{"id":5099,"date":"2022-02-03T13:39:29","date_gmt":"2022-02-03T13:39:29","guid":{"rendered":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5099"},"modified":"2024-04-23T07:56:19","modified_gmt":"2024-04-23T07:56:19","slug":"laifi-ne-idan-an-sayar-da-gidan-shata","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5099","title":{"rendered":"Laifi ne idan an sayar da gidan Shata?"},"content":{"rendered":"<p>A yau, na wayi gari na ga ana nuna damuwa a soshiyal midiya a kan ji-ta-ji-tar wai \u2018ya\u2019yan Alhaji Mamman Shata sun sayar da gidan mahaifin su da ke Funtuwa, ana cewa bai kamata ba. Na farko, ina bada tabbacin cewa ba a sayar da wannan gidan ba. To amma wani hanzari ba gudu ba, shin idan ma an sayar \u0257in, wani laifi ne aka \u0257ibga? Ko ka\u0257an!<\/p>\n<p>Gidan dai mallakar wasu daga cikin \u2018ya\u2019yan Baba Shata ne a yanzu haka. To amma a cikin 2021 mutum biyu (maza) da su ka mallaki sashen gaba na gidan, wanda ya ha\u0257a da garejin motar Dakta Shata da falo inda ya ke zama tare da kar\u0253ar ba\u0199i sun sayar da nasu sashen. Wannan \u0253angare nasu ne, ha\u0199\u0199in su ne. An ma ji wani daga cikin su ya na fa\u0257in, \u201cShin ko a Makka akwai gidan su Manzon Allah (s.a.w.) ne a yau?\u201d Ya fa\u0257i haka ne lokacin da aka nuna masa muhimmancin barin wannan gida na mahaifin sa a matsayin kayan tarihi.<\/p>\n<p>Dalilin wa\u0257annan \u2018ya\u2019ya biyu na Shata na sayar da gadon su shi ne su na da bu\u0199atar su yi gidan kan su, su huta da zama a gidan haya. Kuma ba su da wata hanya sai wannan. A lokacin, sun bu\u0199aci wani yayan su da ke kula da su (Alhaji Mustapha S. Shata) ya sanya hannu a takardar cinikin a matsayin shaida, shi kuma ya \u0199i saboda bai lamunta da sayar da wannan gida mai \u0257imbin tarihi ba. Shi ma Sarkin Maska (Hakimin Funtuwa) bai sa hannu a takardar ba saboda ya samu labarin cewa Alh. Mustapha bai sa hannu ba. Amma wannan bai hana cinikin ba. Kuma hakan ba ya nufin an sayar da gidan baki \u0257ayan shi.<\/p>\n<p>Akwai wani ha\u0257ari da na hango. Nan gaba ake ji. Yanzu haka akwai \u2018ya\u2019yan Shata da su ma za su so su sayar da \u0253angaren da su ka gada, domin su taimaki rayuwar su, musamman ganin cewa su Bala da su ka saida nasu sun yi amfani da ku\u0257in sun yi gidan kan su, sun huta da haya, sun rufa wa kan su asiri. Na san a\u0199alla mutum uku da su ka so su yi hakan su ma, amma aka kwa\u0253e su, aka nuna masu muhimmancin ri\u0199e wannan gida a matsayin abin tarihi (<em>historical legacy<\/em>). Sun amince (amma ta ciki na ciki). To, idan yanzu akwai masu tsawatawa a kan kada \u2018ya\u2019yan Shata su sayar da gidan, nan gaba fa?<\/p>\n<p>Sai dai duk da yake sayarwar ba laifi ba ne a addinance ko a hukumance, na yarda da cewa aje gidan a matsayin kayan tarihi ya na da matu\u0199ar tarihi. Amma ni a nawa ganin yin hakan kuma ba ha\u0199\u0199in \u2018ya\u2019yan Shata ba ne su ka\u0257ai. Ha\u0199\u0199i ne na hukuma da duk masoyan Shata da masu rajin adana kayayyakin tarihin mu na gargajiya.<\/p>\n<p>Me zai hana gwamnatin Jihar Katsina ta sayi wannan gida, ta mallaka shi ga Hukumar Tarihi Da Al\u2019adu ko Jami\u2019ar Umaru Musa Yar\u2019Adua a matsayin cibiyar nazarin ka\u0257e-ka\u0257en Hausa? Ana ma iya sayen gidajen ma\u0199wabtan Shata a\u0199alla guda hu\u0257u domin a fa\u0257a\u0257a wajen, a samar da ofisoshi da laburare da wurin fakin motoci da masallaci da inda za a shuka fulawoyi da itatuwa. Wannan aiki ya fi \u0199arfin \u0257an Shata ko wani mai \u0257an \u0199arfi! Kada ma a bari wani mutum guda \u0257aya ya saya, ko wata \u0199ungiya mai zaman kan ta, domin matsalolin da ka iya tasowa. Mallakin gwamnati ya fi zama dindindin. Idan ma wani attajiri ya ce zai saya, to sai dai ya saya wa hukumar tarihi ko ita jami\u2019ar.