{"id":3060,"date":"2020-12-23T19:50:08","date_gmt":"2020-12-23T19:50:08","guid":{"rendered":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=3060"},"modified":"2024-04-23T08:00:51","modified_gmt":"2024-04-23T08:00:51","slug":"tunawa-da-shehu-maigidaje-funtuwa-bayan-shekara-20","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=3060","title":{"rendered":"Tunawa da Shehu Maigidaje Funtuwa bayan shekara 20"},"content":{"rendered":"<em><span style=\"font-size: 16px;\">\u201cShi Shehu Maigidaje kamar Bahillace can daji,<\/span><\/em>\r\n\r\n<em>A wurin kiwon shanu nai,<\/em>\r\n\r\n<em>In ya koro za su yi \u0253arna,<\/em>\r\n\r\n<em>Sai ka ga matar shi na tare mai.<\/em>\r\n\r\n<em>\u2013<\/em>\r\n\r\n<em>To haka nan Shehu Maigidaje,<\/em>\r\n\r\n<em>In ya \u0257auko wa\u0199a tai a rubuce,<\/em>\r\n\r\n<em>Sai ka ga matash shi na taya shi.\u201d<\/em>\r\n\r\n\u2013 Shata a wa\u0199ar \u2018Na Gode Shehu Maigidaje\u2019\r\n\r\n&nbsp;\r\n\r\nA YAU Laraba, 23 ga Disamba, 2020 ne Alhaji Shehu Maigidaje Funtuwa ya cika shekara ashirin cur da rasuwa. Mutane sun fi saurin tunawa da Alhaji Shehu ne saboda wa\u0199ar da Alhaji Mamman Shata ya yi masa mai taken \u2018Na Gode Shehu Maigidaje,\u2019 amma ni na fi saurin tunawa da mu\u2019amalar da muka yi ni da shi daga farkon shekarun 1990 har zuwa \u0199arshen rayuwar sa.\r\n\r\nIdan na waiga, sai in ga ba ma wata da\u0257ewa muka yi ba a mu\u2019amalar mu, domin kuwa mun fara ha\u0257uwa a cikin 1992, muka rabu bayan shekara takwas, to amma irin zumunci da muka yi sai in ga kamar mun shekara ashirin tare. Mun ha\u0257u a lokacin da na fara fafutikar tattara tarihin rayuwar Alhaji Mamman Shata, a gidan Shatan a Funtuwa. Na je ne domin in ga mawa\u0199in kamar yadda nakan yi jefi-jefi, shi kuma ya je wajen Shatan kamar yadda ya saba yi, sai Alhaji Ya\u2019u Wazirin Shata ya gabatar da mu ga juna.\r\n\r\nDa na ji cewa shi ne wanda Shata ya wa\u0199e \u0257in nan, shi kuma da ya ji ni \u0257an jarida ne \u2013 kuma wanda Shata ya amince mawa ya rubuta tarihin sa \u2013 shi kenan, sai muka \u0257inke. Ya \u0257auke ni a motar sa, zuwa gidan sa a nan cikin Funtuwa, ya kai ni har cikin gida ya gabatar da ni ga iyalin sa. Bayan mun ci abinci mun sha labari, sai ya kai ni tasha, ya sanya ni a mota, na koma Kaduna. A lokacin ina aiki a matsayin Mataimakin Editan jaridar Nasiha (wadda kamfanin jaridar The Reporter ta Janar Shehu Musa Yar\u2019Adua ke bugawa).\r\n\r\nDa farko dai, ni ba tsaran Alhaji Shehu ba ne, amma ya \u0257auke ni a matsayin amini, abokin sirrin sa. Ya sha ba ni labaran da na fi so in ji, wato game da Shata. Ban da aikin Nasiha da na yi, daga baya na zama Editan mujallar mako biyu-biyu mai suna Rana (wadda kamfanin mujallar Hotline ke bugawa). Ya zuwa lokacin, na fahimci cewa Alhaji Shehu hazi\u0199i ne, domin kuwa marubucin wa\u0199o\u0199in Hausa ne, har ana sako wa\u0199o\u0199in sa a Rediyon Nijeriya na Kaduna. Hasali ma dai, shi ne jami\u2019in ya\u0257a labarai na \u0199ungiyar sha\u2019irai ta \u0199asa wadda ta \u0199unshi shahararrun mawa\u0199a irin su Malam Mudi Sipikin, Malam A\u0199ilu Aliyu, Alhaji Baba Maigya\u0257a Agege, Alhaji Garba ABCD Funtuwa, Malam Salihu Kwantagora, da sauran su da dama.\r\n\r\nAkwai wata hira mai tsawo da na ta\u0253a yi da shi, aka buga ta a cikin mujallar Rana, wadda ta \u0199unshi tarihin rayuwar sa, da batun wa\u0199ar da Shata ya yi masa, da batun nasa wa\u0199o\u0199in. Duk wanda ya karanta hirar, zai \u0199ara fahimtar wanene Maigidaje, musamman ra\u2019ayoyin sa game da rayuwa.\r\n\r\nMaigidaje mutum ne wanda ya iya hul\u0257a da jama\u2019a. Mutum ne mai haba-haba da kowa, mai barkwanci, kuma mai zumunci.\r\n\r\nYa kamata a sani cewa a da shi ne shugaban \u0199ungiyar matasa ta tsohuwar \u0198aramar Hukumar Funtuwa (tun tana ha\u0257e da su Bakori, \u018aandume, Faskari da Sabuwa). Da\u0257a\u0257\u0257iyar \u0199ungiya ce mai manufar kawo cigaba tare da ha\u0257in kai tsakanin al\u2019ummar Funtuwa da kewaye.