Hattara Da Ramuka A Gaba!

A jiya Alhamis ne ɗimbin ’ya’yan jam’iyyar PDP, musamman dalaget, su ka yi kwamba a Abuja domin gudanar da zaɓen fitar da gwani na wanda zai yi takarar zama shugaban ƙasa a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar su. Tun kafin ranar, dalaget da sauran membobin PDP ɗin su ka dinga antayowa zuwa cikin babban birnin na tarayya, ta yadda ko ya zuwa ran Talata da wuya mutum ya samu ɗaki a dukkan otal-otal na garin. Su ma wuraren cin abinci sun cika maƙil da baƙin.

In ba domin batun ya shafi PDP ba ne, to da wataƙila sai mu zuba na mujiya kurum, mu yi kallon badaƙalar da ake yi. To amma PDP ta na kurarin cewa ita ce jam’iyyar siyasa da ta fi kowace girma a nahiyar Afrika. Haka kuma ita ce jam’iyyar da ke mulki a Nijeriya. Ta haifar da shugabannin ƙasar har guda uku daga lokacin da aka fara Jamhuriya ta Huɗu, domin kuwa ita ce aka ce ta lashe zaɓuɓɓukan shugaban ƙasa da aka yi a cikin 1999 da 2003 da kuma 2007. Sannan ita ce ke da rinjaye a yawancin jihohin tarayyar ƙasar nan, da kuma Majalisar Tarayya. Ƙungiyar Gwamnonin Nijeriya yawanci membobin PDP ne su ka cika ta, kuma ta na daga cikin ƙungiyoyi masu faɗa a ji a ƙasar nan. Bugu da ƙari, duk wasu tsare-tsare na mulkin ƙasa waɗanda PDP ta fito da su kuma ta ke aiwatarwa, waɗanda aka ɗibiya a kan ɗimbin kuɗaɗen shiga da ke zuwa daga safarar man fetur, su na shafar rayuwar jama’ar ƙasar nan. Saboda haka, ko an ƙi ko an so, zaɓen wanda zai tsaya takarar zama shugaban ƙasa na jam’iyyar ya na da matuƙar tasiri a rayuwar ’yan Nijeriya, ya Allah tasirin nan mai kyau ne ko akasin haka. Don haka, tilas ne mu damu kan wannan lamari, domin duk shukar da za a yi a wannan gangami zai iya shafar rayuwar mu kusan ta kowane ɓangare.

Kamar yadda kowa ya sani ne, wannan ne karo na farko da shugaba mai ci yanzu, wato Dakta Goodluck Jonathan, ya ke takarar wani muƙami da sunan sa. A da, shi sifiya-taya ne kurum – inda a Jihar Bayelsa ya yi mataimakin gwamna, sannan a 2007 ya zama mataimakin shugaban ƙasa. A yanzu ne ya ke gwajin farin jinin sa a karo na farko. Idan har ya na so ya zama zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, to, na farko sai ya tsallake siraɗin zaɓen da aka taru a yi a jiya, 13 ga Janairu. Idan ya ci, sai kuma shallake siraɗi na biyu: wato kada abokan hamayyar sa waɗanda sauran jam’iyyu za su tsayar. Duk waɗannan siraɗan, ba wasan yara ba ne. Aiki ne wurjanjan. Ko a kogin farko da ya ke ƙoƙarin hayewa yanzu, akwai maridan kadoji a ciki; Jonathan ya na bugawa ne a zaɓen fidda gwani mafi tsauri a takarar zama shugaban ƙasa da aka taɓa yi a tarihin siyasar Nijeriya.

Hakan na faruwa ne saboda abin da masu nazarin al’amuran yau da kullum su ke kallo a matsayin daɓa wa ciki wuƙa da PDP ta yi: wato yarjejeniyar karɓa-karɓar shugabancin ƙasa tsakanin arewa da kudu da ta rattaba hannu a kai. Jonathan ya ɗare kujerar shugaban ƙasa ne ta hanyar sa’a kurum lokacin da maigidan sa, Shugaba Umaru Musa Yar’Adua, ya kwanta dama. A yarjejeniyar da aka yi, kamata ya yi shugaban ƙasa da zai maye gurbin Yar’Adua ya fito daga arewa domin kuwa shi Yar’Adua bai kammala wa’adin da ya kamata yankin ya yi ba. To amma shi Jonathan da magoya bayan sa, sun zaɓi su yi fatali da wannan yarjejeniyar. Su kuwa manyan ’yan takarar PDP daga arewa, sai su ka janye, su ka goyi bayan tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar (Turakin Adamawa), sakamakon yarjejeniyar fidda ɗan takara ƙwaya ɗaya na arewa a jam’iyyar da aka yi, kuma akwai yiwuwar shi za su ci gaba da goyon baya a wannan zaɓen fidda gwanin da kuma bayan zaɓen.

A yayin da ake cikin haka, sai ɓangarorin biyu su ka shiga yaƙin watsa wa juna ƙasa a ido. A kullum sai ka ga wanin su ya na yi wa ɗan’uwan sa ɓatanci a jarida, da zargi iri-iri na cin hanci da rashawa da kuma ambaton wasu kalamai maras daɗi da wani daga cikin su ya taɓa yi a baya. Manufa ita ce a nuna cewa wane bai dace da zama shugaba ba. Ɗaya daga cikin wannan zargin na kwana kwanan nan shi ne inda aka ruwaito Atiku ya na ragargazar jam’iyyar ta PDP, aka ce wai ya yi kalamin ne a cikin watan Nuwamba na shekarar 2006.

Shin Atiku bai da hurumin yin irin wannan maganar a WANCAN lokacin, wanda kowa ya san cewa da gaske ne PDP jam’iyya ce inda ba a bin doka da oda? Kalamin da aka ce Atikun ya yi, wai ya yi shi ne a sashen Hausa na Muryar Amurka inda ya ce PDP “ba ta da ƙa’ida; ba ta bin doka da oda da kuma shugabannin ta.” Amma idan mun duba da kyau, za mu ga cewa duk abin nan da Atiku ya faɗa game da PDP a wancan lokacin, gaskiya ne. Akwai ma mutanen da su ka faɗi abin da ya fi haka. Shahararren marubucin nan, Farfesa Wole Soyinka, ya bayyana jam’iyyar PDP da cewa sheƙar baƙaƙen macizai ce kawai.

An shafe shekaru PDP ta na cikin rigingimu, ba don kurum ’ya’yan ta sun ɗauke ta a matsayin hanya mafi gajarta wajen kuɗancewa a dare ɗaya ba, a’a har ma da yadda babu tsarin dimokiraɗiyya a cikin ta. A PDP, ana cusa wa masu zaɓe ɗan takara, a ce shi ake so a zaɓa ko da kuwa jama’a ba su son shi, kuma lallai ne duk wanda aka tsayar sai ka ji shi ne ya lashe zaɓen. Sakamakon haka, a yayin da ake ta kiraye-kirayen cewa ya kamata a kimtsa jam’iyyar, sai ’ya’yan ta da yawa su ka dinga sauya sheƙa. Kuma jam’iyyar ta faɗi a sababbin zaɓuɓɓuka da aka yi a wasu jihohin. A yau ma da hukumar zaɓe ta ke ta yayata cewa za ta gudanar da zaɓe fisabilillahi, ai ga shi nan ’yan PDP da dama sun yi hijira zuwa wasu jam’iyyun, inda su ka tsaya takara. Alamun cewa an fara dawowa daga rakiyar jam’iyyar ta bayyana ƙarara a zaɓuɓɓukan fidda gwani na takarar zuwa Majalisar Tarayya da aka gudanar a ƙarshen makon jiya, inda sanatoci da ’yan Majalisar Wakilai da dama su ka sha kaye a hannun abokan adawar su. To, kallo ma bai ƙare ba har sai an zo zaɓe tsakanin jam’iyya da jam’iyya; a nan ne idon wasu ’yan takara – ciki kuwa har da gwamnoni – zai raina fata. Sai ga shi a yau PDP ta shiga gargada, duk da cika-bakin da shugaban ta na ƙasa na lokacin, wato Prince Vincent Ogbulafor, ya taɓa yi na cewa sai sun yi mulki har na tsawon shekara 60 ba tsinkewa; yanzu akwai alamun za ta faɗi ba nauyi.

Wannan zaɓen fidda gwanin da ’yan PDP ke yi a Abuja zai iya haifar da alheri ko sharri ga jam’iyyar, har abin ya shafi ƙasa baki ɗaya. Akwai ɗar-ɗar ɗin da ake yi na abin da zai iya wakana idan har Jonathan ya faɗi a zaɓen ko idan Atiku ne ya faɗi. Tambayar da ake yi ita ce, shin idan shugaban ƙasar ya sha ƙasa, zai koma koyarwar sa a makaranta ne ko kuwa zai samu wata mafaka ne inda zai riƙa cin duniyar sa da tsinke? Ma’ana, zai yarda ya sauka daga karagar mulki kuwa kamar yadda ya taɓa alƙawartawa? Ko kuwa zai yi irin na Shugaba Laurent Gbagbo na ƙasar Cote d’Ivoire ne, ya ce atafau ba zai sauka ba? Sa’annan ko kuwa shi Atiku, angulu za ta koma gidan ta na tsamiya ne ko kuma zai sake dabarar da ake raɗe-raɗin zai bi, idan har aka tandara shi da ƙasa? Ku sani cewa ita wannan sabuwar dabarar, ba fa wadda ’yan ɓangaren Jonathan ke yaɗawa ba ce, cewa wai Atiku ya ce zai janyo fitina idan ba a zaɓe shi ba. Dabarar dai ita ce wataƙila shi da magoya bayan sa su fice daga PDP su koma wata jam’iyyar su mara wa ɗan takarar ta baya, misali jam’iyyar CPC ta su Janar Muhammadu Buhari, ba don komai ba sai don a tabbatar da cewa an taɗiye Jonathan.

Shahararren marubucin nan ɗan ƙasar Ingila wanda ya rasu ɗaruruwan shekaru da su ka gabata, wato William Shakespeare, ya rubuta a littafin sa na wasan kwaikwayo mai suna ‘Julius Caesar’ cewa a tabbatar an yi kaffa-kaffa da ranar 13 ga Maris ko ranar 13 ga Janairu, domin kuwa wani mugun abu na iya faruwa a ranar ko a sakamakon ta. Sai ga shi ’yan PDP sun taru domin yin zaɓe a ran 13 ga Janairu. To, mu dai addu’ar mu ita ce ko ma wace irin waina aka toya a jiya Alhamis, Allah ya sa ta alheri ce ga Nijeriya. Manyan kurayen da ke mulki a kan dokin PDP sun daɗe su na yi wa ’yan Nijeriya hawan ƙawara, bayan kuwa a baki su na iƙirarin wai sun zo ne su ceci talaka daga fatara da yunwa. Sai ga shi fatara da yunwar ba su ragu ba. Ci-gaban mai ginar rijiya kawai ake yi. Nijeriya ta ci gaba da kasancewa ƙasa mai koma-baya ta fuskar tattalin arziki, sannan ta na daga cikin jerin ƙasashe waɗanda cin hanci da rashawa ya yi wa katutu. Ya Allah, mu na roƙon Ka da kada mu faɗa cikin ramukan da mu ke hangowa a gaban mu. Amin summa amin.

An buga a LEADERSHIP HAUSA ta makon jiya

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *