{"id":4129,"date":"2007-11-22T07:03:00","date_gmt":"2007-11-22T07:03:00","guid":{"rendered":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=4129"},"modified":"2023-11-25T07:59:20","modified_gmt":"2023-11-25T07:59:20","slug":"ci-gaban-adabin-hausa-ina-hausawan-ne","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=4129","title":{"rendered":"Cigaban Adabin Hausa: Ina Hausawan Ne?"},"content":{"rendered":"\r\n<figure id=\"attachment_4609\" aria-describedby=\"caption-attachment-4609\" style=\"width: 200px\" class=\"wp-caption alignnone\"><img data-recalc-dims=\"1\" loading=\"lazy\" decoding=\"async\" data-attachment-id=\"4609\" data-permalink=\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?attachment_id=4609\" data-orig-file=\"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2007\/11\/200809_KanoCensors_Edited.jpg?fit=200%2C133&amp;ssl=1\" data-orig-size=\"200,133\" data-comments-opened=\"1\" data-image-meta=\"{&quot;aperture&quot;:&quot;0&quot;,&quot;credit&quot;:&quot;&quot;,&quot;camera&quot;:&quot;&quot;,&quot;caption&quot;:&quot;&quot;,&quot;created_timestamp&quot;:&quot;0&quot;,&quot;copyright&quot;:&quot;&quot;,&quot;focal_length&quot;:&quot;0&quot;,&quot;iso&quot;:&quot;0&quot;,&quot;shutter_speed&quot;:&quot;0&quot;,&quot;title&quot;:&quot;&quot;,&quot;orientation&quot;:&quot;0&quot;}\" data-image-title=\"200809_KanoCensors_Edited\" data-image-description=\"\" data-image-caption=\"&lt;p&gt;Jami&amp;#8217;an gwamnatin Kano tare da Sarkin Kano Ado Bayero su na cinna wa tarin littattafan Hausa wuta (Hoto: Ado Ahmad Gidan Dabino)&lt;\/p&gt;\n\" data-medium-file=\"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2007\/11\/200809_KanoCensors_Edited.jpg?fit=200%2C133&amp;ssl=1\" data-large-file=\"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2007\/11\/200809_KanoCensors_Edited.jpg?fit=200%2C133&amp;ssl=1\" class=\"size-full wp-image-4609\" src=\"https:\/\/i0.wp.com\/wip.ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2007\/11\/200809_KanoCensors_Edited.jpg?resize=200%2C133&#038;ssl=1\" alt=\"\" width=\"200\" height=\"133\" \/><figcaption id=\"caption-attachment-4609\" class=\"wp-caption-text\"><em>Jami&#8217;an gwamnatin Kano tare da Sarkin Kano Ado Bayero su na cinna wa tarin littattafan Hausa wuta (Hoto: Ado Ahmad Gidan Dabino)<\/em><\/figcaption><\/figure>\r\n<p><span style=\"font-size: 16px;\">Kwanan nan aka yi wani \u0199asaitaccen biki na karrama marubutan Hausa uku wa\u0257anda su ka yi zarra a gasar rubuta littattafan hikaya na Hausa don tunawa da marigayi Injiniya Mohammed Bashir \u0198araye, wanda tsohon kwamishina ne a Jihar Kano. Mai\u0257akin marigayin, Hajiya Bilkisu Abdulmalik Bashir, wadda ita ce Sakataren Zartaswa ta Hukumar Aikin Shari\u2019a ta \u0198asa <\/span><em style=\"font-size: 16px;\">(Executive Secretary, National Judicial Service Council)<\/em><span style=\"font-size: 16px;\">, ita ce ta \u0257auki nauyin shirya gasar. \u0198ungiyar Marubuta ta Nijeriya (ANA), reshen Babban Birnin Tarayya, Abuja, ita ce ta gudanar da bikin. A tarihin adabin Hausa, ba a ta\u0253a yin gagarumin bikin karrama marubuta irin wannan ba. Taron da za a iya kwatanta shi da wannan shi ne wanda aka yi a kamfanin buga littattafai na <\/span><em style=\"font-size: 16px;\">Gaskiya Corporation<\/em><span style=\"font-size: 16px;\"> da ke Zariya lokacin da aka \u0199addamar da sabon bugu na wasu daga cikin littattafan Alhaji Abubakar Imam, cikin 1981, wanda ba a da\u0257e da yin taron ba Allah ya \u0257auki ran shi Alhaji Imam. To amma ko wancan taron na Zariya bai ko kama \u0199afar wannan ba wajen bun\u0199asa da alfarma. Abin sai wanda ya gani!<\/span><\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p>Wani abu da ya ba mutane da dama mamaki game da wannan gasa shi ne yanayin su wa\u0257anda su ka shirya gasar. Irin abin nan ne da ake cewa ana zaton wuta a ma\u0199era, sai ta tashi a masa\u0199a. Na farko, mutumin da ya fara kawo shawarar shirya gasar, ba Bahaushe ba ne. Inyamiri ne mai suna Mista Patrick Tagbo Ogujiofor. Ma\u2019aikaci ne a wannan hukuma ta aikin shari\u2019a, inda shi ne jami\u2019in ya\u0257a labarai. A bayanin da ya yi a jarida kwanan baya, Ogujiofor ya ce tunanin shirya gasar ya faru ne a bara, lokacin da su ka je ta\u2019aziyyar rasuwar Injiniya Bashir \u0198araye. A lokacin, uwar\u0257akin sa Hajiya Bilkisu ta \u0257an furta cewa mijin ta mai \u0199aunar karance-karancen littattafan Hausa ne da kuma son ha\u0253aka adabi. Wannan abu ne wanda kusan dukkan masu ruwa da tsaki a harkar adabin Hausa ba su sani ba, domin kuwa yawancin su ba su yi mu\u2019amala da shi Injiniyan ba.<\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p>To, inda kaya su ka tsinke a gindin kaba shi ne, shi Patrick wani \u0199usa ne a harkar rubuce-rubuce, amma fa da Turanci. Ya ta\u0253a ri\u0199e mu\u0199amin shugaban \u0199ungiyar ANA ta Jihar Yobe, lokacin ya na aiki a can. Mutum ne mai son al\u2019amuran Hausa, kuma ya na jin Hausa kamar jakin Kano. Kai, matar sa ma Bahaushiya ce!<\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p>Saboda haka sai ya ba Hajiya shawarar cewa ya kamata ta shirya wani abu wanda zai sa a ri\u0199a tunawa da marigayin. Nan take sai ta amince da hakan. Su ka tsara cewa a shirya gasar rubutu ga marubutan Hausa. Wani abu da zai ba ka mamaki kuma shi ne, ita kan ta Hajiya Bilkisun ba Bahaushiya ba ce. \u2019Yar \u0199abilar Igbirra ce daga Jihar Kogi. Amma wannan bai hana ta amincewa ta \u0257auki nauyin shirya gasar ba.<\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p>Patrick kuma memba ne a \u0199ungiyar ANA ta Abuja. Sai ya shigo da \u0199ungiyar cikin al\u2019amarin, inda shi da shugaban \u0199ungiyar, wato Dakta Emman Usman Shehu, su ka shiga fafutikar shirya gasar. Ina jin in ban da shi Emman Shehu da kuma wani lauya Bazazzagi, marubuci, mai suna Ahmed Maiwada, babu Bahaushe a \u0199ungiyar. Wa\u0257annan bayin Allah sun yi aiki tu\u0199uru wajen shirya wannan gasa har Allah ya sa aka yi ta aka gama lafiya.<\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p>Na ba ku wannan dogon tarihin ne don ku fahimci cewa ba Hausawa ka\u0257ai ba ne su ke da kishin cigaban adabin Hausa. Za ma mu iya cewa su Hausawan, musamman Musulmin cikin su, ba su damu sosai da cigaban al\u2019adun su ba; sau da yawa su kan bari wasu can su shirya musu hanyoyin ha\u0253aka al\u2019adun su, musamman a fannin rubutu.<\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p>Ga hujja. Gasar rubutu ta farko da aka shirya, a cikin 1933, wani Bature ne jigon yin ta. Baturen, Mista Rupert M. East, jami\u2019in ilmi ne a Zariya. Shi Turawan mulkin mallaka su ka \u0257ora a kan aikin. A wannan gasar ne aka samu marubuta zubin farko, irin su Abubakar Imam, Abubakar Tafawa-Balewa, Muhammadu Bello Kagara, Muhammadu Gwarzo da John Tafida Wusasa. Haka kuma gasar da aka yi a cikin 1982, Garba Asiwaju Malumfashi ne jagoran shirya ta. Bahaushe ne, to amma fa Kirista. Ya shirya gasar a matsayin sa na daraktan al\u2019adu a Ma\u2019aikatar Al\u2019adu ta Tarayya, ba domin addini ba, sai don ha\u0253aka adabin Hausa. A gasar ne aka samu marubuta irin su Sulaiman Ibrahim Katsina da Bature Gagare.<\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p>Ita kan ta wannan gasar da aka yi a bana, yawancin masu shirya ta ba Musulmi ba ne; ina nufin su Patrick, Emman Shehu da Ahmed Maiwada. Biyun \u0199arshe Hausawa ne, to amma ba Musulmi ba ne. Sun shirya gasar ne ba tare da sun sa tunanin addini a ran su ba, a\u2019a sai don su ga yadda za a yi a inganta adabin Hausa, tare da ma\u0199udan ku\u0257in da Hajiya Bilkisu ta bayar.<\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p>Shin ina Hausawa su ke? Ina Musulmi? Wa\u0257annan tambayoyin su na daga cikin wa\u0257anda ni da Farfesa Abdalla Uba Adamu, \u0257aya daga cikin al\u0199alan da su ka yi hukunci kan wannan gasa ta Injiniya Bashir \u0198araye, mu ka yi wa kan mu ita lokacin da shi Malam Abdalla ya zo Abuja don halartar taron karrama marubutan da su ka yi zarra a gasar. Gaskiyar magana ita ce Hausawa Musulmi ba su damu da ha\u0253aka al\u2019adun su ba, musamman ma dai a wannan zamanin. Ba su \u0257auki rubutu da wani muhimmanci ba.