{"id":4399,"date":"2007-05-12T19:36:11","date_gmt":"2007-05-12T19:36:11","guid":{"rendered":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=4399"},"modified":"2007-05-12T19:36:11","modified_gmt":"2007-05-12T19:36:11","slug":"mun-zama-shugabanni-a-shirin-fim","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=4399","title":{"rendered":"Mun zama shugabanni a shirin fim"},"content":{"rendered":"<p>Abin mamaki ba ya karewa. A yau da rana an zabe ni a matsayin Sakatare-Janar na Kungiyar Masu Shirya Finafinai ta Jihar Kaduna (Kaduna State Film Producers Association). Jiya Abdullahi Maikano Usman ya aiko mani da &#8216;text message&#8217; ya sanar da ni cewa za a yi zaben a Ma&#8217;aikatar Al&#8217;adun Gargajiya ta Jihar Kaduna a nan garin Kaduna, kuma ya ce ya kamata in je. Da ma ni memba ne a kungiyar (saboda finafinai na, wato &#8216;Gagarabadau&#8217;, &#8216;Daren Farko,&#8217; &#8216;Kash!&#8217; da kuma &#8216;Artabu&#8217;).<\/p>\n<p>Da zuwa na, sai aka bukaci masu takarar zama Sakatare su janye. Ana ganin cewa babu wanda ya cancanci wannan mukami a wurin, sai ni! Ni kuma ga ni da tsoron a ba ni mukami a kungiyar, domin na san matsalolin harkar fim na Hausa sarai, musamman ma a Kaduna. Mutane da yawa su ka taru su ka ce lallai ne sai in fito takara. Hasali ma dai an rufe karbar &#8216;yan takara tun tuni (kwanaki masu yawa) amma aka canza dokar saboda ni. To, ganin cewa mutane sun nuna mani goyon baya, sai na amince. Na ci zaben babu hamayya. Mutum 15 su ka zabe ni daga cikin mutum 15 da su ka jefa kuri&#8217;ar! Ba a yi wani &#8216;PDP&#8217; ba a wurin.<\/p>\n<p>Shugaban kungiyar a yanzu shi ne Yusuf Mohammed (mai &#8216;Al-Yusuffas Film Production&#8217;).<\/p>\n<p>Na gode Allah da ya ba ni wannan dama ta yi wa masu shirya fim aiki a Jihar Kaduna. To amma akwai jan aiki a gaban mu. Harkar fim ta durkushe. Mutane masu kallon fim sun dawo daga rakiyar &#8216;yan fim, su na ganin cewa duk finafinan shirme ake yi yanzu. Su kan su &#8216;yan fim din, ba su damu da samo mafita ba; sai gaba su ke yi a tsakanin su.<\/p>\n<p>Na dade ina kallon kai na a matsayin marubuci kuma dan jarida kawai, amma ba d&#8217;an fim ba duk da yake na shirya finafinai. To yanzu ni dan fim ne kenan? Bari za mu gani!<\/p>\n<p>Ina so in ga cewa na kawo shawara ga &#8216;yan kwamitin mu na shugabanni a kafa Hukumar Tace Finafinai a Jihar Kaduna (<em>Kaduna State Film Censorship Board<\/em>), irin ta Kano da Sakkwato. Za mu hada gwiwa da Gwamnatin Jihar Kaduna a karkashin sabon Gwamna, wato Alhaji Namadi Sambo, don ganin an kafa hukumar. Wannan zai taimaka wajen bunkasa harkar a nan jihar. Ba sai mutum ya je Kano ya yi kwana da kwanaki ba domin a tace masa fim. Ina ganin cewa idan har mu ka cimma wannan burin, to ai mun yi aiki ma.<\/p>\n<p>Haka kuma ya dace mu tinkari batun yanayin finafinan, wato jigon su, da kyan aiki, da tsarin su, da sauran su dai. Akwai kuma batun dabi&#8217;ar &#8216;yan fim, wadda mutanen gari ke kuka da ita, musamman idan an buga munanan labarai game da su a mujallun industiri. Shi ma kalubale ne babba.<\/p>\n<p>A gani na, shugabannin da aka zaba masu kishin harkar ne, kuma &#8216;ya&#8217;yan kungiyar su na girmama su. Idan mu ka yi amfani da wannan damar ta samun shugabanci, mu ka kama wasu daga cikin manyan matsalolin mu ka magance su, to alhamdu lillahi, kwalliya ta biya kudin sabulu.<\/p>\n<p>Allah ya ba mu sa&#8217;a, amin.<\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div>\n<p id=\"pvc_stats_4399\" class=\"pvc_stats total_only  \" data-element-id=\"4399\" style=\"\"><i class=\"pvc-stats-icon medium\" aria-hidden=\"true\"><svg xmlns=\"http:\/\/www.w3.org\/2000\/svg\" version=\"1.0\" viewBox=\"0 0 502 315\" preserveAspectRatio=\"xMidYMid meet\"><g transform=\"translate(0,332) scale(0.1,-0.1)\" fill=\"\" stroke=\"none\"><path d=\"M2394 3279 l-29 -30 -3 -207 c-2 -182 0 -211 15 -242 39 -76 157 -76 196 0 15 31 17 60 15 243 l-3 209 -33 29 c-26 23 -41 29 -80 29 -41 0 -53 -5 -78 -31z\"\/><path d=\"M3085 3251 c-45 -19 -58 -50 -96 -229 -47 -217 -49 -260 -13 -295 52 -53 146 -42 177 20 16 31 87 366 87 410 0 70 -86 122 -155 94z\"\/><path d=\"M1751 3234 c-13 -9 -29 -31 -37 -50 -12 -29 -10 -49 21 -204 19 -94 39 -189 45 -210 14 -50 54 -80 110 -80 34 0 48 6 76 34 21 21 34 44 34 59 0 14 -18 113 -40 219 -37 178 -43 195 -70 221 -36 32 -101 37 -139 11z\"\/><path d=\"M1163 3073 c-36 -7 -73 -59 -73 -102 0 -56 133 -378 171 -413 34 -32 83 -37 129 -13 70 36 67 87 -16 290 -86 209 -89 214 -129 231 -35 14 -42 15 -82 7z\"\/><path d=\"M3689 3066 c-15 -9 -33 -30 -42 -48 -48 -103 -147 -355 -147 -375 0 -98 131 -148 192 -74 13 15 57 108 97 206 80 196 84 226 37 273 -30 30 -99 39 -137 18z\"\/><path d=\"M583 2784 c-38 -19 -67 -74 -58 -113 9 -42 211 -354 242 -373 16 -10 45 -18 66 -18 51 0 107 52 107 100 0 39 -1 41 -124 234 -80 126 -108 162 -133 173 -41 17 -61 16 -100 -3z\"\/><path d=\"M4250 2784 c-14 -9 -74 -91 -133 -183 -95 -150 -107 -173 -107 -213 0 -55 33 -94 87 -104 67 -13 90 8 211 198 130 202 137 225 78 284 -27 27 -42 34 -72 34 -22 0 -50 -8 -64 -16z\"\/><path d=\"M2275 2693 c-553 -48 -1095 -270 -1585 -649 -135 -104 -459 -423 -483 -476 -23 -49 -22 -139 2 -186 73 -142 361 -457 571 -626 285 -228 642 -407 990 -497 242 -63 336 -73 660 -74 310 0 370 5 595 52 535 111 1045 392 1455 803 122 121 250 273 275 326 19 41 19 137 0 174 -41 79 -309 363 -465 492 -447 370 -946 591 -1479 653 -113 14 -422 18 -536 8z m395 -428 c171 -34 330 -124 456 -258 112 -119 167 -219 211 -378 27 -96 24 -300 -5 -401 -72 -255 -236 -447 -474 -557 -132 -62 -201 -76 -368 -76 -167 0 -236 14 -368 76 -213 98 -373 271 -451 485 -162 444 86 934 547 1084 153 49 292 57 452 25z m909 -232 c222 -123 408 -262 593 -441 76 -74 138 -139 138 -144 0 -16 -233 -242 -330 -319 -155 -123 -309 -223 -461 -299 l-81 -41 32 46 c18 26 49 83 70 128 143 306 141 649 -6 957 -25 52 -61 116 -79 142 l-34 47 45 -20 c26 -10 76 -36 113 -56z m-2057 25 c-40 -58 -105 -190 -130 -263 -110 -324 -59 -707 132 -981 25 -35 42 -64 37 -64 -19 0 -241 119 -326 174 -188 122 -406 314 -532 468 l-58 71 108 103 c185 178 428 349 672 473 66 33 121 60 123 61 2 0 -10 -19 -26 -42z\"\/><path d=\"M2375 1950 c-198 -44 -350 -190 -395 -379 -18 -76 -8 -221 19 -290 114 -284 457 -406 731 -260 98 52 188 154 231 260 27 69 37 214 19 290 -38 163 -166 304 -326 360 -67 23 -215 33 -279 19z\"\/><\/g><\/svg><\/i> <img data-recalc-dims=\"1\" loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"16\" height=\"16\" alt=\"Loading\" src=\"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/plugins\/page-views-count\/ajax-loader-2x.gif?resize=16%2C16&#038;ssl=1\" border=0 \/><\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Abin mamaki ba ya karewa. A yau da rana an zabe ni a matsayin Sakatare-Janar na Kungiyar Masu Shirya Finafinai ta Jihar Kaduna (Kaduna State Film Producers Association). Jiya Abdullahi Maikano Usman ya aiko mani da &#8216;text message&#8217; ya sanar da ni cewa za a yi zaben a Ma&#8217;aikatar Al&#8217;adun Gargajiya ta Jihar Kaduna a [&hellip;]<\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div>\n<p id=\"pvc_stats_4399\" class=\"pvc_stats total_only  \" data-element-id=\"4399\" style=\"\"><i class=\"pvc-stats-icon medium\" aria-hidden=\"true\"><svg xmlns=\"http:\/\/www.w3.org\/2000\/svg\" version=\"1.0\" viewBox=\"0 0 502 315\" preserveAspectRatio=\"xMidYMid meet\"><g transform=\"translate(0,332) scale(0.1,-0.1)\" fill=\"\" stroke=\"none\"><path d=\"M2394 3279 l-29 -30 -3 -207 c-2 -182 0 -211 15 -242 39 -76 157 -76 196 0 15 31 17 60 15 243 l-3 209 -33 29 c-26 23 -41 29 -80 29 -41 0 -53 -5 -78 -31z\"\/><path d=\"M3085 3251 c-45 -19 -58 -50 -96 -229 -47 -217 -49 -260 -13 -295 52 -53 146 -42 177 20 16 31 87 366 87 410 0 70 -86 122 -155 94z\"\/><path d=\"M1751 3234 c-13 -9 -29 -31 -37 -50 -12 -29 -10 -49 21 -204 19 -94 39 -189 45 -210 14 -50 54 -80 110 -80 34 0 48 6 76 34 21 21 34 44 34 59 0 14 -18 113 -40 219 -37 178 -43 195 -70 221 -36 32 -101 37 -139 11z\"\/><path d=\"M1163 3073 c-36 -7 -73 -59 -73 -102 0 -56 133 -378 171 -413 34 -32 83 -37 129 -13 70 36 67 87 -16 290 -86 209 -89 214 -129 231 -35 14 -42 15 -82 7z\"\/><path d=\"M3689 3066 c-15 -9 -33 -30 -42 -48 -48 -103 -147 -355 -147 -375 0 -98 131 -148 192 -74 13 15 57 108 97 206 80 196 84 226 37 273 -30 30 -99 39 -137 18z\"\/><path d=\"M583 2784 c-38 -19 -67 -74 -58 -113 9 -42 211 -354 242 -373 16 -10 45 -18 66 -18 51 0 107 52 107 100 0 39 -1 41 -124 234 -80 126 -108 162 -133 173 -41 17 -61 16 -100 -3z\"\/><path d=\"M4250 2784 c-14 -9 -74 -91 -133 -183 -95 -150 -107 -173 -107 -213 0 -55 33 -94 87 -104 67 -13 90 8 211 198 130 202 137 225 78 284 -27 27 -42 34 -72 34 -22 0 -50 -8 -64 -16z\"\/><path d=\"M2275 2693 c-553 -48 -1095 -270 -1585 -649 -135 -104 -459 -423 -483 -476 -23 -49 -22 -139 2 -186 73 -142 361 -457 571 -626 285 -228 642 -407 990 -497 242 -63 336 -73 660 -74 310 0 370 5 595 52 535 111 1045 392 1455 803 122 121 250 273 275 326 19 41 19 137 0 174 -41 79 -309 363 -465 492 -447 370 -946 591 -1479 653 -113 14 -422 18 -536 8z m395 -428 c171 -34 330 -124 456 -258 112 -119 167 -219 211 -378 27 -96 24 -300 -5 -401 -72 -255 -236 -447 -474 -557 -132 -62 -201 -76 -368 -76 -167 0 -236 14 -368 76 -213 98 -373 271 -451 485 -162 444 86 934 547 1084 153 49 292 57 452 25z m909 -232 c222 -123 408 -262 593 -441 76 -74 138 -139 138 -144 0 -16 -233 -242 -330 -319 -155 -123 -309 -223 -461 -299 l-81 -41 32 46 c18 26 49 83 70 128 143 306 141 649 -6 957 -25 52 -61 116 -79 142 l-34 47 45 -20 c26 -10 76 -36 113 -56z m-2057 25 c-40 -58 -105 -190 -130 -263 -110 -324 -59 -707 132 -981 25 -35 42 -64 37 -64 -19 0 -241 119 -326 174 -188 122 -406 314 -532 468 l-58 71 108 103 c185 178 428 349 672 473 66 33 121 60 123 61 2 0 -10 -19 -26 -42z\"\/><path d=\"M2375 1950 c-198 -44 -350 -190 -395 -379 -18 -76 -8 -221 19 -290 114 -284 457 -406 731 -260 98 52 188 154 231 260 27 69 37 214 19 290 -38 163 -166 304 -326 360 -67 23 -215 33 -279 19z\"\/><\/g><\/svg><\/i> <img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"16\" height=\"16\" alt=\"Loading\" src=\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/plugins\/page-views-count\/ajax-loader-2x.gif\" border=0 \/><\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div>\n","protected":false},"author":4,"featured_media":0,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_FSMCFIC_featured_image_caption":"","_FSMCFIC_featured_image_nocaption":"","_FSMCFIC_featured_image_hide":"","_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[7],"tags":[],"class_list":["post-4399","post","type-post","status-publish","format-standard","hentry","category-hausa"],"yoast_head":"<!