Hira Da Usman Bobo Kan Badaƙalar Maryam Hiyana

  • Gyaran waya ya ba abokin sa, shi kuma ya kwafi majigin daga ciki
  • Bobo ya rantse sau 16 cikin guntuwar tattaunawa
  • Ya na neman afuwar dukkan Musulmi

ALHAJI Usman Bobo, ɗan canjin nan da ya ɗauki majigin batsa tare da Maryam Usman Hiyana (ga hoton ta nan a sama), ya ɓace ɓat tun daga lokacin da sirrin su ya tonu. A farkon faruwar lamarin, shugabannin ’yan fim na Kano sun kira shi sun nuna masa ɓacin ran su kan wannan abu. Majiyar mujallar Fim ta ce mutumin ya yi nadama a gare su, har ya na cewa wallahi shi ba kan sa ya ke ji ba, yarinyar ya ke ji. An ba mujallar lambobin wayar Usman, amma ya ƙi samuwa.

Kwatsam, a ranar Lahadi, 19 ga Agusta, sai ga labarin Bobo ya ɓullo a sashen Hausa na BBC, a shirin su na rana. Duk da yake akwai abubuwa da yawa da ba a tambayi mutumin ba, amma hirar ta ƙara haske kan wannan rikirkitaccen lamari. A hirar, Bobo ya bayyana cewa ya na zaman ɓoyo ne a yanzu, kuma ya nuna tsantsar nadama, sa’annan ya yi kira ga jama’a da su yafe masa wannan taɓargaza da ya tafka. Ga yadda hirar ta kasance:

BBC: Ko me ya sa ka aikata wannan abin kunya?

BOBO: Wallahi tallahi ba na yi da gayya ba ne.

BBC: To kamar ya abin ya taso daga gare ka, kai?

BOBO: Wallahi abin nan sirri ne. Wani aboki na ne ya saci wayar nan… wani aboki na, wallahi tallahi, wayar nan na ba shi ya yi min gyaran ta. Ka na ji na ko? Kuma abin nan an yi shi sama da shekara ɗaya, wajen shekara ɗaya da wata tara kenan. Kuma wallahi tallahi na yi nadama. Kuma ina fatan don Allah don Annabi duniya ta yafe min abin da ya faru. Wallahi, domin duniya… saboda Allah da Annabi su yafe min. Abin nan ba wai na yi shi ba ne ko da gayya ko da wani abu, ka fahimta… ko da fariya. Wallahi sace wayar nan aka yi, wallahi tallahi, abin ya fita.

BBC: Kai ne dai ka yi abin a waya aka ɗauka. Me ya sa tun asali ɗin, misali, ka ɗau abin a cikin waya ka yi shi, duk da ka san ba abu ne da ya dace ka ɗauka a waya ba, misali?

BOBO: Ai lokacin na ke gaya maka, tun a lokacin na riga na goge, wani ne ya sace abin.

BBC: To yanzu yaya ka ke ji game da wannan abu da ya taso haka?

BOBO: Baƙin ciki, wallahi! Abin ya na damu na sosai, wallahi tallahi! Wallahi ba na iya shiga jama’a, ba na iya yin komai wallahi.

BBC: Yanzu ka na sane da cewa akwai waɗanda ma su ke cewa lallai da kai da ita wannan yarinyar da ku ka yi wannan abu, kamata ya yi sai an hukunta ku saboda ba kan ku kawai ku ka yi wa ba, kun yi wa mutane, kun janyo wa al’umar Musulman arewacin Nijeriya da ma duk inda su ke wani abu na ƙasƙanci?

BOBO: E, shi ne na ke roƙon Musulman duniya. Ina nuna damuwa ta a kan laifin da na yi wa Musulunci da Musulmai. Shi ya sa na ke neman gafara ga Musulman duniya su yafe min saboda Allah da Annabi. Kuma ina fatan Allah Ubangiji ya yafe min, kuma ya shirye mu gaba ɗaya.

BBC: Kamar zuwa yanzu ka san halin da ita yarinyar da ku ka ɗauki hoton ta ke ciki? Ka yi magana da ita zuwa yanzu?

BOBO: Wallahi tallahi ba mu yi magana ba, amma na san ta na cikin damuwa wallahi.

BBC: Daga lokacin da abin ya bazu zuwa yanzu, ka na ci gaba da harkokin sana’ar ka ko kuwa me ya ke faruwa?

BOBO: Wallahi tallahi ba ma wanda ya san inda na ke a halin yanzu, don na gudu, na bar ma garin gaba ɗaya, wallahi.

BBC: Ka na nufin ba ma a cikin Legas ɗin ka ke ba a yanzu?

BOBO: Wallahi ba a cikin Legas na ke ba.

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *