251 c-45 -19 -58 -50 -96 -229 -47 -217 -49 -260 -13 -295 52 -53 146 -42 177 20 16 31 87 366 87 410 0 70 -86 122 -155 94z\"\/><path d=\"M1751 3234 c-13 -9 -29 -31 -37 -50 -12 -29 -10 -49 21 -204 19 -94 39 -189 45 -210 14 -50 54 -80 110 -80 34 0 48 6 76 34 21 21 34 44 34 59 0 14 -18 113 -40 219 -37 178 -43 195 -70 221 -36 32 -101 37 -139 11z\"\/><path d=\"M1163 3073 c-36 -7 -73 -59 -73 -102 0 -56 133 -378 171 -413 34 -32 83 -37 129 -13 70 36 67 87 -16 290 -86 209 -89 214 -129 231 -35 14 -42 15 -82 7z\"\/><path d=\"M3689 3066 c-15 -9 -33 -30 -42 -48 -48 -103 -147 -355 -147 -375 0 -98 131 -148 192 -74 13 15 57 108 97 206 80 196 84 226 37 273 -30 30 -99 39 -137 18z\"\/><path d=\"M583 2784 c-38 -19 -67 -74 -58 -113 9 -42 211 -354 242 -373 16 -10 45 -18 66 -18 51 0 107 52 107 100 0 39 -1 41 -124 234 -80 126 -108 162 -133 173 -41 17 -61 16 -100 -3z\"\/><path d=\"M4250 2784 c-14 -9 -74 -91 -133 -183 -95 -150 -107 -173 -107 -213 0 -55 33 -94 87 -104 67 -13 90 8 211 198 130 202 137 225 78 284 -27 27 -42 34 -72 34 -22 0 -50 -8 -64 -16z\"\/><path d=\"M2275 2693 c-553 -48 -1095 -270 -1585 -649 -135 -104 -459 -423 -483 -476 -23 -49 -22 -139 2 -186 73 -142 361 -457 571 -626 285 -228 642 -407 990 -497 242 -63 336 -73 660 -74 310 0 370 5 595 52 535 111 1045 392 1455 803 122 121 250 273 275 326 19 41 19 137 0 174 -41 79 -309 363 -465 492 -447 370 -946 591 -1479 653 -113 14 -422 18 -536 8z m395 -428 c171 -34 330 -124 456 -258 112 -119 167 -219 211 -378 27 -96 24 -300 -5 -401 -72 -255 -236 -447 -474 -557 -132 -62 -201 -76 -368 -76 -167 0 -236 14 -368 76 -213 98 -373 271 -451 485 -162 444 86 934 547 1084 153 49 292 57 452 25z m909 -232 c222 -123 408 -262 593 -441 76 -74 138 -139 138 -144 0 -16 -233 -242 -330 -319 -155 -123 -309 -223 -461 -299 l-81 -41 32 46 c18 26 49 83 70 128 143 306 141 649 -6 957 -25 52 -61 116 -79 142 l-34 47 45 -20 c26 -10 76 -36 113 -56z m-2057 25 c-40 -58 -105 -190 -130 -263 -110 -324 -59 -707 132 -981 25 -35 42 -64 37 -64 -19 0 -241 119 -326 174 -188 122 -406 314 -532 468 l-58 71 108 103 c185 178 428 349 672 473 66 33 121 60 123 61 2 0 -10 -19 -26 -42z\"\/><path d=\"M2375 1950 c-198 -44 -350 -190 -395 -379 -18 -76 -8 -221 19 -290 114 -284 457 -406 731 -260 98 52 188 154 231 260 27 69 37 214 19 290 -38 163 -166 304 -326 360 -67 23 -215 33 -279 19z\"\/><\/g><\/svg><\/i> <img data-recalc-dims=\"1\" loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"16\" height=\"16\" alt=\"Loading\" src=\"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/plugins\/page-views-count\/ajax-loader-2x.gif?resize=16%2C16&#038;ssl=1\" border=0 \/><\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>IBRAHIM Malumfashi ne ya \u0199ir\u0199iro\u00a0 kalmar &#8220;Adabin Kasuwar Kano&#8221;, wanda da yawan marubuta da manazarta (ciki har da ni) su ka \u0257auka \u0199as\u0199antarwa ce. Mun shafe shekaru mu na ya\u0199i da Malumfashi kan wannan kalmar, kafin kowannen mu ya aje makamin sa (wato biro) a gefe \u0257aya, domin duk abin da za a ce, an [&hellip;]<\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div>\n<p id=\"pvc_stats_5285\" class=\"pvc_stats total_only  \" data-element-id=\"5285\" style=\"\"><i class=\"pvc-stats-icon medium\" aria-hidden=\"true\"><svg xmlns=\"http:\/\/www.w3.org\/2000\/svg\" version=\"1.0\" viewBox=\"0 0 502 315\" preserveAspectRatio=\"xMidYMid meet\"><g transform=\"translate(0,332) scale(0.1,-0.1)\" fill=\"\" stroke=\"none\"><path d=\"M2394 3279 l-29 -30 -3 -207 c-2 -182 0 -211 15 -242 39 -76 157 -76 196 0 15 31 17 60 15 243 l-3 209 -33 29 c-26 23 -41 29 -80 29 -41 0 -53 -5 -78 -31z\"\/><path d=\"M3085 3251 c-45 -19 -58 -50 -96 -229 -47 -217 -49 -260 -13 -295 52 -53 146 -42 177 20 16 31 87 366 87 410 0 70 -86 122 -155 94z\"\/><path d=\"M1751 3234 c-13 -9 -29 -31 -37 -50 -12 -29 -10 -49 21 -204 19 -94 39 -189 45 -210 14 -50 54 -80 110 -80 34 0 48 6 76 34 21 21 34 44 34 59 0 14 -18 113 -40 219 -37 178 -43 195 -70 221 -36 32 -101 37 -139 11z\"\/><path d=\"M1163 3073 c-36 -7 -73 -59 -73 -102 0 -56 133 -378 171 -413 34 -32 83 -37 129 -13 70 36 67 87 -16 290 -86 209 -89 214 -129 231 -35 14 -42 15 -82 7z\"\/><path d=\"M3689 3066 c-15 -9 -33 -30 -42 -48 -48 -103 -147 -355 -147 -375 0 -98 131 -148 192 -74 13 15 57 108 97 206 80 196 84 226 37 273 -30 30 -99 39 -137 18z\"\/><path d=\"M583 2784 c-38 -19 -67 -74 -58 -113 9 -42 211 -354 242 -373 16 -10 45 -18 66 -18 51 0 107 52 107 100 0 39 -1 41 -124 234 -80 126 -108 162 -133 173 -41 17 -61 16 -100 -3z\"\/><path d=\"M4250 2784 c-14 -9 -74 -91 -133 -183 -95 -150 -107 -173 -107 -213 0 -55 33 -94 87 -104 67 -13 90 8 211 198 130 202 137 225 78 284 -27 27 -42 34 -72 34 -22 0 -50 -8 -64 -16z\"\/><path d=\"M2275 2693 c-553 -48 -1095 -270 -1585 -649 -135 -104 -459 -423 -483 -476 -23 -49 -22 -139 2 -186 73 -142 361 -457 571 -626 285 -228 642 -407 990 -497 242 -63 336 -73 660 -74 310 0 370 5 595 52 535 111 1045 392 1455 803 122 121 250 273 275 326 19 41 19 137 0 174 -41 79 -309 363 -465 492 -447 370 -946 591 -1479 653 -113 14 -422 18 -536 8z m395 -428 c171 -34 330 -124 456 -258 112 -119 167 -219 211 -378 27 -96 24 -300 -5 -401 -72 -255 -236 -447 -474 -557 -132 -62 -201 -76 -368 -76 -167 0 -236 14 -368 76 -213 98 -373 271 -451 485 -162 444 86 934 547 1084 153 49 292 57 452 25z m909 -232 c222 -123 408 -262 593 -441 76 -74 138 -139 138 -144 0 -16 -233 -242 -330 -319 -155 -123 -309 -223 -461 -299 l-81 -41 32 46 c18 26 49 83 70 128 143 306 141 649 -6 957 -25 52 -61 116 -79 142 l-34 47 45 -20 c26 -10 76 -36 113 -56z m-2057 25 c-40 -58 -105 -190 -130 -263 -110 -324 -59 -707 132 -981 25 -35 42 -64 37 -64 -19 0 -241 119 -326 174 -188 122 -406 314 -532 468 l-58 71 108 103 c185 178 428 349 672 473 66 33 121 60 123 61 2 0 -10 -19 -26 -42z\"\/><path d=\"M2375 1950 c-198 -44 -350 -190 -395 -379 -18 -76 -8 -221 19 -290 114 -284 457 -406 731 -260 98 52 188 154 231 260 27 69 37 214 19 290 -38 163 -166 304 -326 360 -67 23 -215 33 -279 19z\"\/><\/g><\/svg><\/i> <img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"16\" height=\"16\" alt=\"Loading\" src=\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/plugins\/page-views-count\/ajax-loader-2x.gif\" border=0 \/><\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div>\n","protected":false},"author":5,"featured_media":5288,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_FSMCFIC_featured_image_caption":"","_FSMCFIC_featured_image_nocaption":"","_FSMCFIC_featured_image_hide":"","_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[7],"tags":[],"class_list":["post-5285","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-hausa"],"yoast_head":"<!-- This site is optimized with the Yoast SEO plugin v26.9 - https:\/\/yoast.com\/product\/yoast-seo-wordpress\/ -->\n<title>Alamomi 40 na da&#039;irar Adabin Kasuwar Kano - Ibrahim Sheme<\/title>\n<meta name=\"robots\" content=\"index, follow, max-snippet:-1, max-image-preview:large, max-video-preview:-1\" \/>\n<link rel=\"canonical\" href=\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5285\" \/>\n<meta property=\"og:locale\" content=\"en_GB\" \/>\n<meta property=\"og:type\" content=\"article\" \/>\n<meta property=\"og:title\" content=\"Alamomi 40 na da&#039;irar Adabin Kasuwar Kano - Ibrahim Sheme\" \/>\n<meta property=\"og:description\" content=\"IBRAHIM Malumfashi ne ya \u0199ir\u0199iro\u00a0 kalmar &#8220;Adabin Kasuwar Kano&#8221;, wanda da yawan marubuta da manazarta (ciki har da ni) su ka \u0257auka \u0199as\u0199antarwa ce. Mun shafe shekaru mu na ya\u0199i da Malumfashi kan wannan kalmar, kafin kowannen mu ya aje makamin sa (wato biro) a gefe \u0257aya, domin duk abin da za a ce, an [&hellip;]\" \/>\n<meta property=\"og:url\" content=\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5285\" \/>\n<meta property=\"og:site_name\" content=\"Ibrahim Sheme\" \/>\n<meta property=\"article:published_time\" content=\"2013-01-19T13:38:03+00:00\" \/>\n<meta property=\"article:modified_time\" content=\"2024-01-20T07:44:35+00:00\" \/>\n<meta property=\"og:image\" content=\"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2024\/01\/FB_IMG_1705734358592.jpg?fit=819%2C460&ssl=1\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:width\" content=\"819\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:height\" content=\"460\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:type\" content=\"image\/jpeg\" \/>\n<meta name=\"author\" content=\"Nafisat@ibrahimsheme.com\" \/>\n<meta name=\"twitter:card\" content=\"summary_large_image\" \/>\n<meta name=\"twitter:label1\" content=\"Written by\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data1\" content=\"IBRAHIM SHEME\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:label2\" content=\"Estimated reading time\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data2\" content=\"7 minutes\" \/>\n<script type=\"application\/ld+json\" class=\"yoast-schema-graph\">{\"@context\":\"https:\/\/schema.org\",\"@graph\":[{\"@type\":\"Article\",\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5285#article\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5285\"},\"author\":{\"name\":\"Nafisat@ibrahimsheme.com\",\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#\/schema\/person\/75c95be2f573872fa0335010b9a5e74f\"},\"headline\":\"Alamomi 40 na da&#8217;irar Adabin Kasuwar Kano\",\"datePublished\":\"2013-01-19T13:38:03+00:00\",\"dateModified\":\"2024-01-20T07:44:35+00:00\",\"mainEntityOfPage\":{\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5285\"},\"wordCount\":1359,\"commentCount\":0,\"publisher\":{\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#organization\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5285#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2024\/01\/FB_IMG_1705734358592.jpg?fit=819%2C460&ssl=1\",\"articleSection\":[\"Da Hausa\"],\"inLanguage\":\"en-GB\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"CommentAction\",\"name\":\"Comment\",\"target\":[\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5285#respond\"]}]},{\"@type\":\"WebPage\",\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5285\",\"url\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5285\",\"name\":\"Alamomi 40 na da'irar Adabin Kasuwar Kano - Ibrahim Sheme\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#website\"},\"primaryImageOfPage\":{\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5285#primaryimage\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5285#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2024\/01\/FB_IMG_1705734358592.jpg?fit=819%2C460&ssl=1\",\"datePublished\":\"2013-01-19T13:38:03+00:00\",\"dateModified\":\"2024-01-20T07:44:35+00:00\",\"breadcrumb\":{\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5285#breadcrumb\"},\"inLanguage\":\"en-GB\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"ReadAction\",\"target\":[\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5285\"]}]},{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-GB\",\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5285#primaryimage\",\"url\":\"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2024\/01\/FB_IMG_1705734358592.jpg?fit=819%2C460&ssl=1\",\"contentUrl\":\"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2024\/01\/FB_IMG_1705734358592.jpg?fit=819%2C460&ssl=1\",\"width\":819,\"height\":460,\"caption\":\"Wasu littattafan Hausa (Hoto daga: Carmen McCain)\"},{\"@type\":\"BreadcrumbList\",\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5285#breadcrumb\",\"itemListElement\":[{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":1,\"name\":\"Home\",\"item\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/\"},{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":2,\"name\":\"Alamomi 40 na da&#8217;irar Adabin Kasuwar Kano\"}]},{\"@type\":\"WebSite\",\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#website\",\"url\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/\",\"name\":\"Ibrahim Sheme\",\"description\":\"\",\"publisher\":{\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#organization\"},\"potentialAction\":[{\"@type\":\"SearchAction\",\"target\":{\"@type\":\"EntryPoint\",\"urlTemplate\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?s={search_term_string}\"},\"query-input\":{\"@type\":\"PropertyValueSpecification\",\"valueRequired\":true,\"valueName\":\"search_term_string\"}}],\"inLanguage\":\"en-GB\"},{\"@type\":\"Organization\",\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#organization\",\"name\":\"Ibrahim Sheme\",\"url\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/\",\"logo\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-GB\",\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#\/schema\/logo\/image\/\",\"url\":\"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1\",\"contentUrl\":\"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1\",\"width\":512,\"height\":512,\"caption\":\"Ibrahim Sheme\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#\/schema\/logo\/image\/\"}},{\"@type\":\"Person\",\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#\/schema\/person\/75c95be2f573872fa0335010b9a5e74f\",\"name\":\"Nafisat@ibrahimsheme.com\",\"image\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-GB\",\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#\/schema\/person\/image\/\",\"url\":\"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/f15431c84219439c4441de28a5ea621c90236e7dc8a8934db0967eeaf5f7382a?s=96&d=mm&r=g\",\"contentUrl\":\"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/f15431c84219439c4441de28a5ea621c90236e7dc8a8934db0967eeaf5f7382a?s=96&d=mm&r=g\",\"caption\":\"Nafisat@ibrahimsheme.com\"},\"sameAs\":[\"https:\/\/ibrahimsheme.com\"],\"url\":\"\"}]}<\/script>\n<!-- \/ Yoast SEO plugin. -->","yoast_head_json":{"title":"Alamomi 40 na da'irar Adabin Kasuwar Kano - Ibrahim Sheme","robots":{"index":"index","follow":"follow","max-snippet":"max-snippet:-1","max-image-preview":"max-image-preview:large","max-video-preview":"max-video-preview:-1"},"canonical":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5285","og_locale":"en_GB","og_type":"article","og_title":"Alamomi 40 na da'irar Adabin Kasuwar Kano - Ibrahim Sheme","og_description":"IBRAHIM Malumfashi ne ya \u0199ir\u0199iro\u00a0 kalmar &#8220;Adabin Kasuwar Kano&#8221;, wanda da yawan marubuta da manazarta (ciki har da ni) su ka \u0257auka \u0199as\u0199antarwa ce. Mun shafe shekaru mu na ya\u0199i da Malumfashi kan wannan kalmar, kafin kowannen mu ya aje makamin sa (wato biro) a gefe \u0257aya, domin duk abin da za a ce, an [&hellip;]","og_url":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5285","og_site_name":"Ibrahim Sheme","article_published_time":"2013-01-19T13:38:03+00:00","article_modified_time":"2024-01-20T07:44:35+00:00","og_image":[{"width":819,"height":460,"url":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2024\/01\/FB_IMG_1705734358592.jpg?fit=819%2C460&ssl=1","type":"image\/jpeg"}],"author":"Nafisat@ibrahimsheme.com","twitter_card":"summary_large_image","twitter_misc":{"Written by":"IBRAHIM SHEME","Estimated reading time":"7 minutes"},"schema":{"@context":"https:\/\/schema.org","@graph":[{"@type":"Article","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5285#article","isPartOf":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5285"},"author":{"name":"Nafisat@ibrahimsheme.com","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#\/schema\/person\/75c95be2f573872fa0335010b9a5e74f"},"headline":"Alamomi 40 na da&#8217;irar Adabin Kasuwar Kano","datePublished":"2013-01-19T13:38:03+00:00","dateModified":"2024-01-20T07:44:35+00:00","mainEntityOfPage":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5285"},"wordCount":1359,"commentCount":0,"publisher":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#organization"},"image":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5285#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2024\/01\/FB_IMG_1705734358592.jpg?fit=819%2C460&ssl=1","articleSection":["Da Hausa"],"inLanguage":"en-GB","potentialAction":[{"@type":"CommentAction","name":"Comment","target":["https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5285#respond"]}]},{"@type":"WebPage","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5285","url":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5285","name":"Alamomi 40 na da'irar Adabin Kasuwar Kano - Ibrahim Sheme","isPartOf":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#website"},"primaryImageOfPage":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5285#primaryimage"},"image":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5285#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2024\/01\/FB_IMG_1705734358592.jpg?fit=819%2C460&ssl=1","datePublished":"2013-01-19T13:38:03+00:00","dateModified":"2024-01-20T07:44:35+00:00","breadcrumb":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5285#breadcrumb"},"inLanguage":"en-GB","potentialAction":[{"@type":"ReadAction","target":["https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5285"]}]},{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-GB","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5285#primaryimage","url":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2024\/01\/FB_IMG_1705734358592.jpg?fit=819%2C460&ssl=1","contentUrl":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2024\/01\/FB_IMG_1705734358592.jpg?fit=819%2C460&ssl=1","width":819,"height":460,"caption":"Wasu littattafan Hausa (Hoto daga: Carmen McCain)"},{"@type":"BreadcrumbList","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5285#breadcrumb","itemListElement":[{"@type":"ListItem","position":1,"name":"Home","item":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/"},{"@type":"ListItem","position":2,"name":"Alamomi 40 na da&#8217;irar Adabin Kasuwar Kano"}]},{"@type":"WebSite","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#website","url":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/","name":"Ibrahim Sheme","description":"","publisher":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#organization"},"potentialAction":[{"@type":"SearchAction","target":{"@type":"EntryPoint","urlTemplate":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?s={search_term_string}"},"query-input":{"@type":"PropertyValueSpecification","valueRequired":true,"valueName":"search_term_string"}}],"inLanguage":"en-GB"},{"@type":"Organization","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#organization","name":"Ibrahim Sheme","url":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/","logo":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-GB","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#\/schema\/logo\/image\/","url":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1","contentUrl":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1","width":512,"height":512,"caption":"Ibrahim Sheme"},"image":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#\/schema\/logo\/image\/"}},{"@type":"Person","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#\/schema\/person\/75c95be2f573872fa0335010b9a5e74f","name":"Nafisat@ibrahimsheme.com","image":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-GB","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#\/schema\/person\/image\/","url":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/f15431c84219439c4441de28a5ea621c90236e7dc8a8934db0967eeaf5f7382a?s=96&d=mm&r=g","contentUrl":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/f15431c84219439c4441de28a5ea621c90236e7dc8a8934db0967eeaf5f7382a?s=96&d=mm&r=g","caption":"Nafisat@ibrahimsheme.com"},"sameAs":["https:\/\/ibrahimsheme.com"],"url":""}]}},"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2024\/01\/FB_IMG_1705734358592.jpg?fit=819%2C460&ssl=1","jetpack_likes_enabled":true,"jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/5285","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/5"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=5285"}],"version-history":[{"count":2,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/5285\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":5290,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/5285\/revisions\/5290"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/5288"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=5285"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=5285"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=5285"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}