Hiyana – Tsiraici a fagen shirin fim

Wata zazzafar muhawara ta barke a kasar Hausa tun daga makon jiya. Wani guntun hoton bidiyo na minti takwas mai nuna tsiraicin wasu matasa biyu ya bayyana a makon da ya wuce. Mutanen biyu dai mace da namiji ne, kuma macen ba wata ba ce illa wata ‘yar fim mai suna Maryam Usman, jarumar shirin ‘Hiyana’. Ana yi mata lakabi da ‘Maryam Hiyana’.

Kasancewar ta ‘yar fim ya sa mutane da dama su na cewa lallai yanzu ta tabbata cewa ‘yan fim ‘yan iska ne. Na kalli “video clip” din da ido na, kuma na kad’u matuka da na gan shi, musamman da yake dukkan su Musulmi ne. An nuno yarinyar tsirara a ciki. Wani saurayin ta wai shi Bobo, wanda ke sana’ar canjin kudi a Legas, ya dauke ta hotunan bidiyo din da kyamarar wayar sa ta selula har na tsawon sama da minti takwas. An nuno ta kwance a kan gado, haihuwar uwar ta, daga nan kuma shi ma ta dauke shi da kyamarar – shi ma zigidir, alkalamin sa a mike; daga nan kuma shu’umin ya hau kan yarinyar, ya yi lalata da ita a lokacin da yake ci gaba da daukar hotunan bidiyo din. Har sai da ya kawo (a gafarce ni!), kuma ya yi wasa da maniyyin sa a kan cinyar ta.

A cikin “clip” din, Bobo da yarinyar su na magana, kuma ana ji radau.

Yanzu mutane cewa su ke yi wai an yi “bulu fim.” To amma a gani na, za a iya cewa an yi “fim” ba a yi “fim” ba. Abin da ya sa na ce haka shi ne, wadannan matasa biyu ba su dauki wannan iskanci da nufin shirya fim ba. Shi fim, ai ya na da matakai da dalilai na shirya shi, da ma’aikata da sauran su, kuma a karshe manufar sa a kai kasuwa a sayar. Har ma sai an yi tallar sa a kafafen watsa labarai kafin a kai shi kasuwa. Su kuwa wannan yarinya da wannan mutum sun yi wannan abu ne domin shi mutumin ya rika kallo bayan sun rabu.

A lura, sun dauki wannan abu ne a cikin 2006, amma sai yanzu ya fito duniya ta sani. Can a kwanan baya Yakubu Lere, mawallafin mujallar Gidauniya, ya buga labari mai nuna cewa wata yarinya ta yi “bulu fim,” har abin ya harzuka ‘yan fim, su ka dakatar da sayar da mujallar a shagunan sayar da finafinai a Kano.

Akwai bayani na daban kan yadda wannan bidiyon tsiraicin ya fita daga hannun su har ya shiga hannun jama’a, amma wannan wani labarin ne na daban.

Babu shakka abin da suka aikata abin Allah-wadai ne, musamman a daidai lokacin da mutuncin ‘yan fim ya ke tangal-tangal din zubewa. Don haka babu dalilin kare su a nan. Sun yi ba daidai ba. Wannan shi ne bidiyo na farko mai nuna tsiraicin Hausawa da ya shiga hannun jama’a miliyoyi (kuma ba a san inda abin zai tsaya ba!).

Ba a yi “blue film” ba domin wannan ba fim ba ne, “clip” ne kawai aka yi domin “private viewing”. Ita kan ta yarinyar, da farko ba ta san ja’irin daukar ta ya ke yi da kyamarar wayar sa ba har sai da ya gaya mata, kuma ta bayyana mamaki tare da cewa ya daina. Amma da yake ya ba ta ta dauke shi (kuma tsautsayi ba ya da rana!), sai ta kyale shi har ya yi lalata da ita ya na dauka.

A sakamakon wannan abu, mutuncin ‘yan fim ya kara zubewa. A ranar Juma’a da ta wuce, malamai sun yi hudubobi a kan wannan al’amari, kuma sun yi tsinuwa. Haka kuma an ci gaba da yin Allah-wadai da al’amarin a wurare da dama. Kafafen yad’a labarai su na ta babatu a kai.

Yarinya dai ta gudu ta boye (an ce wani saurayin ta da ya ce shi ya ji ya gani zai aure ta, shi ne ya boye ta – wai ma za su yi aure kafin azumi).

Duk wani dan fim ya kad’u. Shugabannin ‘yan fim hankalin su ya tashi matuka. A yau din nan sun ba da sanarwar dakatar da shahararrun ‘yan wasa sama da goma (maza da mata) wadanda ake zargi da aikata munanan ayyuka iri-iri, ciki har da zina da shaye-shaye. Sun yi haka ne don ganin sun tsaftace harkar daga bata-gari da ke shigowa su na yin abin da su ka ga dama, kuma don gudun fushin Gwamnatin Jihar Kano, wadda ake ganin za ta iya daukar tsauraran matakai kan harkar fim din baki dayan ta.

Amma jama’a mu yi tunani: ba fa ‘yan fim kadai ba ne ‘yan iska. Mutumin da ya yi ummulhaba’isin wannan aika-aika, BA DAN FIM BA NE, kuma BAHAUSHE ne, magidanci, mai sana’a, miloniya, dan kasuwa. DON HAKA, al’umar Hausawa (Musulmi) baki dayan ta ce ta ke bukatar gyara. Kuma dukkan mu kowa ya dubi kan sa, ya gyara rayuwar sa, domin babu shakka a cikin masu yin kumfar baki kan wannan abu akwai masu aikata zububban da su ka fi wannan da ake babatu a kan sa.

Allah ya shirye mu baki daya, amin.

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *