{"id":5073,"date":"2013-06-16T17:17:34","date_gmt":"2013-06-16T17:17:34","guid":{"rendered":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5073"},"modified":"2023-11-26T08:02:52","modified_gmt":"2023-11-26T08:02:52","slug":"bu%c6%99atar-samun-cibiyar-wa%c6%99o%c6%99i","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5073","title":{"rendered":"Bu\u0199atar Samun Cibiyar Wa\u0199o\u0199i ta Mamman Shata"},"content":{"rendered":"<p style=\"text-align: center;\"><em>\u0198ungiyar Tunawa Da Mamman Shata (Mamman Shata Memorial Association)<\/em><\/p>\n<p style=\"text-align: center;\"><em>TARON FARKO<\/em><\/p>\n<p style=\"text-align: center;\"><em>Arewa House, Kaduna<\/em><\/p>\n<p style=\"text-align: center;\"><em>Asabar, 15 ga Yuni, 2013<\/em><\/p>\n<p style=\"text-align: center;\"><strong>JAWABI KAN MA\u0198ASUDIN KIRAN TARO DAGA MAI KIRAN TARO, MALAM IBRAHIM SHEME, Editan Jaridar Leadership<\/strong><\/p>\n<p>Ina farawa da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin\u0199ai. Tsira da Amincin Allah su tabbata ga Annabin mu, fiyayyen talikai, Muhammad (SAW).<\/p>\n<p>Da farko ina addu\u2019a Allah ya ji\u0199an Alhaji Mamman Shata, Allah Ya yi masa sakayya da gidan Aljannar Firdausi, ya albarkaci bayan shi, ya sa ayyukan sa na alheri su zama tsira a gare shi, kuma ya yafe kurakuran da ya aikata, amin summa amin.<\/p>\n<p>Mahalartan wannan taro kuma ina godiya a gare ku da ku ka amsa gayyatar mu, ku ka taso daga garuruwa daban-daban, wasun ku ma su ka yo asubanci, ku ka zo wannan gari domin halartar wannan taro wanda mu ke fatan Allah ya sa wa albarka. Na yi farin ciki \u0199warai ganin cewa kowannen ku ya na da aikin da ya sa a gaba, amma a yau ya sadaukar da lokacin sa, ya bar duk abin da ya ke yi, ya zo. Wannan ba \u0199aramin \u0199o\u0199ari ba ne, kuma alama ce ta goyon bayan da ku ka bayar ga shukar da mu ke son mu yi a yau. Na gode \u0199warai da gaske.<\/p>\n<p>Ina farin ciki matu\u0199a da Allah (Subhanahu wa Ta\u2019ala) ya nuna mana wannan rana wadda mu ka da\u0257e mu na tsinkayar zuwan ta. Rana ce wadda a cikin ta mu ke yin zaman farko domin sa \u0257an \u2018ba\u2019 a wani yun\u0199uri na karrama wani fasihi wanda babu irin shi a fagen sa na wa\u0199a a \u0199asar Hausa, wato Alhaji (Dr) Mamman Shata Katsina. Kuma wannan karramawa ita ce ta farko da aka yi masa tun bayan rasuwar sa a ran 18 ga Yuni, 1999. Wato kenan nan da kwana uku kacal zai cika shekara 14 da barin duniya. Duk da yake wannan karramawa ba irin ta ba shi takarda ko lambar girma ba ce kamar yadda Gwamnatin Tarayya da kuma Jami\u2019ar Ahmadu Bello su ka ta\u0253a yi masa, ita ma wannan kwatankwacin irin wa\u0257annan \u0257in ce, domin ita ma wani yun\u0199uri ne na nuna gamsuwa da aikin da Alhaji Shata ya yi wa \u0199asar nan, musamman gudunmawar sa ga cigaban \u0199asa ta hanyar yin amfani da fasahar da Allah ya yi masa.<\/p>\n<p>A ta\u0199aice, ba tare da na yi dogon sharhi kan irin wannan gudunmawa tasa ba, zan iya cewa Shata ya fa\u0257akar da \u2019yan Nijeriya tare da nisha\u0257antar da su ta hanyar wa\u0199o\u0199in sa, wa\u0257anda ke cike da nusarwa; wasu su jefa ka kogin tunani, wasu su sa ka dariya, kai wasu ma su ba ka haushi a bisa irin fahimtar da ka yi masu. Ya taimaka \u0199warai wajen adana tarihi da al\u2019adun Malam Bahaushe. Don haka mu ke ganin ya kamata a yi wani ho\u0253\u0253asa na ci gaba da tuno da wannan bawan Allah a kai a kai, musamman a \u0199ungiyance. Da gaske ne cewa ko ba mu yi wani abu ba da wuya a manta da shi tunda dai ya bar dubban wa\u0199o\u0199i da ake sawa a gidajen rediyo da na talabijin, kuma mutum zai iya jin su a motar sa ko a komfuta ko a intanet, to amma duk da haka mu na ganin cewa idan mu ka yi wani tsari na daban ban da wa\u0257ancan, to sanya sunan Shata a zukatan jama\u2019a zai \u0199aru.<\/p>\n<p>Saboda haka ne mu ka ga dacewar a kafa wata \u0199ungiya don tunawa da shi, wadda za ta ri\u0199a aiwatar da wasu tsare-tsare da ayyuka wa\u0257anda za su sa a \u0199ara zurfafa tunawa da shi tare da ba shi matsayin da ya dace da fasihai irin shi. Babu shakka, akwai fasihai irin Shata da aka yi wa hakan a wasu \u0199asashen, sannan a nan \u0199asar an yi wa manyan \u2019yan siyasa da kishin \u0199asa irin wannan \u0199ungiyar, kun ga kenan yin hakan ba wani sabon abu ba ne.