\r\n\r\nWani abu kuma shi ne yawancin ma\u2019aikatan rediyo da ke zuwa Funtuwa domin su yi hira da Shata ko su \u0257auki wa\u0199o\u0199in sa, wato irin su marigayi Khalifa Baba-Ahmed, marigayi Yaya Abubakar, su Halilu Ahmed Getso, to Shehu Maigidaje ne mai masaukin su, kuma shi ne zai yi jagora a je wajen Shata a tara masa \u0199asa har ya amince a je inda za a \u0257auki wa\u0199o\u0199in, a \u0257auka.\r\n\r\nDuk wannan mu\u2019amala ta sa Shata ya \u0257auki Maigidaje kamar \u0257an sa, domin a cikin gidan mawa\u0199in babu inda ba ya shiga. Haka kuma da yake ya iya karatu da rubutu (ta hanyar ya\u0199i da jahilci), Shata kan kira shi ya rubuta masa wasi\u0199a, ko ya aike shi wani waje ya kai masa sa\u0199o.\r\n\r\nA dalilin kasancewar Maigidaje jagora a \u0199ungiyar matasan Funtuwa ne Shata ya yi masa wa\u0199a. Yadda abin ya faru shi ne da ma can \u0199ungiyar kan ro\u0199i Shata ya yi mata wasa a gidan wasa domin ta samu ku\u0257in shiga. Alhaji Shehu ne ke jagorantar zuwa gayyato shi har gida. Idan sun je, Shata ba ya \u0199in zuwa; yakan ce, \u201cTo ai ku \u2018ya\u2019ya na ne.\u201d\r\n\r\nWata rana a cikin 1972, ana irin wasannin nan na \u0199ungiya a Funtuwa, Shata na wa\u0199a, Shehu kuma na ta giggilmiyawa a matsayin shugaba, an \u0257an tsaya ana hutawa, can da maro\u0199in Shata, Alhaji Lawal Tsangaya, ya ga Maigidaje ya gitta, sai ya ce, \u201cAlhaji Shehu mun gode da alherin da kake yi mana ba sai ka ga idon Shata ba. Idan ya yi tafiya ba ya Funtuwa, kai ke ri\u0199e da mu!\u201d\r\n\r\nShata ya yi kamar bai ji ba. Can da zai koma wa\u0199a, yana ri\u0199e da makirfo, sai aka ji ya ce, \u201cNa gode Shehu Maigidaje!\u201d\r\n\r\nShi kenan, \u2018yan amshi suka kar\u0253e, \u2018yan kallo kuma sai sowa da tafi raf-raf-raf! Asalin wa\u0199ar \u2018Na Gode Shehu Maigidaje\u2019 kenan. \u0198waya \u0257aya ce rak ya yi masa, sai dai maimaici idan an je wani wurin; wato ta kasance irin wa\u0199o\u0199in da Shata ya yi wa wasu mutanen masu wa\u0199a \u0257aya kacal amma kar\u0253a\u0253\u0253iya ga jama\u2019a, irin su: \u2018Na Gode Goshi Ta \u018aangude\u2019, \u2018\u0198usoshin Birni Uwawu\u2019, \u2018Malam Mu\u0257\u0257aha \u018aanraka\u2019, \u2018Habu Na Habu\u2019, \u2018Alhaji Sani Zangon Daura\u2019, \u2018Magaji Mai Ido \u018aaya\u2019, \u2018Bahillace Ja\u2019e \u018aan Ali\u2019, \u2018Wamban Kano Habu \u018aan Maje\u2019, \u2018Na Gode Sarkin Fada Alex\u2019, wa\u0199ar Indon Musawa da ta Kyauta Uwar Gajeje, da sauran su.\r\n\r\nWannan wa\u0199a ta yi farin jini matu\u0199a. Ta fito da ainihin wanene Shehu Maigidaje, musamman fi\u0199irar sa da zumuncin sa da tawakkalin sa da tawali\u2019un sa da dangantakar sa da iyalin sa. A cikin ta, Shata ya kwatanta kan sa da Shehu a fagen wa\u0199a, amma fa kowanne akwai nasa fagen \u2013 wannan a fagen ki\u0257a da wa\u0199a, wannan kuma a filin rubutun wa\u0199a \u2013 ya nuna kowa gwani ne a inda Allah ya aje shi.\r\n\r\nWa\u0199ar ta yi wa Maigidaje alfanu matu\u0199a. Kamar yadda ya fa\u0257a mani, ko taron suna ko \u0257aurin aure ya je, aka ce Shehu Maigidaje ya zo, to mutane na so su gan shi ba domin saboda wa\u0199o\u0199in sa da ake sakawa a rediyo ba (wa\u0257anda sun girmi wadda Shata ya yi masa), a\u2019a, sai saboda \u201cwannan wanda Shata ya wa\u0199e ne\u201d! Ya ce \u2018yan sanda ma sun ta\u0253a tare shi domin bincikar takardun mota, amma suna ganin an rubuta \u2018Maigidaje\u2019 sai suka ce, \u201cKo kai ne Shata ya yi wa wa\u0199a?\u201d Da ya ce shi ne, sai abin ya koma na raha. Kai, ba ma shi Alhaji Shehu da ya mutu yau shekara 20 ba, hatta iyalin sa duk inda suka shiga aka ji inkiyar sunan su, za a ce ai \u2018ya\u2019yan wanda Shata ya yi wa wa\u0199a \u0257in nan ne.\r\n\r\nWannan ya yi daidai da fa\u0257ar da maro\u0199i Tsangaya ya yi a kirarin Shata, wato da ya ce duk wanda Shata ya yi wa wa\u0199a ba ya ta\u0253ewa har abada. Manufa dai, sunan sa ba zai gushe ba, kuma duk inda ya shiga sai ya ga haske saboda tauraron sa da wa\u0199ar Shata ta haskake.