<\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p>Sau da yawa, Hausawa Musulmi so su ke a ma daina rubutun. Kamar yadda Hajiya Balaraba Ramat Yakubu, \u0257aya daga cikin zakarun gasar Injiniya \u0198araye, ta fa\u0257a a hirar ta da aka buga a jaridar Leadership Hausa a makon jiya, a Kano an da\u0257e ana \u0199o\u0199arin dur\u0199usar da rubutun hikaya na Hausa na wannan zamanin. An yi tsinuwa da zage-zage a masallatai; an ce marubuta ne manyan masu gur\u0253ata tarbiyya a \u0199asar Hausa. Kuma abin sai \u0199ara gur\u0253acewa ya ke yi. Misalin hakan shi ne yadda kwanan baya Hukumar A Daidaita Sahu ta Jihar Kano ta shirya gangamin \u0199ona littattafan Hausa, inda har Sarkin Kano sai da ya halarta kuma ya jagoranci cinna wa tarin littattafan wuta.<\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p>Kwanan nan kuma Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano ta fito da wata doka mai ban-dariya da takaici, inda ta ce tilas ne duk littafin da za a buga a Jihar Kano sai an kai mata shi ta karanta ta amince tukuna, bayan kuwa ga shi ba ta da masana masu lokacin yin wannan aiki. A kaikaice, manufar dokar ita ce ta hana yin rubutun kwata-kwata.<\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p>Wani abin juyayi shi ne yawancin masu sukar littattafan hikaya na Hausa ba masu karanta su ba ne. Ba su san abin da ke cikin littattafan ba. Su a \u0257an \u0199aramin tunanin su, babu abin da ke cikin littattafan sai labaran soyayya, sharholiya, batsa, zinace-zinace, shan muggan \u0199wayoyi, da sauran su. Kawai idan an samu littafi \u0199waya \u0257aya mai \u0257auke da wani abu wanda bai yi musu da\u0257i ba, ko wata she\u0257ara a cikin wani littafi, shi kenan an samu makamin farfaganda, a shiga kafafen ya\u0257a labarai ana kumfar baki. Ba za a fa\u0257i dalilin yin littafin da aka yi ba (misali, idan an ga batsa a wata she\u0257ara, a ce an yi ta ne don ta dace da muhallin ta). Kuma ba za a ta\u0253a yin nuni da duk wani littafi mai \u0257auke da irin koyarwar da su masu sukar su ke so a yi ba. Ba za su ba da misali da littattafan da su ka dace da tunanin su ba, a\u2019a sai dai wannan \u0199waya \u0257ayan. Ka ga kenan ana yin al\u0199alanci cikin jahilci. Hakika, na san wani al\u0199alancin ana yin sa ne da gangan don a shafa wa marubuta kashin kaji.<br \/>Sannan kuma su masu sukar, daga hukumomi zuwa \u0257ai\u0257aikun mutane, ba su yin komai don agaza wa marubutan. Ba su shirya taron wayar da kai, ba su yin wa\u2019azantarwa, ba su ba da tagomashi na ku\u0257i, ba su shirya gasar rubutu su gindaya \u0199a\u2019idojin da su ke so, kuma ba su sayen littattafan. Hukumar A Daidaita Sahu ta alamta yun\u0199urin agaza wa marubutan, to amma abin da ta yi kamar ka \u0257iga ruwa ne a hamadar rairayi. Wani rufin-\u0257uwan-\u2019yan bori (an rufe gaba, ba a rufe baya ba) kuma da hukumar ta yi shi ne gangamin \u0199ona littattafan marubuta da ta yi, wa\u0257anda kamata ya yi ta ja su a jika, ta saka su kan hanyar da ta ga ya dace.<\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p>Abin mamaki, akwai daga cikin masu nazari da marubuta wa\u0257anda ke yin furutan da ke \u0199ara iza wutar \u0199yama ga marubutan. A marubuta, akwai \u0199yashi da hassada da kuma tunanin in-ba-ni-ba-to-ba-wanda-ya-iya. Idan ka dubi surutan da ake yi wa juna a tsakanin \u0199ungiyoyin marubuta na Kano, to ka san lallai da sauran aiki.<\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p>Sannan manazarta\/masana irin su Malam Ibrahim Malumfashi (wanda ke kan hanyar zama cikakken farfesa a fagen adabi) sun yi ayyukan da ke tabbatar da cewa manufar su ba ta kawo gyara ba ce; kawai su na yin sukar neman suna ne, ba tare da sun kawo tabbatattun hujjoji na sukar da su ke yi ba. Haka kuma abin ba\u0199in ciki shi ne duk da yake wai a jami\u2019a su ke, su ma a tsakanin su akwai \u0199yashi da hassada irin ta malaman zaure. Babu shakka, Malumfashi shi ne kan gaba wajen \u0253ata sunan marubutan Hausa na wannan zamani; da gangan ya \u0199i yarda ya fito rana a gan shi, ya la\u0253e cikin duhun tarihi, ya na bautar shudaddun shu\u0257a\u0257\u0257un gumaka. Idan wani al\u2019amari ya taso na yadda za a yi a inganta adabin Hausa, to ba ya ciki.<\/p>\r\n\r\n\r\n\r\n<p>Babu wata \u0199asa mamallakiyar babban harshe da ya kai gawurtar harshen Hausa inda tsirarun manazarta da \u2019yan kazagin su masu \u0199aramin ilmi su ke farfagandar jawo koma-baya a fagen adabi kamar \u0199asar Hausa. Sai dai abin mamaki, da yake sukar adabi ba ta hana adabi ya\u0257o, har yanzu rubutun ake. Ya \u0199i mutuwa ballantana a yi jana\u2019izar sa. Masu jiran ganin kushewar sa sun ha\u0199a kabari mai zurfi, su na ri\u0199e da farin alawayyon yi masa likkafani, to amma akwai alamun cewa har su mutu shi adabin Hausar ba zai mutu ba. Wannan kabarin da su ka ha\u0199a, su za a rufe a ciki.<\/p>\r\n<p><em>(An buga wannan sharhin a filin Adabi na jaridar LEADERSHIP HAUSA ta ranar Juma&#8217;a ta makon jiya)<\/em><\/p>\r\n<p>&nbsp;<\/p>\r\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div><p id=\"pvc_stats_4129\" class=\"pvc_stats total_only  \" data-element-id=\"4129\" style=\"\"><i class=\"pvc-stats-icon medium\" aria-hidden=\"true\"><svg xmlns=\"http:\/\/www.w3.org\/2000\/svg\" version=\"1.0\" viewBox=\"0 0 502 315\" preserveAspectRatio=\"xMidYMid meet\"><g transform=\"translate(0,332) scale(0.1,-0.1)\" fill=\"\" stroke=\"none\"><path d=\"M2394 3279 l-29 -30 -3 -207 c-2 -182 0 -211 15 -242 39 -76 157 -76 196 0 15 31 17 60 15 243 l-3 209 -33 29 c-26 23 -41 29 -80 29 -41 0 -53 -5 -78 -31z\"\/><path d=\"M3085 3251 c-45 -19 -58 -50 -96 -229 -47 -217 -49 -260 -13 -295 52 -53 146 -42 177 20 16 31 87 366 87 410 0 70 -86 122 -155 94z\"\/><path d=\"M1751 3234 c-13 -9 -29 -31 -37 -50 -12 -29 -10 -49 21 -204 19 -94 39 -189 45 -210 14 -50 54 -80 110 -80 34 0 48 6 76 34 21 21 34 44 34 59 0 14 -18 113 -40 219 -37 178 -43 195 -70 221 -36 32 -101 37 -139 11z\"\/><path d=\"M1163 3073 c-36 -7 -73 -59 -73 -102 0 -56 133 -378 171 -413 34 -32 83 -37 129 -13 70 36 67 87 -16 290 -86 209 -89 214 -129 231 -35 14 -42 15 -82 7z\"\/><path d=\"M3689 3066 c-15 -9 -33 -30 -42 -48 -48 -103 -147 -355 -147 -375 0 -98 131 -148 192 -74 13 15 57 108 97 206 80 196 84 226 37 273 -30 30 -99 39 -137 18z\"\/><path d=\"M583 2784 c-38 -19 -67 -74 -58 -113 9 -42 211 -354 242 -373 16 -10 45 -18 66 -18 51 0 107 52 107 100 0 39 -1 41 -124 234 -80 126 -108 162 -133 173 -41 17 -61 16 -100 -3z\"\/><path d=\"M4250 2784 c-14 -9 -74 -91 -133 -183 -95 -150 -107 -173 -107 -213 0 -55 33 -94 87 -104 67 -13 90 8 211 198 130 202 137 225 78 284 -27 27 -42 34 -72 34 -22 0 -50 -8 -64 -16z\"\/><path d=\"M2275 2693 c-553 -48 -1095 -270 -1585 -649 -135 -104 -459 -423 -483 -476 -23 -49 -22 -139 2 -186 73 -142 361 -457 571 -626 285 -228 642 -407 990 -497 242 -63 336 -73 660 -74 310 0 370 5 595 52 535 111 1045 392 1455 803 122 121 250 273 275 326 19 41 19 137 0 174 -41 79 -309 363 -465 492 -447 370 -946 591 -1479 653 -113 14 -422 18 -536 8z m395 -428 c171 -34 330 -124 456 -258 112 -119 167 -219 211 -378 27 -96 24 -300 -5 -401 -72 -255 -236 -447 -474 -557 -132 -62 -201 -76 -368 -76 -167 0 -236 14 -368 76 -213 98 -373 271 -451 485 -162 444 86 934 547 1084 153 49 292 57 452 25z m909 -232 c222 -123 408 -262 593 -441 76 -74 138 -139 138 -144 0 -16 -233 -242 -330 -319 -155 -123 -309 -223 -461 -299 l-81 -41 32 46 c18 26 49 83 70 128 143 306 141 649 -6 957 -25 52 -61 116 -79 142 l-34 47 45 -20 c26 -10 76 -36 113 -56z m-2057 25 c-40 -58 -105 -190 -130 -263 -110 -324 -59 -707 132 -981 25 -35 42 -64 37 -64 -19 0 -241 119 -326 174 -188 122 -406 314 -532 468 l-58 71 108 103 c185 178 428 349 672 473 66 33 121 60 123 61 2 0 -10 -19 -26 -42z\"\/><path d=\"M2375 1950 c-198 -44 -350 -190 -395 -379 -18 -76 -8 -221 19 -290 114 -284 457 -406 731 -260 98 52 188 154 231 260 27 69 37 214 19 290 -38 163 -166 304 -326 360 -67 23 -215 33 -279 19z\"\/><\/g><\/svg><\/i> <img data-recalc-dims=\"1\" loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"16\" height=\"16\" alt=\"Loading\" src=\"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/plugins\/page-views-count\/ajax-loader-2x.gif?resize=16%2C16&#038;ssl=1\" border=0 \/><\/p><div class=\"pvc_clear\"><\/div>","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Kwanan nan aka yi wani \u0199asaitaccen biki na karrama marubutan Hausa uku wa\u0257anda su ka yi zarra a gasar rubuta littattafan hikaya na Hausa don tunawa da marigayi Injiniya Mohammed Bashir \u0198araye, wanda tsohon kwamishina ne a Jihar Kano. Mai\u0257akin marigayin, Hajiya Bilkisu Abdulmalik Bashir, wadda ita ce Sakataren Zartaswa ta Hukumar Aikin Shari\u2019a ta [&hellip;]<\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div>\n<p id=\"pvc_stats_4129\" class=\"pvc_stats total_only  \" data-element-id=\"4129\" style=\"\"><i class=\"pvc-stats-icon