<\/p>\n<figure id=\"attachment_5111\" aria-describedby=\"caption-attachment-5111\" style=\"width: 300px\" class=\"wp-caption alignnone\"><img data-recalc-dims=\"1\" loading=\"lazy\" decoding=\"async\" data-attachment-id=\"5111\" data-permalink=\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?attachment_id=5111\" data-orig-file=\"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2013\/06\/Cropped_Image_20231108_005006-scaled.jpg?fit=2560%2C1669&amp;ssl=1\" data-orig-size=\"2560,1669\" data-comments-opened=\"1\" data-image-meta=\"{&quot;aperture&quot;:&quot;0&quot;,&quot;credit&quot;:&quot;&quot;,&quot;camera&quot;:&quot;&quot;,&quot;caption&quot;:&quot;&quot;,&quot;created_timestamp&quot;:&quot;0&quot;,&quot;copyright&quot;:&quot;&quot;,&quot;focal_length&quot;:&quot;0&quot;,&quot;iso&quot;:&quot;0&quot;,&quot;shutter_speed&quot;:&quot;0&quot;,&quot;title&quot;:&quot;&quot;,&quot;orientation&quot;:&quot;0&quot;}\" data-image-title=\"Cropped_Image_20231108_005006\" data-image-description=\"\" data-image-caption=\"&lt;p&gt;Taron farko kan tunawa da Alhaji Mamman Shata &lt;\/p&gt;\n\" data-medium-file=\"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2013\/06\/Cropped_Image_20231108_005006-scaled.jpg?fit=300%2C196&amp;ssl=1\" data-large-file=\"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2013\/06\/Cropped_Image_20231108_005006-scaled.jpg?fit=1024%2C667&amp;ssl=1\" class=\"size-medium wp-image-5111\" src=\"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2013\/06\/Cropped_Image_20231108_005006.jpg?resize=300%2C196&#038;ssl=1\" alt=\"\" width=\"300\" height=\"196\" srcset=\"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2013\/06\/Cropped_Image_20231108_005006-scaled.jpg?resize=300%2C196&amp;ssl=1 300w, https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2013\/06\/Cropped_Image_20231108_005006-scaled.jpg?resize=1024%2C667&amp;ssl=1 1024w, https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2013\/06\/Cropped_Image_20231108_005006-scaled.jpg?resize=768%2C501&amp;ssl=1 768w, https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2013\/06\/Cropped_Image_20231108_005006-scaled.jpg?resize=1536%2C1001&amp;ssl=1 1536w, https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2013\/06\/Cropped_Image_20231108_005006-scaled.jpg?resize=2048%2C1335&amp;ssl=1 2048w, https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2013\/06\/Cropped_Image_20231108_005006-scaled.jpg?resize=750%2C489&amp;ssl=1 750w, https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2013\/06\/Cropped_Image_20231108_005006-scaled.jpg?resize=1140%2C743&amp;ssl=1 1140w\" sizes=\"auto, (max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/><figcaption id=\"caption-attachment-5111\" class=\"wp-caption-text\">Taron farko kan tunawa da Alhaji Mamman Shata<\/figcaption><\/figure>\n<p>Shin me wannan \u0199ungiya za ta iya yi? Na farko dai, za ta ri\u0199a shirya taro na kwana \u0257aya a duk shekara inda za a kira masana su gabatar da jawabi a kan wanene Shata da kuma ayyukan sa, kuma a yi masa addu\u2019a. Wannan taro za a iya shirya shi a daidai zagayowar ranar da ya rasu, wato 18 ga Yuni. Masoyan Shata da iyalan sa da jami\u2019an gwamnati da sauran jama\u2019ar da ke da sha\u2019awa za su iya halartar taron. Idan abin ya bun\u0199asa, \u0199ungiya za ta iya maida taron na kwana biyu ko na mako \u0257aya inda za a yi kamar kalankuwa ta maka\u0257a da mawa\u0199an Hausa inda kowannen su zai baje hajar sa. Na biyu, \u0199ungiyar za ta iya yin jagora wajen kafa wata cibiya da sunan, wato misali, <strong>Cibiyar Mamman Shata<\/strong> (<em>Mamman Shata Centre<\/em> a turance) ko <strong>Cibiyar Mawa\u0199an Hausa ta Mamman Shata<\/strong> (wato <em>Mamman Shata Hausa Music Centre)<\/em>. Ita wannan cibiya za ta kasance wani gidan tarihi ne inda za a tara duk wasu abubuwan tarihi da su ka shafi Shata. Babban dai shi ne wa\u0199o\u0199in sa. Za a tattaro duk wa\u0199o\u0199in sa a adana su a wannan gida da nufin samar da su ga masu bincike da masu saurare. Wannan ya na da muhimmanci, musamman idan mu ka yi la\u2019akari da cewa a yanzu wa\u0199o\u0199in Shata a warwatse su ke a kafafen ya\u0257a labarai (musamman gidajen rediyo da na talbijin), sannan wasu su na hannun \u0257ai\u0257aikun mutane. Akwai mutumin da ke da wa\u0199a \u0257ari, wani dubu ko fiye a hannun sa, akwai ma mai dubu uku! Sannan akwai mutumin da ya ce mani akwai wa\u0199ar da Shata ya yi masa wadda ba wanda ya ke da ita sai shi ka]ai. Ban ta\u0253a jin sunan mutumin ba, amma ya na kunna min wa\u0199ar a wayar sa sai ga muryar Shata na fita, ya na yi wa mutumin nan wa\u0199a.<\/p>\n<p>Su kan su gidajen rediyo da na talbijin da ke da laburare na wa\u0199o\u0199i, wasu babu tabbacin \u0257orewar ingancin wa\u0199o\u0199in.<\/p>\n<p>To, idan yau mu ne, gobe ba mu ba ne, saboda haka a duk ran da aka ce babu irin wa\u0257annan \u0257ai\u0257aikun mutanen sai ka ga wa\u0199o\u0199in da ke hannun su sun zama na gado, an rarraba su, daga nan sun shiga hanyar \u0253acewa. Saboda haka, Cibiya za ta yi \u0199o\u0199arin samo kwafe na duk wa\u0257annan wa\u0199o\u0199i na Shata domin a adana su a wannan gida na tarihi.<\/p>\n<p>Kuma wani abu shi ne yadda zamani ke sauyawa ta fuskar na\u2019urorin kimiyya. A da can, a farkon zamanin Shata, babu ma kayan rikodin. Wannan ya sa, kamar yadda shi da bakin sa ya fa\u0257a, ba a \u0257auki wasu wa\u0199o\u0199in da ya yi a faifai ba. Kun ga kenan babu su ko ka\u0257an, domin wasu bai maimaita su aka \u0257auka ba. Ana nan, da tafiya ta yi tafiya, sai aka zo ana samun wa\u0199o\u0199in sa a garmaho; daga nan sai kaset, sai kuma sidi (CD), sai ga dibidi (DVD), sai MP3 ya zo, sai MP4; ga su yanzu a intanet da kuma cikin wayoyin mutane. To nan gaba ba mu san abin da ke tafe ba. Ta yiwu a samu wata wa}a wadda na\u2019urar da ke akwai ba za ta iya sarrafa ta ba domin \u0199ila ba a riga aka juya ta zuwa sabon nau\u2019in kimiyyar ba tun a baya.<\/p>\n<p>Sannan ban da wa\u0199o\u0199i, wasu abubuwan na tarihi da za a iya tattarawa a wannan cibiya sun ha\u0257a da hotuna da tufafi da takalma da agogo da hula da duk wani abu da ya danganci mamacin. A \u0253angaren hotuna, a cibiyar za ka iya samun hotunan iyalin shi, da na mutanen da ya yi wa wa\u0199a da na wasu wurare da ya je ko ya ambata a wa\u0199a. Ga wani misali: lokacin da mu ke tattara tarihin Shata domin yin littafi, mun samo \u0257imbin hotunan mutanen da Shata ya yi wa wa\u0199a, da na Shatan da na iyalin shi. Wa\u0257annan hotuna su na nan a hannun mu. To ran da ba mu fa? Ka ga \u0199ila wasun su su salwanta. Amma in akwai cibiya, sai mu kai su can a aje saboda mai bu\u0199ata ya je ya gan su.<\/p>\n<p>Bugu da \u0199ari, ina hangen cewa wannan cibiya za ta iya kasancewa ta kowane mawa\u0199in Hausa, in dai wanda ya yi amfani da ki\u0257a ne. Wato irin su Naramba\u0257a, \u018aan\u0199wairo, Uji, \u018aanmaraya, Sarkin Taushi, \u018aan\u2019anace, Ahmadu Doka, Sirajo Mai Asharalle, \u018aanbade da Barmani Choge. Hatta maka\u0257an wannan zamanin, wa\u0257anda ke amfani da fiyano, irin su Aminu Ala, Adamu Nagudu, Yakubu Muhammad, Sani Danja, Abubakar Yarima, Fati Nijar, Maryam A. Baba, Rabi Mustapha, Umar M. Shariff, Adam A. Zango da ire-iren su da dama, za a iya samun wani wuri da aka ke\u0253e masu a wannan cibiya. Dalilin \u0199ara sauran maka\u0257a da mawa\u0199a a wannan tsari shi ne ganin cewa ba zai yiwu a yi cibiyoyi daban-daban a kan dukkan wa\u0257annan mawa\u0199an ba, wa\u0257anda su ma ya kamata a ce akwai inda mutum zai je kai-tsaye ya samu ayyukan fasahar su can wata rana lokacin da babu mu ko babu su \u2013 kamar yadda babu Shata a yau.<\/p>\n<p>Za a iya yin wannan cibiyar a garin da aka ga ya dace, Funtuwa ce ko Katsina ko Kano ko Kaduna, ko ma ina ne a \u0199asar Hausa. Kuma za ta iya kasancewa cibiya mai zaman kan ta kamar yadda ake da Cibiyar Shehu Musa Yar\u2019Adua a Abuja, sannan za ta iya zama a \u0199ar\u0199ashin wata jami\u2019a kamar yadda ake da Gidan Arewa don tunawa da Sardauna a Kaduna. Wannan \u0199ungiya tare da iyayen ta ko mashawartan ta za su iya yanke shawara a kan haka. Manufa dai ita ce a samu wani wuri inda za a tattara wa\u0199o\u0199i da tarihin Shata, \u0199ila kuma da na wasu mawa\u0199an, ta yadda tarihi ba zai shafe dukkan sassan su ba.<\/p>\n<p>Babu shakka, kai daga ji ka san cewa wannan aiki gagarumi ne. Aiki ne wanda ke bu\u0199atar lokaci, da sadaukarwa, da ha\u0257in kai, da kuma ku\u0257i masu gida rana. To amma duk da haka, aiki ne mai yiwuwa. Saboda haka ha\u0199\u0199in \u0199ungiya ne ta tabbatar da cewa ta \u0257auki aikin da gaske idan har da gasken ta ke yi. Kuma \u0199ungiya ta sani, ba ku\u0257i ne babba ba a wajen wannan aiki, a\u2019a, sadaukarwa ce da kuma \u0199auna ga wanda aka yi domin shi da kuma \u0199aunar mu ga al\u2019adu kyawawa na Hausa. Idan har akwai sadaukarwa, to ku\u0257in aikin sai su zo cikin sau\u0199i. Ina ro\u0199on ku da ku zage dantse, ku tashi tsaye wajen tabbatar da faruwar abin da mu ke so mu yi a wannan \u0199ungiya.<\/p>\n<p>Ha\u0257uwar mu a nan a yau alama ce ta irin \u0199aunar mu ga wannan aiki. Dukkan mu a nan mun zo ne saboda mun amince da mu yi wannan aikin, domin fa ba wanda aka aika wa da ku\u0257in mota kafin ya zo, ko aka ce za a ba shi na komawa gida. Saboda haka abin farin ciki na ne ganin cewa mun \u0199udiri aniyar yin wannan aiki.