-- This site is optimized with the Yoast SEO plugin v26.9 - https:\/\/yoast.com\/product\/yoast-seo-wordpress\/ -->\n<title>Mun zama shugabanni a shirin fim - Ibrahim Sheme<\/title>\n<meta name=\"robots\" content=\"index, follow, max-snippet:-1, max-image-preview:large, max-video-preview:-1\" \/>\n<link rel=\"canonical\" href=\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=4399\" \/>\n<meta property=\"og:locale\" content=\"en_GB\" \/>\n<meta property=\"og:type\" content=\"article\" \/>\n<meta property=\"og:title\" content=\"Mun zama shugabanni a shirin fim - Ibrahim Sheme\" \/>\n<meta property=\"og:description\" content=\"Abin mamaki ba ya karewa. A yau da rana an zabe ni a matsayin Sakatare-Janar na Kungiyar Masu Shirya Finafinai ta Jihar Kaduna (Kaduna State Film Producers Association). Jiya Abdullahi Maikano Usman ya aiko mani da &#8216;text message&#8217; ya sanar da ni cewa za a yi zaben a Ma&#8217;aikatar Al&#8217;adun Gargajiya ta Jihar Kaduna a [&hellip;]\" \/>\n<meta property=\"og:url\" content=\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=4399\" \/>\n<meta property=\"og:site_name\" content=\"Ibrahim Sheme\" \/>\n<meta property=\"article:published_time\" content=\"2007-05-12T19:36:11+00:00\" \/>\n<meta name=\"author\" content=\"Nafisat\" \/>\n<meta name=\"twitter:card\" content=\"summary_large_image\" \/>\n<meta name=\"twitter:label1\" content=\"Written by\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data1\" content=\"IBRAHIM SHEME\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:label2\" content=\"Estimated reading time\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data2\" content=\"3 minutes\" \/>\n<script type=\"application\/ld+json\" class=\"yoast-schema-graph\">{\"@context\":\"https:\/\/schema.org\",\"@graph\":[{\"@type\":\"Article\",\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=4399#article\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=4399\"},\"author\":{\"name\":\"Nafisat\",\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#\/schema\/person\/bb4e2be5e35db546de899bf1493897e4\"},\"headline\":\"Mun zama shugabanni a shirin fim\",\"datePublished\":\"2007-05-12T19:36:11+00:00\",\"mainEntityOfPage\":{\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=4399\"},\"wordCount\":539,\"commentCount\":0,\"publisher\":{\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#organization\"},\"articleSection\":[\"Da Hausa\"],\"inLanguage\":\"en-GB\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"CommentAction\",\"name\":\"Comment\",\"target\":[\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=4399#respond\"]}]},{\"@type\":\"WebPage\",\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=4399\",\"url\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=4399\",\"name\":\"Mun zama shugabanni a shirin fim - Ibrahim Sheme\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#website\"},\"datePublished\":\"2007-05-12T19:36:11+00:00\",\"breadcrumb\":{\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=4399#breadcrumb\"},\"inLanguage\":\"en-GB\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"ReadAction\",\"target\":[\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=4399\"]}]},{\"@type\":\"BreadcrumbList\",\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=4399#breadcrumb\",\"itemListElement\":[{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":1,\"name\":\"Home\",\"item\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/\"},{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":2,\"name\":\"Mun zama shugabanni a shirin fim\"}]},{\"@type\":\"WebSite\",\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#website\",\"url\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/\",\"name\":\"Ibrahim Sheme\",\"description\":\"\",\"publisher\":{\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#organization\"},\"potentialAction\":[{\"@type\":\"SearchAction\",\"target\":{\"@type\":\"EntryPoint\",\"urlTemplate\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?s={search_term_string}\"},\"query-input\":{\"@type\":\"PropertyValueSpecification\",\"valueRequired\":true,\"valueName\":\"search_term_string\"}}],\"inLanguage\":\"en-GB\"},{\"@type\":\"Organization\",\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#organization\",\"name\":\"Ibrahim Sheme\",\"url\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/\",\"logo\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-GB\",\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#\/schema\/logo\/image\/\",\"url\":\"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1\",\"contentUrl\":\"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1\",\"width\":512,\"height\":512,\"caption\":\"Ibrahim Sheme\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#\/schema\/logo\/image\/\"}},{\"@type\":\"Person\",\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#\/schema\/person\/bb4e2be5e35db546de899bf1493897e4\",\"name\":\"Nafisat\",\"image\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-GB\",\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#\/schema\/person\/image\/\",\"url\":\"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g\",\"contentUrl\":\"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g\",\"caption\":\"Nafisat\"},\"sameAs\":[\"https:\/\/ibrahimsheme.com\"],\"url\":\"\"}]}<\/script>\n<!-- \/ Yoast SEO plugin. -->","yoast_head_json":{"title":"Mun zama shugabanni a shirin fim - Ibrahim Sheme","robots":{"index":"index","follow":"follow","max-snippet":"max-snippet:-1","max-image-preview":"max-image-preview:large","max-video-preview":"max-video-preview:-1"},"canonical":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=4399","og_locale":"en_GB","og_type":"article","og_title":"Mun zama shugabanni a shirin fim - Ibrahim Sheme","og_description":"Abin mamaki ba ya karewa. A yau da rana an zabe ni a matsayin Sakatare-Janar na Kungiyar Masu Shirya Finafinai ta Jihar Kaduna (Kaduna State Film Producers Association). Jiya Abdullahi Maikano Usman ya aiko mani da &#8216;text message&#8217; ya sanar da ni cewa za a yi zaben a Ma&#8217;aikatar Al&#8217;adun Gargajiya ta Jihar Kaduna a [&hellip;]","og_url":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=4399","og_site_name":"Ibrahim Sheme","article_published_time":"2007-05-12T19:36:11+00:00","author":"Nafisat","twitter_card":"summary_large_image","twitter_misc":{"Written by":"IBRAHIM SHEME","Estimated reading time":"3 minutes"},"schema":{"@context":"https:\/\/schema.org","@graph":[{"@type":"Article","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=4399#article","isPartOf":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=4399"},"author":{"name":"Nafisat","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#\/schema\/person\/bb4e2be5e35db546de899bf1493897e4"},"headline":"Mun zama shugabanni a shirin fim","datePublished":"2007-05-12T19:36:11+00:00","mainEntityOfPage":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=4399"},"wordCount":539,"commentCount":0,"publisher":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#organization"},"articleSection":["Da Hausa"],"inLanguage":"en-GB","potentialAction":[{"@type":"CommentAction","name":"Comment","target":["https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=4399#respond"]}]},{"@type":"WebPage","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=4399","url":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=4399","name":"Mun zama shugabanni a shirin fim - Ibrahim Sheme","isPartOf":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#website"},"datePublished":"2007-05-12T19:36:11+00:00","breadcrumb":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=4399#breadcrumb"},"inLanguage":"en-GB","potentialAction":[{"@type":"ReadAction","target":["https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=4399"]}]},{"@type":"BreadcrumbList","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=4399#breadcrumb","itemListElement":[{"@type":"ListItem","position":1,"name":"Home","item":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/"},{"@type":"ListItem","position":2,"name":"Mun zama shugabanni a shirin fim"}]},{"@type":"WebSite","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#website","url":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/","name":"Ibrahim Sheme","description":"","publisher":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#organization"},"potentialAction":[{"@type":"SearchAction","target":{"@type":"EntryPoint","urlTemplate":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?s={search_term_string}"},"query-input":{"@type":"PropertyValueSpecification","valueRequired":true,"valueName":"search_term_string"}}],"inLanguage":"en-GB"},{"@type":"Organization","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#organization","name":"Ibrahim Sheme","url":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/","logo":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-GB","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#\/schema\/logo\/image\/","url":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1","contentUrl":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1","width":512,"height":512,"caption":"Ibrahim Sheme"},"image":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#\/schema\/logo\/image\/"}},{"@type":"Person","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#\/schema\/person\/bb4e2be5e35db546de899bf1493897e4","name":"Nafisat","image":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-GB","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#\/schema\/person\/image\/","url":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g","contentUrl":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g","caption":"Nafisat"},"sameAs":["https:\/\/ibrahimsheme.com"],"url":""}]}},"jetpack_featured_media_url":"","jetpack_likes_enabled":true,"jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4399","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/4"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=4399"}],"version-history":[{"count":0,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4399\/revisions"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=4399"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=4399"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=4399"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}