medium\" aria-hidden=\"true\"><svg xmlns=\"http:\/\/www.w3.org\/2000\/svg\" version=\"1.0\" viewBox=\"0 0 502 315\" preserveAspectRatio=\"xMidYMid meet\"><g transform=\"translate(0,332) scale(0.1,-0.1)\" fill=\"\" stroke=\"none\"><path d=\"M2394 3279 l-29 -30 -3 -207 c-2 -182 0 -211 15 -242 39 -76 157 -76 196 0 15 31 17 60 15 243 l-3 209 -33 29 c-26 23 -41 29 -80 29 -41 0 -53 -5 -78 -31z\"\/><path d=\"M3085 3251 c-45 -19 -58 -50 -96 -229 -47 -217 -49 -260 -13 -295 52 -53 146 -42 177 20 16 31 87 366 87 410 0 70 -86 122 -155 94z\"\/><path d=\"M1751 3234 c-13 -9 -29 -31 -37 -50 -12 -29 -10 -49 21 -204 19 -94 39 -189 45 -210 14 -50 54 -80 110 -80 34 0 48 6 76 34 21 21 34 44 34 59 0 14 -18 113 -40 219 -37 178 -43 195 -70 221 -36 32 -101 37 -139 11z\"\/><path d=\"M1163 3073 c-36 -7 -73 -59 -73 -102 0 -56 133 -378 171 -413 34 -32 83 -37 129 -13 70 36 67 87 -16 290 -86 209 -89 214 -129 231 -35 14 -42 15 -82 7z\"\/><path d=\"M3689 3066 c-15 -9 -33 -30 -42 -48 -48 -103 -147 -355 -147 -375 0 -98 131 -148 192 -74 13 15 57 108 97 206 80 196 84 226 37 273 -30 30 -99 39 -137 18z\"\/><path d=\"M583 2784 c-38 -19 -67 -74 -58 -113 9 -42 211 -354 242 -373 16 -10 45 -18 66 -18 51 0 107 52 107 100 0 39 -1 41 -124 234 -80 126 -108 162 -133 173 -41 17 -61 16 -100 -3z\"\/><path d=\"M4250 2784 c-14 -9 -74 -91 -133 -183 -95 -150 -107 -173 -107 -213 0 -55 33 -94 87 -104 67 -13 90 8 211 198 130 202 137 225 78 284 -27 27 -42 34 -72 34 -22 0 -50 -8 -64 -16z\"\/><path d=\"M2275 2693 c-553 -48 -1095 -270 -1585 -649 -135 -104 -459 -423 -483 -476 -23 -49 -22 -139 2 -186 73 -142 361 -457 571 -626 285 -228 642 -407 990 -497 242 -63 336 -73 660 -74 310 0 370 5 595 52 535 111 1045 392 1455 803 122 121 250 273 275 326 19 41 19 137 0 174 -41 79 -309 363 -465 492 -447 370 -946 591 -1479 653 -113 14 -422 18 -536 8z m395 -428 c171 -34 330 -124 456 -258 112 -119 167 -219 211 -378 27 -96 24 -300 -5 -401 -72 -255 -236 -447 -474 -557 -132 -62 -201 -76 -368 -76 -167 0 -236 14 -368 76 -213 98 -373 271 -451 485 -162 444 86 934 547 1084 153 49 292 57 452 25z m909 -232 c222 -123 408 -262 593 -441 76 -74 138 -139 138 -144 0 -16 -233 -242 -330 -319 -155 -123 -309 -223 -461 -299 l-81 -41 32 46 c18 26 49 83 70 128 143 306 141 649 -6 957 -25 52 -61 116 -79 142 l-34 47 45 -20 c26 -10 76 -36 113 -56z m-2057 25 c-40 -58 -105 -190 -130 -263 -110 -324 -59 -707 132 -981 25 -35 42 -64 37 -64 -19 0 -241 119 -326 174 -188 122 -406 314 -532 468 l-58 71 108 103 c185 178 428 349 672 473 66 33 121 60 123 61 2 0 -10 -19 -26 -42z\"\/><path d=\"M2375 1950 c-198 -44 -350 -190 -395 -379 -18 -76 -8 -221 19 -290 114 -284 457 -406 731 -260 98 52 188 154 231 260 27 69 37 214 19 290 -38 163 -166 304 -326 360 -67 23 -215 33 -279 19z\"\/><\/g><\/svg><\/i> <img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"16\" height=\"16\" alt=\"Loading\" src=\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/plugins\/page-views-count\/ajax-loader-2x.gif\" border=0 \/><\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div>\n","protected":false},"author":4,"featured_media":4609,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_FSMCFIC_featured_image_caption":"","_FSMCFIC_featured_image_nocaption":"","_FSMCFIC_featured_image_hide":"","_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[7],"tags":[],"class_list":["post-4129","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-hausa"],"yoast_head":"<!-- This site is optimized with the Yoast SEO plugin v26.9 - https:\/\/yoast.com\/product\/yoast-seo-wordpress\/ -->\n<title>Cigaban Adabin Hausa: Ina Hausawan Ne? - Ibrahim Sheme<\/title>\n<meta name=\"robots\" content=\"index, follow, max-snippet:-1, max-image-preview:large, max-video-preview:-1\" \/>\n<link rel=\"canonical\" href=\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=4129\" \/>\n<meta property=\"og:locale\" content=\"en_GB\" \/>\n<meta property=\"og:type\" content=\"article\" \/>\n<meta property=\"og:title\" content=\"Cigaban Adabin Hausa: Ina Hausawan Ne? - Ibrahim Sheme\" \/>\n<meta property=\"og:description\" content=\"Kwanan nan aka yi wani \u0199asaitaccen biki na karrama marubutan Hausa uku wa\u0257anda su ka yi zarra a gasar rubuta littattafan hikaya na Hausa don tunawa da marigayi Injiniya Mohammed Bashir \u0198araye, wanda tsohon kwamishina ne a Jihar Kano. Mai\u0257akin marigayin, Hajiya Bilkisu Abdulmalik Bashir, wadda ita ce Sakataren Zartaswa ta Hukumar Aikin Shari\u2019a ta [&hellip;]\" \/>\n<meta property=\"og:url\" content=\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=4129\" \/>\n<meta property=\"og:site_name\" content=\"Ibrahim Sheme\" \/>\n<meta property=\"article:published_time\" content=\"2007-11-22T07:03:00+00:00\" \/>\n<meta property=\"article:modified_time\" content=\"2023-11-25T07:59:20+00:00\" \/>\n<meta property=\"og:image\" content=\"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2007\/11\/200809_KanoCensors_Edited.jpg?fit=200%2C133&ssl=1\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:width\" content=\"200\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:height\" content=\"133\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:type\" content=\"image\/jpeg\" \/>\n<meta name=\"author\" content=\"Nafisat\" \/>\n<meta name=\"twitter:card\" content=\"summary_large_image\" \/>\n<meta name=\"twitter:label1\" content=\"Written by\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data1\" content=\"IBRAHIM SHEME\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:label2\" content=\"Estimated reading time\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data2\" content=\"9 minutes\" \/>\n<script type=\"application\/ld+json\" class=\"yoast-schema-graph\">{\"@context\":\"https:\/\/schema.org\",\"@graph\":[{\"@type\":\"Article\",\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=4129#article\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=4129\"},\"author\":{\"name\":\"Nafisat\",\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#\/schema\/person\/bb4e2be5e35db546de899bf1493897e4\"},\"headline\":\"Cigaban Adabin Hausa: Ina Hausawan Ne?\",\"datePublished\":\"2007-11-22T07:03:00+00:00\",\"dateModified\":\"2023-11-25T07:59:20+00:00\",\"mainEntityOfPage\":{\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=4129\"},\"wordCount\":1820,\"commentCount\":0,\"publisher\":{\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#organization\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=4129#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2007\/11\/200809_KanoCensors_Edited.jpg?fit=200%2C133&ssl=1\",\"articleSection\":[\"Da Hausa\"],\"inLanguage\":\"en-GB\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"CommentAction\",\"name\":\"Comment\",\"target\":[\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=4129#respond\"]}]},{\"@type\":\"WebPage\",\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=4129\",\"url\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=4129\",\"name\":\"Cigaban Adabin Hausa: Ina Hausawan Ne? - Ibrahim Sheme\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#website\"},\"primaryImageOfPage\":{\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=4129#primaryimage\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=4129#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2007\/11\/200809_KanoCensors_Edited.jpg?fit=200%2C133&ssl=1\",\"datePublished\":\"2007-11-22T07:03:00+00:00\",\"dateModified\":\"2023-11-25T07:59:20+00:00\",\"breadcrumb\":{\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=4129#breadcrumb\"},\"inLanguage\":\"en-GB\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"ReadAction\",\"target\":[\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=4129\"]}]},{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-GB\",\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=4129#primaryimage\",\"url\":\"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2007\/11\/200809_KanoCensors_Edited.jpg?fit=200%2C133&ssl=1\",\"contentUrl\":\"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2007\/11\/200809_KanoCensors_Edited.jpg?fit=200%2C133&ssl=1\",\"width\":200,\"height\":133,\"caption\":\"Jami'an gwamnatin Kano tare da Sarkin Kano Ado Bayero su na cinna wa tarin littattafan Hausa wuta (Hoto: Ado Ahmad Gidan Dabino)\"},{\"@type\":\"BreadcrumbList\",\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=4129#breadcrumb\",\"itemListElement\":[{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":1,\"name\":\"Home\",\"item\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/\"},{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":2,\"name\":\"Cigaban Adabin Hausa: Ina Hausawan Ne?\"}]},{\"@type\":\"WebSite\",\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#website\",\"url\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/\",\"name\":\"Ibrahim Sheme\",\"description\":\"\",\"publisher\":{\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#organization\"},\"potentialAction\":[{\"@type\":\"SearchAction\",\"target\":{\"@type\":\"EntryPoint\",\"urlTemplate\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?s={search_term_string}\"},\"query-input\":{\"@type\":\"PropertyValueSpecification\",\"valueRequired\":true,\"valueName\":\"search_term_string\"}}],\"inLanguage\":\"en-GB\"},{\"@type\":\"Organization\",\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#organization\",\"name\":\"Ibrahim Sheme\",\"url\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/\",\"logo\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-GB\",\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#\/schema\/logo\/image\/\",\"url\":\"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1\",\"contentUrl\":\"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1\",\"width\":512,\"height\":512,\"caption\":\"Ibrahim Sheme\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#\/schema\/logo\/image\/\"}},{\"@type\":\"Person\",\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#\/schema\/person\/bb4e2be5e35db546de899bf1493897e4\",\"name\":\"Nafisat\",\"image\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-GB\",\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#\/schema\/person\/image\/\",\"url\":\"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g\",\"contentUrl\":\"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g\",\"caption\":\"Nafisat\"},\"sameAs\":[\"https:\/\/ibrahimsheme.com\"],\"url\":\"\"}]}<\/script>\n<!-- \/ Yoast SEO plugin. -->","yoast_head_json":{"title":"Cigaban Adabin Hausa: Ina Hausawan Ne? - Ibrahim Sheme","robots":{"index":"index","follow":"follow","max-snippet":"max-snippet:-1","max-image-preview":"max-image-preview:large","max-video-preview":"max-video-preview:-1"},"canonical":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=4129","og_locale":"en_GB","og_type":"article","og_title":"Cigaban Adabin Hausa: Ina Hausawan Ne? - Ibrahim Sheme","og_description":"Kwanan nan aka yi wani \u0199asaitaccen biki na karrama marubutan Hausa uku wa\u0257anda su ka yi zarra a gasar rubuta littattafan hikaya na Hausa don tunawa da marigayi Injiniya Mohammed Bashir \u0198araye, wanda tsohon kwamishina ne a Jihar Kano. Mai\u0257akin marigayin, Hajiya Bilkisu Abdulmalik Bashir, wadda ita ce Sakataren Zartaswa ta Hukumar Aikin Shari\u2019a ta [&hellip;]","og_url":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=4129","og_site_name":"Ibrahim Sheme","article_published_time":"2007-11-22T07:03:00+00:00","article_modified_time":"2023-11-25T07:59:20+00:00","og_image":[{"width":200,"height":133,"url":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2007\/11\/200809_KanoCensors_Edited.jpg?fit=200%2C133&ssl=1","type":"image\/jpeg"}],"author":"Nafisat","twitter_card":"summary_large_image","twitter_misc":{"Written by":"IBRAHIM SHEME","Estimated reading time":"9 minutes"},"schema":{"@context":"https:\/\/schema.org","@graph":[{"@type":"Article","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=4129#article","isPartOf":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=4129"},"author":{"name":"Nafisat","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#\/schema\/person\/bb4e2be5e35db546de899bf1493897e4"},"headline":"Cigaban Adabin Hausa: Ina Hausawan Ne?","datePublished":"2007-11-22T07:03:00+00:00","dateModified":"2023-11-25T07:59:20+00:00","mainEntityOfPage":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=4129"},"wordCount":1820,"commentCount":0,"publisher":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#organization"},"image":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=4129#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2007\/11\/200809_KanoCensors_Edited.jpg?fit=200%2C133&ssl=1","articleSection":["Da