<\/p>\n<p>A \u0199arshe, ina kira ga iyalin Alhaji Shata, wa\u0257anda akwai wakilcin su a nan wurin, da su ba \u0199ungiyar nan ha\u0257in kai domin ta cimma \u0199udirorin ta. Idan sun yi hakan, to sun kyauta wa Baba Shata, kuma sun kyauta wa \u0199asar nan.<\/p>\n<p>Ina fatan tattaunawar mu za ta yi albarka, tare da addu\u2019ar Allah ya sa wannan shuka da za mu yi ta yi albarkar da kowannen mu zai yi farin ciki da ita.<\/p>\n<p>Ina ro\u0199on Allah da ya taimaka mana, ya ba mu ikon kafa wannan \u0199ungiya da gina ta da kuma aiwatar da \u0199udirorin ta, amin summa amin.<\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div>\n<p id=\"pvc_stats_5073\" class=\"pvc_stats total_only  \" data-element-id=\"5073\" style=\"\"><i class=\"pvc-stats-icon medium\" aria-hidden=\"true\"><svg xmlns=\"http:\/\/www.w3.org\/2000\/svg\" version=\"1.0\" viewBox=\"0 0 502 315\" preserveAspectRatio=\"xMidYMid meet\"><g transform=\"translate(0,332) scale(0.1,-0.1)\" fill=\"\" stroke=\"none\"><path d=\"M2394 3279 l-29 -30 -3 -207 c-2 -182 0 -211 15 -242 39 -76 157 -76 196 0 15 31 17 60 15 243 l-3 209 -33 29 c-26 23 -41 29 -80 29 -41 0 -53 -5 -78 -31z\"\/><path d=\"M3085 3251 c-45 -19 -58 -50 -96 -229 -47 -217 -49 -260 -13 -295 52 -53 146 -42 177 20 16 31 87 366 87 410 0 70 -86 122 -155 94z\"\/><path d=\"M1751 3234 c-13 -9 -29 -31 -37 -50 -12 -29 -10 -49 21 -204 19 -94 39 -189 45 -210 14 -50 54 -80 110 -80 34 0 48 6 76 34 21 21 34 44 34 59 0 14 -18 113 -40 219 -37 178 -43 195 -70 221 -36 32 -101 37 -139 11z\"\/><path d=\"M1163 3073 c-36 -7 -73 -59 -73 -102 0 -56 133 -378 171 -413 34 -32 83 -37 129 -13 70 36 67 87 -16 290 -86 209 -89 214 -129 231 -35 14 -42 15 -82 7z\"\/><path d=\"M3689 3066 c-15 -9 -33 -30 -42 -48 -48 -103 -147 -355 -147 -375 0 -98 131 -148 192 -74 13 15 57 108 97 206 80 196 84 226 37 273 -30 30 -99 39 -137 18z\"\/><path d=\"M583 2784 c-38 -19 -67 -74 -58 -113 9 -42 211 -354 242 -373 16 -10 45 -18 66 -18 51 0 107 52 107 100 0 39 -1 41 -124 234 -80 126 -108 162 -133 173 -41 17 -61 16 -100 -3z\"\/><path d=\"M4250 2784 c-14 -9 -74 -91 -133 -183 -95 -150 -107 -173 -107 -213 0 -55 33 -94 87 -104 67 -13 90 8 211 198 130 202 137 225 78 284 -27 27 -42 34 -72 34 -22 0 -50 -8 -64 -16z\"\/><path d=\"M2275 2693 c-553 -48 -1095 -270 -1585 -649 -135 -104 -459 -423 -483 -476 -23 -49 -22 -139 2 -186 73 -142 361 -457 571 -626 285 -228 642 -407 990 -497 242 -63 336 -73 660 -74 310 0 370 5 595 52 535 111 1045 392 1455 803 122 121 250 273 275 326 19 41 19 137 0 174 -41 79 -309 363 -465 492 -447 370 -946 591 -1479 653 -113 14 -422 18 -536 8z m395 -428 c171 -34 330 -124 456 -258 112 -119 167 -219 211 -378 27 -96 24 -300 -5 -401 -72 -255 -236 -447 -474 -557 -132 -62 -201 -76 -368 -76 -167 0 -236 14 -368 76 -213 98 -373 271 -451 485 -162 444 86 934 547 1084 153 49 292 57 452 25z m909 -232 c222 -123 408 -262 593 -441 76 -74 138 -139 138 -144 0 -16 -233 -242 -330 -319 -155 -123 -309 -223 -461 -299 l-81 -41 32 46 c18 26 49 83 70 128 143 306 141 649 -6 957 -25 52 -61 116 -79 142 l-34 47 45 -20 c26 -10 76 -36 113 -56z m-2057 25 c-40 -58 -105 -190 -130 -263 -110 -324 -59 -707 132 -981 25 -35 42 -64 37 -64 -19 0 -241 119 -326 174 -188 122 -406 314 -532 468 l-58 71 108 103 c185 178 428 349 672 473 66 33 121 60 123 61 2 0 -10 -19 -26 -42z\"\/><path d=\"M2375 1950 c-198 -44 -350 -190 -395 -379 -18 -76 -8 -221 19 -290 114 -284 457 -406 731 -260 98 52 188 154 231 260 27 69 37 214 19 290 -38 163 -166 304 -326 360 -67 23 -215 33 -279 19z\"\/><\/g><\/svg><\/i> <img data-recalc-dims=\"1\" loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"16\" height=\"16\" alt=\"Loading\" src=\"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/plugins\/page-views-count\/ajax-loader-2x.gif?resize=16%2C16&#038;ssl=1\" border=0 \/><\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>\u0198ungiyar Tunawa Da Mamman Shata (Mamman Shata Memorial Association) TARON FARKO Arewa House, Kaduna Asabar, 15 ga Yuni, 2013 JAWABI KAN MA\u0198ASUDIN KIRAN TARO DAGA MAI KIRAN TARO, MALAM IBRAHIM SHEME, Editan Jaridar Leadership Ina farawa da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin\u0199ai. Tsira da Amincin Allah su tabbata ga Annabin mu, fiyayyen talikai, Muhammad [&hellip;]<\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div>\n<p id=\"pvc_stats_5073\" class=\"pvc_stats total_only  \" data-element-id=\"5073\" style=\"\"><i class=\"pvc-stats-icon medium\" aria-hidden=\"true\"><svg xmlns=\"http:\/\/www.w3.org\/2000\/svg\" version=\"1.0\" viewBox=\"0 0 502 315\" preserveAspectRatio=\"xMidYMid meet\"><g transform=\"translate(0,332) scale(0.1,-0.1)\" fill=\"\" stroke=\"none\"><path d=\"M2394 3279 l-29 -30 -3 -207 c-2 -182 0 -211 15 -242 39 -76 157 -76 196 0 15 31 17 60 15 243 l-3 209 -33 29 c-26 23 -41 29 -80 29 -41 0 -53 -5 -78 -31z\"\/><path d=\"M3085 3251 c-45 -19 -58 -50 -96 -229 -47 -217 -49 -260 -13 -295 52 -53 146 -42 177 20 16 31 87 366 87 410 0 70 -86 122 -155 94z\"\/><path d=\"M1751 3234 c-13 -9 -29 -31 -37 -50 -12 -29 -10 -49 21 -204 19 -94 39 -189 45 -210 14 -50 54 -80 110 -80 34 0 48 6 76 34 21 21 34 44 34 59 0 14 -18 113 -40 219 -37 178 -43 195 -70 221 -36 32 -101 37 -139 11z\"\/><path d=\"M1163 3073 c-36 -7 -73 -59 -73 -102 0 -56 133 -378 171 -413 34 -32 83 -37 129 -13 70 36 67 87 -16 290 -86 209 -89 214 -129 231 -35 14 -42 15 -82 7z\"\/><path d=\"M3689 3066 c-15 -9 -33 -30 -42 -48 -48 -103 -147 -355 -147 -375 0 -98 131 -148 192 -74 13 15 57 108 97 206 80 196 84 226 37 273 -30 30 -99 39 -137 18z\"\/><path d=\"M583 2784 c-38 -19 -67 -74 -58 -113 9 -42 211 -354 242 -373 16 -10 45 -18 66 -18 51 0 107 52 107 100 0 39 -1 41 -124 234 -80 126 -108 162 -133 173 -41 17 -61 16 -100 -3z\"\/><path d=\"M4250 2784 c-14 -9 -74 -91 -133 -183 -95 -150 -107 -173 -107 -213 0 -55 33 -94 87 -104 67 -13 90 8 211 198 130 202 137 225 78 284 -27 27 -42 34 -72 34 -22 0 -50 -8 -64 -16z\"\/><path d=\"M2275 2693 c-553 -48 -1095 -270 -1585 -649 -135 -104 -459 -423 -483 -476 -23 -49 -22 -139 2 -186 73 -142 361 -457 571 -626 285 -228 642 -407 990 -497 242 -63 336 -73 660 -74 310 0 370 5 595 52 535 111 1045 392 1455 803 122 121 250 273 275 326 19 41 19 137 0 174 -41 79 -309 363 -465 492 -447 370 -946 591 -1479 653 -113 14 -422 18 -536 8z m395 -428 c171 -34 330 -124 456 -258 112 -119 167 -219 211 -378 27 -96 24 -300 -5 -401 -72 -255 -236 -447 -474 -557 -132 -62 -201 -76 -368 -76 -167 0 -236 14 -368 76 -213 98 -373 271 -451 485 -162 444 86 934 547 1084 153 49 292 57 452 25z m909 -232 c222 -123 408 -262 593 -441 76 -74 138 -139 138 -144 0 -16 -233 -242 -330 -319 -155 -123 -309 -223 -461 -299 l-81 -41 32 46 c18 26 49 83 70 128 143 306 141 649 -6 957 -25 52 -61 116 -79 142 l-34 47 45 -20 c26 -10 76 -36 113 -56z m-2057 25 c-40 -58 -105 -190 -130 -263 -110 -324 -59 -707 132 -981 25 -35 42 -64 37 -64 -19 0 -241 119 -326 174 -188 122 -406 314 -532 468 l-58 71 108 103 c185 178 428 349 672 473 66 33 121 60 123 61 2 0 -10 -19 -26 -42z\"\/><path d=\"M2375 1950 c-198 -44 -350 -190 -395 -379 -18 -76 -8 -221 19 -290 114 -284 457 -406 731 -260 98 52 188 154 231 260 27 69 37 214 19 290 -38 163 -166 304 -326 360 -67 23 -215 33 -279 19z\"\/><\/g><\/svg><\/i> <img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"16\" height=\"16\" alt=\"Loading\" src=\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/plugins\/page-views-count\/ajax-loader-2x.gif\" border=0 \/><\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div>\n","protected":false},"author":5,"featured_media":5109,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_FSMCFIC_featured_image_caption":"","_FSMCFIC_featured_image_nocaption":"","_FSMCFIC_featured_image_hide":"","_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[7],"tags":[349,348,347,66,19,346,350],"class_list":["post-5073","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-hausa","tag-aladu","tag-centre","tag-cibiya","tag-ibrahim-sheme","tag-mamman-shata","tag-tarihi","tag-waa"],"yoast_head":"<!-- This site is optimized with the Yoast SEO plugin v26.9 - https:\/\/yoast.com\/product\/yoast-seo-wordpress\/ -->\n<title>Bu\u0199atar Samun Cibiyar Wa\u0199o\u0199i ta Mamman Shata - Ibrahim Sheme<\/title>\n<meta name=\"robots\" content=\"index, follow, max-snippet:-1, max-image-preview:large, max-video-preview:-1\" \/>\n<link rel=\"canonical\" href=\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5073\" \/>\n<meta property=\"og:locale\" content=\"en_GB\" \/>\n<meta property=\"og:type\" content=\"article\" \/>\n<meta property=\"og:title\" content=\"Bu\u0199atar Samun Cibiyar Wa\u0199o\u0199i ta Mamman Shata - Ibrahim Sheme\" \/>\n<meta property=\"og:description\" content=\"\u0198ungiyar Tunawa Da Mamman Shata (Mamman Shata Memorial Association) TARON FARKO Arewa House, Kaduna Asabar, 15 ga Yuni, 2013 JAWABI KAN MA\u0198ASUDIN KIRAN TARO DAGA MAI KIRAN TARO, MALAM IBRAHIM SHEME, Editan Jaridar Leadership Ina farawa da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin\u0199ai. Tsira da Amincin Allah su tabbata ga Annabin mu, fiyayyen talikai, Muhammad [&hellip;]\" \/>\n<meta property=\"og:url\" content=\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5073\" \/>\n<meta property=\"og:site_name\" content=\"Ibrahim Sheme\" \/>\n<meta property=\"article:published_time\" content=\"2013-06-16T17:17:34+00:00\" \/>\n<meta property=\"article:modified_time\" content=\"2023-11-26T08:02:52+00:00\" \/>\n<meta property=\"og:image\" content=\"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2013\/06\/Cropped_Image_20231108_004649.jpg?fit=2048%2C1034&ssl=1\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:width\" content=\"2048\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:height\" content=\"1034\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:type\" content=\"image\/jpeg\" \/>\n<meta name=\"author\" content=\"Nafisat@ibrahimsheme.com\" \/>\n<meta name=\"twitter:card\" content=\"summary_large_image\" \/>\n<meta name=\"twitter:label1\" content=\"Written by\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data1\" content=\"IBRAHIM SHEME\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:label2\" content=\"Estimated reading time\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data2\" content=\"10 minutes\" \/>\n<script type=\"application\/ld+json\" class=\"yoast-schema-graph\">{\"@context\":\"https:\/\/schema.org\",\"@graph\":[{\"@type\":\"Article\",\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5073#article\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5073\"},\"author\":{\"name\":\"Nafisat@ibrahimsheme.com\",\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#\/schema\/person\/75c95be2f573872fa0335010b9a5e74f\"},\"headline\":\"Bu\u0199atar Samun Cibiyar Wa\u0199o\u0199i ta Mamman Shata\",\"datePublished\":\"2013-06-16T17:17:34+00:00\",\"dateModified\":\"2023-11-26T08:02:52+00:00\",\"mainEntityOfPage\":{\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5073\"},\"wordCount\":2051,\"commentCount\":0,\"publisher\":{\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#organization\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5073#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2013\/06\/Cropped_Image_20231108_004649.jpg?fit=2048%2C1034&ssl=1\",\"keywords\":[\"al'adu\",\"Centre\",\"cibiya\",\"Ibrahim Sheme\",\"mamman shata\",\"tarihi\",\"wa\u0199a\"],\"articleSection\":[\"Da Hausa\"],\"inLanguage\":\"en-GB\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"CommentAction\",\"name\":\"Comment\",\"target\":[\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5073#respond\"]}]},{\"@type\":\"WebPage\",\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5073\",\"url\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5073\",\"name\":\"Bu\u0199atar Samun Cibiyar Wa\u0199o\u0199i ta Mamman Shata - Ibrahim Sheme\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#website\"},\"primaryImageOfPage\":{\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5073#primaryimage\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5073#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2013\/06\/Cropped_Image_20231108_004649.jpg?fit=2048%2C1034&ssl=1\",\"datePublished\":\"2013-06-16T17:17:34+00:00\",\"dateModified\":\"2023-11-26T08:02:52+00:00\",\"breadcrumb\":{\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5073#breadcrumb\"},\"inLanguage\":\"en-GB\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"ReadAction\",\"target\":[\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5073\"]}]},{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-GB\",\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5073#primaryimage\",\"url\":\"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2013\/06\/Cropped_Image_20231108_004649.jpg?fit=2048%2C1034&ssl=1\",\"contentUrl\":\"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2013\/06\/Cropped_Image_20231108_004649.jpg?fit=2048%2C1034&ssl=1\",\"width\":2048,\"height\":1034,\"caption\":\"Wa\u0257ansu fayafayen garmaho na wa\u0199o\u0199in Shata\"},{\"@type\":\"BreadcrumbList\",\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5073#breadcrumb\",\"itemListElement\":[{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":1,\"name\":\"Home\",\"item\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/\"},{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":2,\"name\":\"Bu\u0199atar Samun Cibiyar Wa\u0199o\u0199i ta Mamman Shata\"}]},{\"@type\":\"WebSite\",\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#website\",\"url\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/\",\"name\":\"Ibrahim Sheme\",\"description\":\"\",\"publisher\":{\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#organization\"},\"potentialAction\":[{\"@type\":\"SearchAction\",\"target\":{\"@type\":\"EntryPoint\",\"urlTemplate\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?s={search_term_string}\"},\"query-input\":{\"@type\":\"PropertyValueSpecification\",\"valueRequired\":true,\"valueName\":\"search_term_string\"}}],\"inLanguage\":\"en-GB\"},{\"@type\":\"Organization\",\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#organization\",\"name\":\"Ibrahim Sheme\",\"url\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/\",\"logo\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-GB\",\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#\/schema\/logo\/image\/\",\"url\":\"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1\",\"contentUrl\":\"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1\",\"width\":512,\"height\":512,\"caption\":\"Ibrahim Sheme\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#\/schema\/logo\/image\/\"}},{\"@type\":\"Person\",\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#\/schema\/person\/75c95be2f573872fa0335010b9a5e74f\",\"name\":\"Nafisat@ibrahimsheme.com\",\"image\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-GB\",\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#\/schema\/person\/image\/\",\"url\":\"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/f15431c84219439c4441de28a5ea621c90236e7dc8a8934db0967eeaf5f7382a?s=96&d=mm&r=g\",\"contentUrl\":\"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/f15431c84219439c4441de28a5ea621c90236e7dc8a8934db0967eeaf5f7382a?s=96&d=mm&r=g\",\"caption\":\"Nafisat@ibrahimsheme.com\"},\"sameAs\":[\"https:\/\/ibrahimsheme.com\"],\"url\":\"\"}]}<\/script>\n<!-- \/ Yoast SEO plugin. -->","yoast_head_json":{"title":"Bu\u0199atar Samun Cibiyar Wa\u0199o\u0199i ta Mamman Shata - Ibrahim Sheme","robots":{"index":"index","follow":"follow","max-snippet":"max-snippet:-1","max-image-preview":"max-image-preview:large","max-video-preview":"max-video-preview:-1"},"canonical":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5073","og_locale":"en_GB","og_type":"article","og_title":"Bu\u0199atar Samun Cibiyar Wa\u0199o\u0199i ta Mamman Shata - Ibrahim Sheme","og_description":"\u0198ungiyar Tunawa Da Mamman Shata (Mamman Shata Memorial Association) TARON FARKO Arewa House, Kaduna Asabar, 15 ga Yuni, 2013 JAWABI KAN MA\u0198ASUDIN KIRAN TARO DAGA MAI KIRAN TARO, MALAM IBRAHIM SHEME, Editan Jaridar Leadership Ina farawa da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin\u0199ai. Tsira da Amincin Allah su tabbata ga Annabin mu, fiyayyen talikai, Muhammad [&hellip;]","og_url":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5073","og_site_name":"Ibrahim Sheme","article_published_time":"2013-06-16T17:17:34+00:00","article_modified_time":"2023-11-26T08:02:52+00:00","og_image":[{"width":2048,"height":1034,"url":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2013\/06\/Cropped_Image_20231108_004649.jpg?fit=2048%2C1034&ssl=1","type":"image\/jpeg"}],"author":"Nafisat@ibrahimsheme.com","twitter_card":"summary_large_image","twitter_misc":{"Written by":"IBRAHIM SHEME","Estimated reading time":"10 minutes"},"schema":{"@context":"https:\/\/schema.org","@graph":[{"@type":"Article","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5073#article","isPartOf":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5073"},"author":{"name":"Nafisat@ibrahimsheme.com","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#\/schema\/person\/75c95be2f573872fa0335010b9a5e74f"},"headline":"Bu\u0199atar Samun Cibiyar Wa\u0199o\u0199i ta Mamman Shata","datePublished":"2013-06-16T17:17:34+00:00","dateModified":"2023-11-26T08:02:52+00:00","mainEntityOfPage":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5073"},"wordCount":2051,"commentCount":0,"publisher":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#organization"},"image":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5073#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2013\/06\/Cropped_Image_20231108_004649.jpg?fit=2048%2C1034&ssl=1","keywords":["al'adu","Centre","cibiya","Ibrahim Sheme","mamman shata","tarihi","wa\u0199a"],"articleSection":["Da Hausa"],"inLanguage":"en-GB","potentialAction":[{"@type":"CommentAction","name":"Comment","target":["https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5073#respond"]}]},{"@type":"WebPage","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5073","url":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5073","name":"Bu\u0199atar Samun Cibiyar Wa\u0199o\u0199i ta Mamman Shata - Ibrahim Sheme","isPartOf":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#website"},"primaryImageOfPage":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5073#primaryimage"},"image":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5073#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2013\/06\/Cropped_Image_20231108_004649.jpg?fit=2048%2C1034&ssl=1","datePublished":"2013-06-16T17:17:34+00:00","dateModified":"2023-11-26T08:02:52+00:00","breadcrumb":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5073#breadcrumb"},"inLanguage":"en-GB","potentialAction":[{"@type":"ReadAction","target":["https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5073"]}]},{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-GB","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5073#primaryimage","url":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2013\/06\/Cropped_Image_20231108_004649.jpg?fit=2048%2C1034&ssl=1","contentUrl":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2013\/06\/Cropped_Image_20231108_004649.jpg?fit=2048%2C1034&ssl=1","width":2048,"height":1034,"caption":"Wa\u0257ansu fayafayen garmaho na wa\u0199o\u0199in Shata"},{"@type":"BreadcrumbList","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=5073#breadcrumb","itemListElement":[{"@type":"ListItem","position":1,"name":"Home","item":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/"},{"@type":"ListItem","position":2,"name":"Bu\u0199atar Samun Cibiyar Wa\u0199o\u0199i ta Mamman Shata"}]},{"@type":"WebSite","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#website","url":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/","name":"Ibrahim Sheme","description":"","publisher":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#organization"},"potentialAction":[{"@type":"SearchAction","target":{"@type":"EntryPoint","urlTemplate":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?s={search_term_string}"},"query-input":{"@type":"PropertyValueSpecification","valueRequired":true,"valueName":"search_term_string"}}],"inLanguage":"en-GB"},{"@type":"Organization","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#organization","name":"Ibrahim Sheme","url":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/","logo":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-GB","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#\/schema\/logo\/image\/","url":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1","contentUrl":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1","width":512,"height":512,"caption":"Ibrahim Sheme"},"image":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#\/schema\/logo\/image\/"}},{"@type":"Person","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#\/schema\/person\/75c95be2f573872fa0335010b9a5e74f","name":"Nafisat@ibrahimsheme.com","image":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-GB","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#\/schema\/person\/image\/","url":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/f15431c84219439c4441de28a5ea621c90236e7dc8a8934db0967eeaf5f7382a?s=96&d=mm&r=g","contentUrl":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/f15431c84219439c4441de28a5ea621c90236e7dc8a8934db0967eeaf5f7382a?s=96&d=mm&r=g","caption":"Nafisat@ibrahimsheme.com"},"sameAs":["https:\/\/ibrahimsheme.com"],"url":""}]}},"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2013\/06\/Cropped_Image_20231108_004649.jpg?fit=2048%2C1034&ssl=1","jetpack_likes_enabled":true,"jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/5073","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/5"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=5073"}],"version-history":[{"count":6,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/5073\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":5199,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/5073\/revisions\/5199"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/5109"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=5073"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=5073"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=5073"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}