<\/p>\n<p>Abu mai muhimmanci shi ne kada a banzatar da halin da iyalan Shata su ke ciki. A gaskiya, su na da bu\u0199atu nasu na kan su kamar kowa, kuma duk mun san cewa rayuwa ta yi wuya a yanzu. Wa ya damu da halin da su ke ci? Wa ke taimaka masu? Ko aikin yi ko tallafin \u0199aro karatu ba a ba su, don darajar mahaifin su. Sannan gwamnati ba ta damu da gidan Shatan ba a matsayin wani abu na tarihi. Kai, Shatan ma kan shi gwamnati ba ta damu da shi ba a yanzu! Me ta yi don karrama shi? Me ta yi wa iyalin sa?<\/p>\n<p>Na ta\u0253a kiran taro wanda na ke jin shi ne na farko na tunawa da Shata shekaru tara da su ka gabata inda na lissafa wa\u0257annan muradai da na ambata a sama. Mun yi taron a ranar 15 ga Yuni, 2013 a Gidan Arewa da ke Kaduna inda mu ka kafa \u0198ungiyar Tunawa Da Mamman Shata (wato <em>Mamman Shata Memorial Association<\/em> a turance) domin tunkarar al\u2019amarin tattara kayan tarihin Shata har da sauran maka\u0257an Hausa baki \u0257aya, wanda zai kasance a \u0199ar\u0199ashin wata cibiyar bincike ta musamman mai suna \u2018Mamman Shata Centre\u2019 ko \u2018Mamman Shata Hausa Music Centre\u2019. Wasu \u2018ya\u2019yan Shata sun halarci taron, irin su Jamila, marigayi Mamuda, Sagir (Bala), Mukhtar, Halima (Dubulle) da Maimuna \u0257iyar matar da Shata ya fara aura a rayuwar sa, da sauran su. Akwai kuma mu masoyan Shata; ban da ni akwai Hamisu Adamu Gamarali Funtua (wanda aka za\u0253a a matsayin shugaban \u0199ungiyar), Yusuf Tijjani Albasu, Kabir Umar (PRO), Aliyu Ibrahim \u0198an\u0199ara, Al-Amin Ciroma, Muhammad Sani Umar Faskari, Abdullahi \u018aantasi Funtua, Abba Muhammad, Abubakar Yusuf Ladan, Aliyu Abdullahi Gora, Salisu Fa\u2019ida Funtua, da sauran su. Rahoton taron da jawabin da na yi duk su na cikin littafin \u2018Shata Ikon Allah!\u2019 da na rubuta (shafi na 884 zuwa na 885 da kuma shafi na 893 zuwa na 896). A \u0199arshe, rarrabuwar kai ta farra\u0199a \u0199ungiyar. Yanzu mun bar wa \u201cgwanayen abin\u201d (wa\u0257anda su ka rusa wancan \u0199udirin na farko), su yi mu gani.<\/p>\n<p>Saboda haka dai, batun maida gidan Shata wata cibiya, ba a yau aka fara shi ba. Amma maganar da ake yi a yanzu duk ta fatar baki ce kurum domin an kasa \u0257aukar \u0199wa\u0199\u0199waran mataki a kai. Masu kurin cewa su masoyan Shata ne, su tashi tsaye mu gani. Za mu so su ida wannan nufi da mu ka sa wa \u0257an \u2018ba\u2019 shekara 9 da ta gabata.<\/p>\n<p>Amma fa ko me za a yi, to a yi shi tare da batun taimaka wa \u2018ya\u2019yan Shata wa\u0257anda ke bu\u0199atar taimako. Akwai maza da mata (wasu matan ma mazajen su sun mutu sun bar su da yara, jikokin Shatan) wa\u0257anda ke bu\u0199atar taimako. Duk wani surutu a kan a samar da cibiyar tarihin Shata zai kasance zancen kwabo idan har ba a kula da halin da iyalin Baba Shata ke ciki ba. Don haka ma, idan sun sayar da kayan sa da su ka gada, ciki har da gidan, ba su yi wa kowa laifi ba. Ko shi Shatan da bakin shi ya ce idan sun sayar da wannan gida na Funtuwa, ba laifi ba ne domin \u0199asa ce kawai da ya tara.<\/p>\n<p>Ina so a sani cewa a yanzu ko da wani ya saye gidan baki \u0257ayan sa, za a iya saya a wajen sa ko magadan sa (tare da babbar riba) a lokacin da masu kishin abin na gaskiya su ka zo \u2013 kila a wani \u0199arnin bayan namu. Yanzu kam ni ban ga laifin masu sayarwa ba domin su tsira da mutuncin kan su ko su samu abin sakawa a bakin salati. To Malam, ina amfanin ba\u0257i ba rai?<\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div>\n<p id=\"pvc_stats_5099\" class=\"pvc_stats total_only  \" data-element-id=\"5099\" style=\"\"><i class=\"pvc-stats-icon medium\" aria-hidden=\"true\"><svg xmlns=\"http:\/\/www.w3.org\/2000\/svg\" version=\"1.0\" viewBox=\"0 0 502 315\" preserveAspectRatio=\"xMidYMid meet\"><g transform=\"translate(0,332) scale(0.1,-0.1)\" fill=\"\" stroke=\"none\"><path d=\"M2394 3279 l-29 -30 -3 -207 c-2 -182 0 -211 15 -242 39 -76 157 -76 196 0 15 31 17 60 15 243 l-3 209 -33 29 c-26 23 -41 29 -80 29 -41 0 -53 -5 -78 -31z\"\/><path d=\"M3085 3251 c-45 -19 -58 -50 -96 -229 -47 -217 -49 -260 -13 -295 52 -53 146 -42 177 20 16 31 87 366 87 410 0 70 -86 122 -155 94z\"\/><path d=\"M1751 3234 c-13 -9 -29 -31 -37 -50 -12 -29 -10 -49 21 -204 19 -94 39 -189 45 -210 14 -50 54 -80 110 -80 34 0 48 6 76 34 21 21 34 44 34 59 0 14 -18 113 -40 219 -37 178 -43 195 -70 221 -36 32 -101 37 -139 11z\"\/><path d=\"M1163 3073 c-36 -7 -73 -59 -73 -102 0 -56 133 -378 171 -413 34 -32 83 -37 129 -13 70 36 67 87 -16 290 -86 209 -89 214 -129 231 -35 14 -42 15 -82 7z\"\/><path d=\"M3689 3066 c-15 -9 -33 -30 -42 -48 -48 -103 -147 -355 -147 -375 0 -98 131 -148 192 -74 13 15 57 108 97 206 80 196 84 226 37 273 -30 30 -99 39 -137 18z\"\/><path d=\"M583 2784 c-38 -19 -67 -74 -58 -113 9 -42 211 -354 242 -373 16 -10 45 -18 66 -18 51 0 107 52 107 100 0 39 -1 41 -124 234 -80 126 -108 162 -133 173 -41 17 -61 16 -100 -3z\"\/><path d=\"M4250 2784 c-14 -9 -74 -91 -133 -183 -95 -150 -107 -173 -107 -213 0 -55 33 -94 87 -104 67 -13 90 8 211 198 130 202 137 225 78 284 -27 27 -42 34 -72 34 -22 0 -50 -8 -64 -16z\"\/><path d=\"M2275 2693 c-553 -48 -1095 -270 -1585 -649 -135 -104 -459 -423 -483 -476 -23 -49 -22 -139 2 -186 73 -142 361 -457 571 -626 285 -228 642 -407 990 -497 242 -63 336 -73 660 -74 310 0 370 5 595 52 535 111 1045 392 1455 803 122 121 250 273 275 326 19 41 19 137 0 174 -41 79 -309 363 -465 492 -447 370 -946 591 -1479 653 -113 14 -422 18 -536 8z m395 -428 c171 -34 330 -124 456 -258 112 -119 167 -219 211 -378 27 -96 24 -300 -5 -401 -72 -255 -236 -447 -474 -557 -132 -62 -201 -76 -368 -76 -167 0 -236 14 -368 76 -213 98 -373 271 -451 485 -162 444 86 934 547 1084 153 49 292 57 452 25z m909 -232 c222 -123 408 -262 593 -441 76 -74 138 -139 138 -144 0 -16 -233 -242 -330 -319 -155 -123 -309 -223 -461 -299 l-81 -41 32 46 c18 26 49 83 70 128 143 306 141 649 -6 957 -25 52 -61 116 -79 142 l-34 47 45 -20 c26 -10 76 -36 113 -56z m-2057 25 c-40 -58 -105 -190 -130 -263 -110 -324 -59 -707 132 -981 25 -35 42 -64 37 -64 -19 0 -241 119 -326 174 -188 122 -406 314 -532 468 l-58 71 108 103 c185 178 428 349 672 473 66 33 121 60 123 61 2 0 -10 -19 -26 -42z\"\/><path d=\"M2375 1950 c-198 -44 -350 -190 -395 -379 -18 -76 -8 -221 19 -290 114 -284 457 -406 731 -260 98 52 188 154 231 260 27 69 37 214 19 290 -38 163 -166 304 -326 360 -67 23 -215 33 -279 19z\"\/><\/g><\/svg><\/i> <img data-recalc-dims=\"1\" loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"16\" height=\"16\" alt=\"Loading\" src=\"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/plugins\/page-views-count\/ajax-loader-2x.gif?resize=16%2C16&#038;ssl=1\" border=0 \/><\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>A yau, na wayi gari na ga ana nuna damuwa a soshiyal midiya a kan ji-ta-ji-tar wai \u2018ya\u2019yan Alhaji Mamman Shata sun sayar da gidan mahaifin su da ke Funtuwa, ana cewa bai kamata ba. Na farko, ina bada tabbacin cewa ba a sayar da wannan gidan ba. To amma wani hanzari ba gudu ba, [&hellip;]<\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div>\n<p id=\"pvc_stats_5099\" class=\"pvc_stats total_only  \" data-element-id=\"5099\" style=\"\"><i class=\"pvc-stats-icon medium\" aria-hidden=\"true\"><svg xmlns=\"http:\/\/www.w3.org\/2000\/svg\" version=\"1.0\" viewBox=\"0 0 502 315\" preserveAspectRatio=\"xMidYMid meet\"><g transform=\"translate(0,332) scale(0.1,-0.1)\" fill=\"\" stroke=\"none\"><path d=\"M2394 3279 l-29 -30 -3 -207 c-2 -182 0 -211 15 -242 39 -76 157 -76 196 0 15 31 17 60 15 243 l-3 209 -33 29 c-26 23 -41 29 -80 29 -41 0 -53 -5 -78 -31z\"\/><path d=\"M3085 3251 c-45 -19 -58 -50 -96 -229 -47 -217 -49 -260 -13 -295 52 -53 146 -42 177 20 16 31 87 366 87 410 0 70 -86 122 -155 94z\"\/><path d=\"M1751 3234 c-13 -9 -29 -31 -37 -50 -12 -29 -10 -49 21 -204 19 -94 39 -189 45 -210 14 -50 54 -80 110 -80 34 0 48 6 76 34 21 21 34 44 34 59 0 14 -18 113 -40 219 -37 178 -43 195 -70 221 -36 32 -101 37 -139 11z\"\/><path d=\"M1163 3073 c-36 -7 -73 -59 -73 -102 0 -56 133 -378 171 -413 34 -32 83 -37 129 -13 70 36 67 87 -16 290 -86 209 -89 214 -129 231 -35 14 -42 15 -82 7z\"\/><path d=\"M3689 3066 c-15 -9 -33 -30 -42 -48 -48 -103 -147 -355 -147 -375 0 -98 131 -148 192 -74 13 15 57 108 97 206 80 196 84 226 37 273 -30 30 -99 39 -137 18z\"\/><path d=\"M583 2784 c-38 -19 -67 -74 -58 -113 9 -42 211 -354 242 -373 16 -10 45 -18 66 -18 51 0 107 52 107 100 0 39 -1 41 -124 234 -80 126 -108 162 -133 173 -41 17 -61 16 -100 -3z\"\/><path d=\"M4250 2784 c-14 -9 -74 -91 -133 -183 -95 -150 -107 -173 -107 -213 0 -55 33 -94 87 -104 67 -13 90 8 211 198 130 202 137 225 78 284 -27 27 -42 34 -72 34 -22 0 -50 -8 -64 -16z\"\/><path d=\"M2275 2693 c-553 -48 -1095 -270 -1585 -649 -135 -104 -459 -423 -483 -476 -23 -49 -22 -139 2 -186 73 -142 361 -457 571 -626 285 -228 642 -407 990 -497 242 -63 336 -73 660 -74 310 0 370 5 595 52 535 111 1045 392 1455 803 122 121 250 273 275 326 19 41 19 137 0 174 -41 79 -309 363 -465 492 -447 370 -946 591 -1479 653 -113 14 -422 18 -536 8z m395 -428 c171 -34 330 -124 456 -258 112 -119 167 -219 211 -378 27 -96 24 -300 -5 -401 -72 -255 -236 -447 -474 -557 -132 -62 -201 -76 -368 -76 -167 0 -236 14 -368 76 -213 98 -373 271 -451 485 -162 444 86 934 547 1084 153 49 292 57 452 25z m909 -232 c222 -123 408 -262 593 -441 76 -74 138 -139 138 -144 0 -16 -233 -242 -330 -319 -155 -123 -309 -223 -461 -299 l-81 -41 32 46 c18 26 49 83 70 128 143 306 141 649 -6 957 -25 52 -61 116 -79 142 l-34 47 45 -20 c26 -10 76 -36 113 -56z m-2057 25 c-40 -58 -105 -190 -130 -263 -110 -324 -59 -707 132 -981 25 -35 42 -64 37 -64 -19 0 -241 119 -326 174 -188 122 -406 314 -532 468 l-58 71 108 103 c185 178 428 349 672 473 66 33 121 60 123 61 2 0 -10 -19 -26 -42z\"\/><path d=\"M2375 1950 c-198 -44 -350 -190 -395 -379 -18 -76 -8 -221 19 -290 114 -284 457 -406 731 -260 98 52 188 154 231 260 27 69 37 214 19 290 -38 163 -166 304 -326 360 -67 23 -215 33 -279 19z\"\/><\/g><\/svg><\/i> <img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"16\" height=\"16\" alt=\"Loading\" src=\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/plugins\/page-views-count\/ajax-loader-2x.gif\" border=0 \/><\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div>\n","protected":false},"author":5,"featured_media":5100,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_FSMCFIC_featured_image_caption":"","_FSMCFIC_featured_image_nocaption":"","_FSMCFIC_featured_image_hide":"","_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[422],"tags":[19],"class_list":["post-5099","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-waoi","tag-mamman-shata"],"yoast_head":"<!-- This site is optimized with the Yoast SEO plugin v26.9 - https:\/\/yoast.com\/product\/yoast-seo-wordpress\/ -->\n<title>Laifi ne idan an sayar da gidan Shata? - Ibrahim Sheme<\/title>\n<meta name=\"robots\" content=\"index, follow, max-snippet:-1, max-image-preview:large, max-video-preview:-1\" \/>\n<link rel=\"canonical\" href=\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5099\" \/>\n<meta property=\"og:locale\" content=\"en_GB\" \/>\n<meta property=\"og:type\" content=\"article\" \/>\n<meta property=\"og:title\" content=\"Laifi ne idan an sayar da gidan Shata? - Ibrahim Sheme\" \/>\n<meta property=\"og:description\" content=\"A yau, na wayi gari na ga ana nuna damuwa a soshiyal midiya a kan ji-ta-ji-tar wai \u2018ya\u2019yan Alhaji Mamman Shata sun sayar da gidan mahaifin su da ke Funtuwa, ana cewa bai kamata ba. Na farko, ina bada tabbacin cewa ba a sayar da wannan gidan ba. To amma wani hanzari ba gudu ba, [&hellip;]\" \/>\n<meta property=\"og:url\" content=\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5099\" \/>\n<meta property=\"og:site_name\" content=\"Ibrahim Sheme\" \/>\n<meta property=\"article:published_time\" content=\"2022-02-03T13:39:29+00:00\" \/>\n<meta property=\"article:modified_time\" content=\"2024-04-23T07:56:19+00:00\" \/>\n<meta property=\"og:image\" content=\"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2023\/11\/IMG-20220203-WA0009.jpg?fit=1032%2C726&ssl=1\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:width\" content=\"1032\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:height\" content=\"726\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:type\" content=\"image\/jpeg\" \/>\n<meta name=\"author\" content=\"Nafisat@ibrahimsheme.com\" \/>\n<meta name=\"twitter:card\" content=\"summary_large_image\" \/>\n<meta name=\"twitter:label1\" content=\"Written by\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data1\" content=\"IBRAHIM SHEME\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:label2\" content=\"Estimated reading time\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data2\" content=\"6 minutes\" \/>\n<script type=\"application\/ld+json\" class=\"yoast-schema-graph\">{\"@context\":\"https:\/\/schema.org\",\"@graph\":[{\"@type\":\"Article\",\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5099#article\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5099\"},\"author\":{\"name\":\"Nafisat@ibrahimsheme.com\",\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#\/schema\/person\/75c95be2f573872fa0335010b9a5e74f\"},\"headline\":\"Laifi ne idan an sayar da gidan Shata?\",\"datePublished\":\"2022-02-03T13:39:29+00:00\",\"dateModified\":\"2024-04-23T07:56:19+00:00\",\"mainEntityOfPage\":{\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5099\"},\"wordCount\":1268,\"commentCount\":0,\"publisher\":{\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#organization\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5099#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2023\/11\/IMG-20220203-WA0009.jpg?fit=1032%2C726&ssl=1\",\"keywords\":[\"mamman shata\"],\"articleSection\":[\"Wa\u0199a\"],\"inLanguage\":\"en-GB\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"CommentAction\",\"name\":\"Comment\",\"target\":[\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5099#respond\"]}]},{\"@type\":\"WebPage\",\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5099\",\"url\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5099\",\"name\":\"Laifi ne idan an sayar da gidan Shata? - Ibrahim Sheme\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#website\"},\"primaryImageOfPage\":{\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5099#primaryimage\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5099#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2023\/11\/IMG-20220203-WA0009.jpg?fit=1032%2C726&ssl=1\",\"datePublished\":\"2022-02-03T13:39:29+00:00\",\"dateModified\":\"2024-04-23T07:56:19+00:00\",\"breadcrumb\":{\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5099#breadcrumb\"},\"inLanguage\":\"en-GB\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"ReadAction\",\"target\":[\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5099\"]}]},{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-GB\",\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5099#primaryimage\",\"url\":\"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2023\/11\/IMG-20220203-WA0009.jpg?fit=1032%2C726&ssl=1\",\"contentUrl\":\"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2023\/11\/IMG-20220203-WA0009.jpg?fit=1032%2C726&ssl=1\",\"width\":1032,\"height\":726,\"caption\":\"Gidan Alhaji (Dakta) Mamman Shata da ke Funtuwa... a shekarar da ya rasu, 1999\"},{\"@type\":\"BreadcrumbList\",\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5099#breadcrumb\",\"itemListElement\":[{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":1,\"name\":\"Home\",\"item\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/\"},{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":2,\"name\":\"Laifi ne idan an sayar da gidan Shata?\"}]},{\"@type\":\"WebSite\",\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#website\",\"url\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/\",\"name\":\"Ibrahim Sheme\",\"description\":\"\",\"publisher\":{\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#organization\"},\"potentialAction\":[{\"@type\":\"SearchAction\",\"target\":{\"@type\":\"EntryPoint\",\"urlTemplate\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?s={search_term_string}\"},\"query-input\":{\"@type\":\"PropertyValueSpecification\",\"valueRequired\":true,\"valueName\":\"search_term_string\"}}],\"inLanguage\":\"en-GB\"},{\"@type\":\"Organization\",\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#organization\",\"name\":\"Ibrahim Sheme\",\"url\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/\",\"logo\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-GB\",\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#\/schema\/logo\/image\/\",\"url\":\"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1\",\"contentUrl\":\"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1\",\"width\":512,\"height\":512,\"caption\":\"Ibrahim Sheme\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#\/schema\/logo\/image\/\"}},{\"@type\":\"Person\",\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#\/schema\/person\/75c95be2f573872fa0335010b9a5e74f\",\"name\":\"Nafisat@ibrahimsheme.com\",\"image\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-GB\",\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#\/schema\/person\/image\/\",\"url\":\"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/f15431c84219439c4441de28a5ea621c90236e7dc8a8934db0967eeaf5f7382a?s=96&d=mm&r=g\",\"contentUrl\":\"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/f15431c84219439c4441de28a5ea621c90236e7dc8a8934db0967eeaf5f7382a?s=96&d=mm&r=g\",\"caption\":\"Nafisat@ibrahimsheme.com\"},\"sameAs\":[\"https:\/\/ibrahimsheme.com\"],\"url\":\"\"}]}<\/script>\n<!-- \/ Yoast SEO plugin. -->","yoast_head_json":{"title":"Laifi ne idan an sayar da gidan Shata? - Ibrahim Sheme","robots":{"index":"index","follow":"follow","max-snippet":"max-snippet:-1","max-image-preview":"max-image-preview:large","max-video-preview":"max-video-preview:-1"},"canonical":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5099","og_locale":"en_GB","og_type":"article","og_title":"Laifi ne idan an sayar da gidan Shata? - Ibrahim Sheme","og_description":"A yau, na wayi gari na ga ana nuna damuwa a soshiyal midiya a kan ji-ta-ji-tar wai \u2018ya\u2019yan Alhaji Mamman Shata sun sayar da gidan mahaifin su da ke Funtuwa, ana cewa bai kamata ba. Na farko, ina bada tabbacin cewa ba a sayar da wannan gidan ba. To amma wani hanzari ba gudu ba, [&hellip;]","og_url":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5099","og_site_name":"Ibrahim Sheme","article_published_time":"2022-02-03T13:39:29+00:00","article_modified_time":"2024-04-23T07:56:19+00:00","og_image":[{"width":1032,"height":726,"url":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2023\/11\/IMG-20220203-WA0009.jpg?fit=1032%2C726&ssl=1","type":"image\/jpeg"}],"author":"Nafisat@ibrahimsheme.com","twitter_card":"summary_large_image","twitter_misc":{"Written by":"IBRAHIM SHEME","Estimated reading time":"6 minutes"},"schema":{"@context":"https:\/\/schema.org","@graph":[{"@type":"Article","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5099#article","isPartOf":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5099"},"author":{"name":"Nafisat@ibrahimsheme.com","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#\/schema\/person\/75c95be2f573872fa0335010b9a5e74f"},"headline":"Laifi ne idan an sayar da gidan Shata?","datePublished":"2022-02-03T13:39:29+00:00","dateModified":"2024-04-23T07:56:19+00:00","mainEntityOfPage":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5099"},"wordCount":1268,"commentCount":0,"publisher":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#organization"},"image":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5099#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2023\/11\/IMG-20220203-WA0009.jpg?fit=1032%2C726&ssl=1","keywords":["mamman shata"],"articleSection":["Wa\u0199a"],"inLanguage":"en-GB","potentialAction":[{"@type":"CommentAction","name":"Comment","target":["https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5099#respond"]}]},{"@type":"WebPage","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5099","url":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5099","name":"Laifi ne idan an sayar da gidan Shata? - Ibrahim Sheme","isPartOf":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#website"},"primaryImageOfPage":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5099#primaryimage"},"image":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5099#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2023\/11\/IMG-20220203-WA0009.jpg?fit=1032%2C726&ssl=1","datePublished":"2022-02-03T13:39:29+00:00","dateModified":"2024-04-23T07:56:19+00:00","breadcrumb":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5099#breadcrumb"},"inLanguage":"en-GB","potentialAction":[{"@type":"ReadAction","target":["https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5099"]}]},{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-GB","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5099#primaryimage","url":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2023\/11\/IMG-20220203-WA0009.jpg?fit=1032%2C726&ssl=1","contentUrl":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2023\/11\/IMG-20220203-WA0009.jpg?fit=1032%2C726&ssl=1","width":1032,"height":726,"caption":"Gidan Alhaji (Dakta) Mamman Shata da ke Funtuwa... a shekarar da ya rasu, 1999"},{"@type":"BreadcrumbList","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5099#breadcrumb","itemListElement":[{"@type":"ListItem","position":1,"name":"Home","item":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/"},{"@type":"ListItem","position":2,"name":"Laifi ne idan an sayar da gidan Shata?"}]},{"@type":"WebSite","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#website","url":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/","name":"Ibrahim Sheme","description":"","publisher":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#organization"},"potentialAction":[{"@type":"SearchAction","target":{"@type":"EntryPoint","urlTemplate":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?s={search_term_string}"},"query-input":{"@type":"PropertyValueSpecification","valueRequired":true,"valueName":"search_term_string"}}],"inLanguage":"en-GB"},{"@type":"Organization","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#organization","name":"Ibrahim Sheme","url":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/","logo":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-GB","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#\/schema\/logo\/image\/","url":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1","contentUrl":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1","width":512,"height":512,"caption":"Ibrahim Sheme"},"image":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#\/schema\/logo\/image\/"}},{"@type":"Person","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#\/schema\/person\/75c95be2f573872fa0335010b9a5e74f","name":"Nafisat@ibrahimsheme.com","image":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-GB","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#\/schema\/person\/image\/","url":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/f15431c84219439c4441de28a5ea621c90236e7dc8a8934db0967eeaf5f7382a?s=96&d=mm&r=g","contentUrl":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/f15431c84219439c4441de28a5ea621c90236e7dc8a8934db0967eeaf5f7382a?s=96&d=mm&r=g","caption":"Nafisat@ibrahimsheme.com"},"sameAs":["https:\/\/ibrahimsheme.com"],"url":""}]}},"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2023\/11\/IMG-20220203-WA0009.jpg?fit=1032%2C726&ssl=1","jetpack_likes_enabled":true,"jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/5099","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/5"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=5099"}],"version-history":[{"count":2,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/5099\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":5107,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/5099\/revisions\/5107"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/5100"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=5099"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=5099"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=5099"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}