Hausa"],"inLanguage":"en-GB","potentialAction":[{"@type":"CommentAction","name":"Comment","target":["https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=4129#respond"]}]},{"@type":"WebPage","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=4129","url":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=4129","name":"Cigaban Adabin Hausa: Ina Hausawan Ne? - Ibrahim Sheme","isPartOf":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#website"},"primaryImageOfPage":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=4129#primaryimage"},"image":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=4129#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2007\/11\/200809_KanoCensors_Edited.jpg?fit=200%2C133&ssl=1","datePublished":"2007-11-22T07:03:00+00:00","dateModified":"2023-11-25T07:59:20+00:00","breadcrumb":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=4129#breadcrumb"},"inLanguage":"en-GB","potentialAction":[{"@type":"ReadAction","target":["https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=4129"]}]},{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-GB","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=4129#primaryimage","url":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2007\/11\/200809_KanoCensors_Edited.jpg?fit=200%2C133&ssl=1","contentUrl":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2007\/11\/200809_KanoCensors_Edited.jpg?fit=200%2C133&ssl=1","width":200,"height":133,"caption":"Jami'an gwamnatin Kano tare da Sarkin Kano Ado Bayero su na cinna wa tarin littattafan Hausa wuta (Hoto: Ado Ahmad Gidan Dabino)"},{"@type":"BreadcrumbList","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=4129#breadcrumb","itemListElement":[{"@type":"ListItem","position":1,"name":"Home","item":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/"},{"@type":"ListItem","position":2,"name":"Cigaban Adabin Hausa: Ina Hausawan Ne?"}]},{"@type":"WebSite","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#website","url":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/","name":"Ibrahim Sheme","description":"","publisher":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#organization"},"potentialAction":[{"@type":"SearchAction","target":{"@type":"EntryPoint","urlTemplate":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?s={search_term_string}"},"query-input":{"@type":"PropertyValueSpecification","valueRequired":true,"valueName":"search_term_string"}}],"inLanguage":"en-GB"},{"@type":"Organization","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#organization","name":"Ibrahim Sheme","url":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/","logo":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-GB","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#\/schema\/logo\/image\/","url":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1","contentUrl":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1","width":512,"height":512,"caption":"Ibrahim Sheme"},"image":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#\/schema\/logo\/image\/"}},{"@type":"Person","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#\/schema\/person\/bb4e2be5e35db546de899bf1493897e4","name":"Nafisat","image":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-GB","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#\/schema\/person\/image\/","url":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g","contentUrl":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g","caption":"Nafisat"},"sameAs":["https:\/\/ibrahimsheme.com"],"url":""}]}},"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2007\/11\/200809_KanoCensors_Edited.jpg?fit=200%2C133&ssl=1","jetpack_likes_enabled":true,"jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4129","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/4"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=4129"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4129\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":5188,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/4129\/revisions\/5188"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/4609"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=4129"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=4129"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=4129"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}