\r\n\r\nWani abu game da Maigidaje shi ne, ban da harkar kasuwanci da yake yi, kamar dillancin gidaje da saye da sayarwa, babban \u0257an siyasa ne. Mu\u2019amalar sa da mutane ta ce ta sa tilas ya zama \u0257an siyasa. A lokacin da muke abota ne aka na\u0257a shi Daraktan Ya\u0257a Labarai na rundunar ya\u0199in neman za\u0253en Alhaji Mahmuda Waziri a matsayin shugaban \u0199asa. Hakan ya \u0199ara kusanta shi da jama\u2019a.\r\n\r\nNa kan yi mamakin yadda a duk lokacin da ya shiga garin Kaduna sai ya je waje na, ko a gida ko ofis, mun gana. Kuma yakan so in raka shi wurare, mu je nan mu je can a motar sa. Ta dalilin sa na san wasu garuruwa da dama na \u0199asar Katsina, irin su Bindawa da Mani da Mashi. Ta dalilin sa na ta\u0253a zuwa gaban Sarkin Daura Alhaji Muhammadu Bashar, muka yi gaisuwa. Ta dalilin sa na san hakimai irin su Alhaji Tukur Nadabo, Hakimin Bakori, har na yi hira da shi kan wa\u0199o\u0199in da Shata ya yi masa da mahaifin sa.\r\n\r\nAkwai wasu abubuwan ma wa\u0257anda ke alamta kusanci na da Maigidaje. Misali, lokacin da na yi auren fari, Alhaji Shehu ne ya \u0257auko amaryar tawa tare da \u0199awayen ta daga gidan su a motar sa, ya kai ta gida na. Wani misalin shi ne lokacin da zan tafi \u0199aro karatu a Birtaniya a cikin 1993, Shehu Maigidaje ya bugo mota da sassafe daga Funtuwa, ya zo Kaduna ya \u0257auke ni ya kai ni Kano, inda na hau jirgin sama. Haka kuma lokacin da na gama karatu na na digiri na biyu a Birtaniya, Alhaji Shehu ne ya tafi Kano daga Funtuwa shi ka\u0257ai, ya tarbe ni a filin jirgin sama, ya \u0257auko ni zuwa gida Kaduna.\r\n\r\nIrin wa\u0257annan misalan suna da yawa, na dai ta\u0199aita ne. Na \u0199arshen wanda ba zan tsallake ba shi ne wani yun\u0199uri da muka ta\u0253a yi, ni da Maigidaje, na sasanta Shata da wata matar sa da suka da\u0257e da rabuwa, wadda kuma Shatan ke so kamar me. Yun\u0199urin dai ya ci tura, amma ya nuna irin kusanci na ni da Maigidaje da kuma wanda muke da shi da Alhaji Shata.\r\n\r\nAlhaji Shehu ya rasu ne a Funtuwa a ranar Asabar, 23 ga Disamba, 2000 bayan ya yi rashin lafiya, yana da shekaru 51 kacal a duniya. Ba wani tsufa ya yi ba, amma ya shuka alheri mai yawa.\r\n\r\nA duk lokacin da na tuno da shi, sai na tuno da wani bashi da yake bi na, wato na in taimaka in buga masa littafin rubutattun wa\u0199o\u0199in sa. A kullum ina addu\u2019ar Allah ya ba ni damar ida nufi, shi kuma ina masa addu\u2019ar Allah ya rahamshe shi, ya sa mutuwar sa hutu ce, kuma ya albarkaci abin da ya bari, amin.\r\n\r\n<!-- \/wp:post-content --><div class=\"pvc_clear\"><\/div><p id=\"pvc_stats_3060\" class=\"pvc_stats total_only  \" data-element-id=\"3060\" style=\"\"><i class=\"pvc-stats-icon medium\" aria-hidden=\"true\"><svg xmlns=\"http:\/\/www.w3.org\/2000\/svg\" version=\"1.0\" viewBox=\"0 0 502 315\" preserveAspectRatio=\"xMidYMid meet\"><g transform=\"translate(0,332) scale(0.1,-0.1)\" fill=\"\" stroke=\"none\"><path d=\"M2394 3279 l-29 -30 -3 -207 c-2 -182 0 -211 15 -242 39 -76 157 -76 196 0 15 31 17 60 15 243 l-3 209 -33 29 c-26 23 -41 29 -80 29 -41 0 -53 -5 -78 -31z\"\/><path d=\"M3085 3251 c-45 -19 -58 -50 -96 -229 -47 -217 -49 -260 -13 -295 52 -53 146 -42 177 20 16 31 87 366 87 410 0 70 -86 122 -155 94z\"\/><path d=\"M1751 3234 c-13 -9 -29 -31 -37 -50 -12 -29 -10 -49 21 -204 19 -94 39 -189 45 -210 14 -50 54 -80 110 -80 34 0 48 6 76 34 21 21 34 44 34 59 0 14 -18 113 -40 219 -37 178 -43 195 -70 221 -36 32 -101 37 -139 11z\"\/><path d=\"M1163 3073 c-36 -7 -73 -59 -73 -102 0 -56 133 -378 171 -413 34 -32 83 -37 129 -13 70 36 67 87 -16 290 -86 209 -89 214 -129 231 -35 14 -42 15 -82 7z\"\/><path d=\"M3689 3066 c-15 -9 -33 -30 -42 -48 -48 -103 -147 -355 -147 -375 0 -98 131 -148 192 -74 13 15 57 108 97 206 80 196 84 226 37 273 -30 30 -99 39 -137 18z\"\/><path d=\"M583 2784 c-38 -19 -67 -74 -58 -113 9 -42 211 -354 242 -373 16 -10 45 -18 66 -18 51 0 107 52 107 100 0 39 -1 41 -124 234 -80 126 -108 162 -133 173 -41 17 -61 16 -100 -3z\"\/><path d=\"M4250 2784 c-14 -9 -74 -91 -133 -183 -95 -150 -107 -173 -107 -213 0 -55 33 -94 87 -104 67 -13 90 8 211 198 130 202 137 225 78 284 -27 27 -42 34 -72 34 -22 0 -50 -8 -64 -16z\"\/><path d=\"M2275 2693 c-553 -48 -1095 -270 -1585 -649 -135 -104 -459 -423 -483 -476 -23 -49 -22 -139 2 -186 73 -142 361 -457 571 -626 285 -228 642 -407 990 -497 242 -63 336 -73 660 -74 310 0 370 5 595 52 535 111 1045 392 1455 803 122 121 250 273 275 326 19 41 19 137 0 174 -41 79 -309 363 -465 492 -447 370 -946 591 -1479 653 -113 14 -422 18 -536 8z m395 -428 c171 -34 330 -124 456 -258 112 -119 167 -219 211 -378 27 -96 24 -300 -5 -401 -72 -255 -236 -447 -474 -557 -132 -62 -201 -76 -368 -76 -167 0 -236 14 -368 76 -213 98 -373 271 -451 485 -162 444 86 934 547 1084 153 49 292 57 452 25z m909 -232 c222 -123 408 -262 593 -441 76 -74 138 -139 138 -144 0 -16 -233 -242 -330 -319 -155 -123 -309 -223 -461 -299 l-81 -41 32 46 c18 26 49 83 70 128 143 306 141 649 -6 957 -25 52 -61 116 -79 142 l-34 47 45 -20 c26 -10 76 -36 113 -56z m-2057 25 c-40 -58 -105 -190 -130 -263 -110 -324 -59 -707 132 -981 25 -35 42 -64 37 -64 -19 0 -241 119 -326 174 -188 122 -406 314 -532 468 l-58 71 108 103 c185 178 428 349 672 473 66 33 121 60 123 61 2 0 -10 -19 -26 -42z\"\/><path d=\"M2375 1950 c-198 -44 -350 -190 -395 -379 -18 -76 -8 -221 19 -290 114 -284 457 -406 731 -260 98 52 188 154 231 260 27 69 37 214 19 290 -38 163 -166 304 -326 360 -67 23 -215 33 -279 19z\"\/><\/g><\/svg><\/i> <img data-recalc-dims=\"1\" loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"16\" height=\"16\" alt=\"Loading\" src=\"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/plugins\/page-views-count\/ajax-loader-2x.gif?resize=16%2C16&#038;ssl=1\" border=0 \/><\/p><div class=\"pvc_clear\"><\/div>","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>\u201cShi Shehu Maigidaje kamar Bahillace can daji, A wurin kiwon shanu nai, In ya koro za su yi \u0253arna, Sai ka ga matar shi na tare mai. \u2013 To haka nan Shehu Maigidaje, In ya \u0257auko wa\u0199a tai a rubuce, Sai ka ga matash shi na taya shi.\u201d \u2013 Shata a wa\u0199ar \u2018Na Gode Shehu [&hellip;]<\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div>\n<p id=\"pvc_stats_3060\" class=\"pvc_stats total_only  \" data-element-id=\"3060\" style=\"\"><i class=\"pvc-stats-icon medium\" aria-hidden=\"true\"><svg xmlns=\"http:\/\/www.w3.org\/2000\/svg\" version=\"1.0\" viewBox=\"0 0 502 315\" preserveAspectRatio=\"xMidYMid meet\"><g transform=\"translate(0,332) scale(0.1,-0.1)\" fill=\"\" stroke=\"none\"><path d=\"M2394 3279 l-29 -30 -3 -207 c-2 -182 0 -211 15 -242 39 -76 157 -76 196 0 15 31 17 60 15 243 l-3 209 -33 29 c-26 23 -41 29 -80 29 -41 0 -53 -5 -78 -31z\"\/><path d=\"M3085 3251 c-45 -19 -58 -50 -96 -229 -47 -217 -49 -260 -13 -295 52 -53 146 -42 177 20 16 31 87 366 87 410 0 70 -86 122 -155 94z\"\/><path d=\"M1751 3234 c-13 -9 -29 -31 -37 -50 -12 -29 -10 -49 21 -204 19 -94 39 -189 45 -210 14 -50 54 -80 110 -80 34 0 48 6 76 34 21 21 34 44 34 59 0 14 -18 113 -40 219 -37 178 -43 195 -70 221 -36 32 -101 37 -139 11z\"\/><path d=\"M1163 3073 c-36 -7 -73 -59 -73 -102 0 -56 133 -378 171 -413 34 -32 83 -37 129 -13 70 36 67 87 -16 290 -86 209 -89 214 -129 231 -35 14 -42 15 -82 7z\"\/><path d=\"M3689 3066 c-15 -9 -33 -30 -42 -48 -48 -103 -147 -355 -147 -375 0 -98 131 -148 192 -74 13 15 57 108 97 206 80 196 84 226 37 273 -30 30 -99 39 -137 18z\"\/><path d=\"M583 2784 c-38 -19 -67 -74 -58 -113 9 -42 211 -354 242 -373 16 -10 45 -18 66 -18 51 0 107 52 107 100 0 39 -1 41 -124 234 -80 126 -108 162 -133 173 -41 17 -61 16 -100 -3z\"\/><path d=\"M4250 2784 c-14 -9 -74 -91 -133 -183 -95 -150 -107 -173 -107 -213 0 -55 33 -94 87 -104 67 -13 90 8 211 198 130 202 137 225 78 284 -27 27 -42 34 -72 34 -22 0 -50 -8 -64 -16z\"\/><path d=\"M2275 2693 c-553 -48 -1095 -270 -1585 -649 -135 -104 -459 -423 -483 -476 -23 -49 -22 -139 2 -186 73 -142 361 -457 571 -626 285 -228 642 -407 990 -497 242 -63 336 -73 660 -74 310 0 370 5 595 52 535 111 1045 392 1455 803 122 121 250 273 275 326 19 41 19 137 0 174 -41 79 -309 363 -465 492 -447 370 -946 591 -1479 653 -113 14 -422 18 -536 8z m395 -428 c171 -34 330 -124 456 -258 112 -119 167 -219 211 -378 27 -96 24 -300 -5 -401 -72 -255 -236 -447 -474 -557 -132 -62 -201 -76 -368 -76 -167 0 -236 14 -368 76 -213 98 -373 271 -451 485 -162 444 86 934 547 1084 153 49 292 57 452 25z m909 -232 c222 -123 408 -262 593 -441 76 -74 138 -139 138 -144 0 -16 -233 -242 -330 -319 -155 -123 -309 -223 -461 -299 l-81 -41 32 46 c18 26 49 83 70 128 143 306 141 649 -6 957 -25 52 -61 116 -79 142 l-34 47 45 -20 c26 -10 76 -36 113 -56z m-2057 25 c-40 -58 -105 -190 -130 -263 -110 -324 -59 -707 132 -981 25 -35 42 -64 37 -64 -19 0 -241 119 -326 174 -188 122 -406 314 -532 468 l-58 71 108 103 c185 178 428 349 672 473 66 33 121 60 123 61 2 0 -10 -19 -26 -42z\"\/><path d=\"M2375 1950 c-198 -44 -350 -190 -395 -379 -18 -76 -8 -221 19 -290 114 -284 457 -406 731 -260 98 52 188 154 231 260 27 69 37 214 19 290 -38 163 -166 304 -326 360 -67 23 -215 33 -279 19z\"\/><\/g><\/svg><\/i> <img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" width=\"16\" height=\"16\" alt=\"Loading\" src=\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/plugins\/page-views-count\/ajax-loader-2x.gif\" border=0 \/><\/p>\n<div class=\"pvc_clear\"><\/div>\n","protected":false},"author":4,"featured_media":4553,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_FSMCFIC_featured_image_caption":"Alhaji Shehu Maigidaje Funtuwa (1949-2000)","_FSMCFIC_featured_image_nocaption":"","_FSMCFIC_featured_image_hide":"","_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[422],"tags":[19,116,20],"class_list":["post-3060","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-waoi","tag-mamman-shata","tag-shehu-maigidaje-funtuwa","tag-waoin-hausa"],"yoast_head":"<!-- This site is optimized with the Yoast SEO plugin v26.9 - https:\/\/yoast.com\/product\/yoast-seo-wordpress\/ -->\n<title>Tunawa da Shehu Maigidaje Funtuwa bayan shekara 20 - Ibrahim Sheme<\/title>\n<meta name=\"robots\" content=\"index, follow, max-snippet:-1, max-image-preview:large, max-video-preview:-1\" \/>\n<link rel=\"canonical\" href=\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=3060\" \/>\n<meta property=\"og:locale\" content=\"en_GB\" \/>\n<meta property=\"og:type\" content=\"article\" \/>\n<meta property=\"og:title\" content=\"Tunawa da Shehu Maigidaje Funtuwa bayan shekara 20 - Ibrahim Sheme\" \/>\n<meta property=\"og:description\" content=\"\u201cShi Shehu Maigidaje kamar Bahillace can daji, A wurin kiwon shanu nai, In ya koro za su yi \u0253arna, Sai ka ga matar shi na tare mai. \u2013 To haka nan Shehu Maigidaje, In ya \u0257auko wa\u0199a tai a rubuce, Sai ka ga matash shi na taya shi.\u201d \u2013 Shata a wa\u0199ar \u2018Na Gode Shehu [&hellip;]\" \/>\n<meta property=\"og:url\" content=\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=3060\" \/>\n<meta property=\"og:site_name\" content=\"Ibrahim Sheme\" \/>\n<meta property=\"article:published_time\" content=\"2020-12-23T19:50:08+00:00\" \/>\n<meta property=\"article:modified_time\" content=\"2024-04-23T08:00:51+00:00\" \/>\n<meta property=\"og:image\" content=\"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2022\/10\/IMG-20201225-WA0005.jpg?fit=180%2C304&ssl=1\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:width\" content=\"180\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:height\" content=\"304\" \/>\n\t<meta property=\"og:image:type\" content=\"image\/jpeg\" \/>\n<meta name=\"author\" content=\"Nafisat\" \/>\n<meta name=\"twitter:card\" content=\"summary_large_image\" \/>\n<meta name=\"twitter:label1\" content=\"Written by\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data1\" content=\"Ibrahim Sheme\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:label2\" content=\"Estimated reading time\" \/>\n\t<meta name=\"twitter:data2\" content=\"9 minutes\" \/>\n<script type=\"application\/ld+json\" class=\"yoast-schema-graph\">{\"@context\":\"https:\/\/schema.org\",\"@graph\":[{\"@type\":\"Article\",\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=3060#article\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=3060\"},\"author\":{\"name\":\"Nafisat\",\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#\/schema\/person\/bb4e2be5e35db546de899bf1493897e4\"},\"headline\":\"Tunawa da Shehu Maigidaje Funtuwa bayan shekara 20\",\"datePublished\":\"2020-12-23T19:50:08+00:00\",\"dateModified\":\"2024-04-23T08:00:51+00:00\",\"mainEntityOfPage\":{\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=3060\"},\"wordCount\":1794,\"commentCount\":0,\"publisher\":{\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#organization\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=3060#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2022\/10\/IMG-20201225-WA0005.jpg?fit=180%2C304&ssl=1\",\"keywords\":[\"mamman shata\",\"Shehu Maigidaje Funtuwa\",\"wa\u0199o\u0199in Hausa\"],\"articleSection\":[\"Wa\u0199a\"],\"inLanguage\":\"en-GB\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"CommentAction\",\"name\":\"Comment\",\"target\":[\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=3060#respond\"]}]},{\"@type\":\"WebPage\",\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=3060\",\"url\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=3060\",\"name\":\"Tunawa da Shehu Maigidaje Funtuwa bayan shekara 20 - Ibrahim Sheme\",\"isPartOf\":{\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#website\"},\"primaryImageOfPage\":{\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=3060#primaryimage\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=3060#primaryimage\"},\"thumbnailUrl\":\"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2022\/10\/IMG-20201225-WA0005.jpg?fit=180%2C304&ssl=1\",\"datePublished\":\"2020-12-23T19:50:08+00:00\",\"dateModified\":\"2024-04-23T08:00:51+00:00\",\"breadcrumb\":{\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=3060#breadcrumb\"},\"inLanguage\":\"en-GB\",\"potentialAction\":[{\"@type\":\"ReadAction\",\"target\":[\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=3060\"]}]},{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-GB\",\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=3060#primaryimage\",\"url\":\"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2022\/10\/IMG-20201225-WA0005.jpg?fit=180%2C304&ssl=1\",\"contentUrl\":\"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2022\/10\/IMG-20201225-WA0005.jpg?fit=180%2C304&ssl=1\",\"width\":180,\"height\":304},{\"@type\":\"BreadcrumbList\",\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=3060#breadcrumb\",\"itemListElement\":[{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":1,\"name\":\"Home\",\"item\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/\"},{\"@type\":\"ListItem\",\"position\":2,\"name\":\"Tunawa da Shehu Maigidaje Funtuwa bayan shekara 20\"}]},{\"@type\":\"WebSite\",\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#website\",\"url\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/\",\"name\":\"Ibrahim Sheme\",\"description\":\"\",\"publisher\":{\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#organization\"},\"potentialAction\":[{\"@type\":\"SearchAction\",\"target\":{\"@type\":\"EntryPoint\",\"urlTemplate\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?s={search_term_string}\"},\"query-input\":{\"@type\":\"PropertyValueSpecification\",\"valueRequired\":true,\"valueName\":\"search_term_string\"}}],\"inLanguage\":\"en-GB\"},{\"@type\":\"Organization\",\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#organization\",\"name\":\"Ibrahim Sheme\",\"url\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/\",\"logo\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-GB\",\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#\/schema\/logo\/image\/\",\"url\":\"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1\",\"contentUrl\":\"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1\",\"width\":512,\"height\":512,\"caption\":\"Ibrahim Sheme\"},\"image\":{\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#\/schema\/logo\/image\/\"}},{\"@type\":\"Person\",\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#\/schema\/person\/bb4e2be5e35db546de899bf1493897e4\",\"name\":\"Nafisat\",\"image\":{\"@type\":\"ImageObject\",\"inLanguage\":\"en-GB\",\"@id\":\"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#\/schema\/person\/image\/\",\"url\":\"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g\",\"contentUrl\":\"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g\",\"caption\":\"Nafisat\"},\"sameAs\":[\"https:\/\/ibrahimsheme.com\"],\"url\":\"\"}]}<\/script>\n<!-- \/ Yoast SEO plugin. -->","yoast_head_json":{"title":"Tunawa da Shehu Maigidaje Funtuwa bayan shekara 20 - Ibrahim Sheme","robots":{"index":"index","follow":"follow","max-snippet":"max-snippet:-1","max-image-preview":"max-image-preview:large","max-video-preview":"max-video-preview:-1"},"canonical":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=3060","og_locale":"en_GB","og_type":"article","og_title":"Tunawa da Shehu Maigidaje Funtuwa bayan shekara 20 - Ibrahim Sheme","og_description":"\u201cShi Shehu Maigidaje kamar Bahillace can daji, A wurin kiwon shanu nai, In ya koro za su yi \u0253arna, Sai ka ga matar shi na tare mai. \u2013 To haka nan Shehu Maigidaje, In ya \u0257auko wa\u0199a tai a rubuce, Sai ka ga matash shi na taya shi.\u201d \u2013 Shata a wa\u0199ar \u2018Na Gode Shehu [&hellip;]","og_url":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=3060","og_site_name":"Ibrahim Sheme","article_published_time":"2020-12-23T19:50:08+00:00","article_modified_time":"2024-04-23T08:00:51+00:00","og_image":[{"width":180,"height":304,"url":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2022\/10\/IMG-20201225-WA0005.jpg?fit=180%2C304&ssl=1","type":"image\/jpeg"}],"author":"Nafisat","twitter_card":"summary_large_image","twitter_misc":{"Written by":"Ibrahim Sheme","Estimated reading time":"9 minutes"},"schema":{"@context":"https:\/\/schema.org","@graph":[{"@type":"Article","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=3060#article","isPartOf":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=3060"},"author":{"name":"Nafisat","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#\/schema\/person\/bb4e2be5e35db546de899bf1493897e4"},"headline":"Tunawa da Shehu Maigidaje Funtuwa bayan shekara 20","datePublished":"2020-12-23T19:50:08+00:00","dateModified":"2024-04-23T08:00:51+00:00","mainEntityOfPage":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=3060"},"wordCount":1794,"commentCount":0,"publisher":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#organization"},"image":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=3060#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2022\/10\/IMG-20201225-WA0005.jpg?fit=180%2C304&ssl=1","keywords":["mamman shata","Shehu Maigidaje Funtuwa","wa\u0199o\u0199in Hausa"],"articleSection":["Wa\u0199a"],"inLanguage":"en-GB","potentialAction":[{"@type":"CommentAction","name":"Comment","target":["https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=3060#respond"]}]},{"@type":"WebPage","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=3060","url":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=3060","name":"Tunawa da Shehu Maigidaje Funtuwa bayan shekara 20 - Ibrahim Sheme","isPartOf":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#website"},"primaryImageOfPage":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=3060#primaryimage"},"image":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=3060#primaryimage"},"thumbnailUrl":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2022\/10\/IMG-20201225-WA0005.jpg?fit=180%2C304&ssl=1","datePublished":"2020-12-23T19:50:08+00:00","dateModified":"2024-04-23T08:00:51+00:00","breadcrumb":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=3060#breadcrumb"},"inLanguage":"en-GB","potentialAction":[{"@type":"ReadAction","target":["https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=3060"]}]},{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-GB","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=3060#primaryimage","url":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2022\/10\/IMG-20201225-WA0005.jpg?fit=180%2C304&ssl=1","contentUrl":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2022\/10\/IMG-20201225-WA0005.jpg?fit=180%2C304&ssl=1","width":180,"height":304},{"@type":"BreadcrumbList","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?p=3060#breadcrumb","itemListElement":[{"@type":"ListItem","position":1,"name":"Home","item":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/"},{"@type":"ListItem","position":2,"name":"Tunawa da Shehu Maigidaje Funtuwa bayan shekara 20"}]},{"@type":"WebSite","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#website","url":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/","name":"Ibrahim Sheme","description":"","publisher":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#organization"},"potentialAction":[{"@type":"SearchAction","target":{"@type":"EntryPoint","urlTemplate":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/?s={search_term_string}"},"query-input":{"@type":"PropertyValueSpecification","valueRequired":true,"valueName":"search_term_string"}}],"inLanguage":"en-GB"},{"@type":"Organization","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#organization","name":"Ibrahim Sheme","url":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/","logo":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-GB","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#\/schema\/logo\/image\/","url":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1","contentUrl":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/IshemeLogo.png?fit=512%2C512&ssl=1","width":512,"height":512,"caption":"Ibrahim Sheme"},"image":{"@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#\/schema\/logo\/image\/"}},{"@type":"Person","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#\/schema\/person\/bb4e2be5e35db546de899bf1493897e4","name":"Nafisat","image":{"@type":"ImageObject","inLanguage":"en-GB","@id":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/#\/schema\/person\/image\/","url":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g","contentUrl":"https:\/\/secure.gravatar.com\/avatar\/e999cea8cab471727b3785d6d6c13039b2fc941be9c3077e56e254375b4b48f5?s=96&d=mm&r=g","caption":"Nafisat"},"sameAs":["https:\/\/ibrahimsheme.com"],"url":""}]}},"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/i0.wp.com\/ibrahimsheme.com\/wp-content\/uploads\/2022\/10\/IMG-20201225-WA0005.jpg?fit=180%2C304&ssl=1","jetpack_likes_enabled":true,"jetpack_sharing_enabled":true,"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3060","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/users\/4"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcomments&post=3060"}],"version-history":[{"count":3,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3060\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":5354,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/posts\/3060\/revisions\/5354"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/index.php?rest_route=\/wp\/v2\/media\/4553"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fmedia&parent=3060"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Fcategories&post=3060"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/ibrahimsheme.com\/index.php?rest_route=%2Fwp%2Fv2%2Ftags&post=3060"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}