Hafsatu Abdulwahid: Gwagwarmayar Jikanyar Mujaddadi A Fagen Rubutu

Macen da ta fara rubuta littafin hikaya a Arewa, wato HAJIYA HAFSATU AHMAD ABDULWAHEED, ta samu karramawa ta musamman daga Ƙungiyar Marubuta ta Nijeriya (ANA). Shin yaya ta ji a ran ta? Kuma ina ta sa gaba yanzu?

HAJIYA Hafsatu Ahmad Abdulwaheed ita ce mace ta farko da ta rubuta littafin hikaya da aka wallafa shi a Arewacin Nijeriya kwata. Littafin ta na farko, ‘So Aljannar Duniya’, ya fito cikin a 1972 lokacin da aka yi gasar marubutan Hausa, har ta zo ta biyu. Marubuciyar ta rubuta littattafai da dama waɗanda ba su fito ba, kuma ta daɗe ta na faɗi-tashin ganin yadda littattafan ta za su fito, amma rashin kuɗi ya hana.

Kwanan nan, abubuwa biyu sun faru ga Hajiyar. Na farko, ana nan ana shirin fito da wasu daga cikin littattafan ta, ciki har da wani na gajerun ƙirƙirarrun labarai. Na biyu, lokacin daj aka yi wani gagarumin bikin karrama marubutan Arewa a Minna, Jihar Neja, Hajiya Hafsatu ta na daga cikin marubutan Hausa da aka karrama da kyautar lambar girma.

Ba wannan ba ne karo na farko da na yi hira da Hajiyar, domin idan kun tuna a ‘yan shekarun baya mun taɓa kawo maku wata hira da ita. A wannan karon, mun tattauna ne kan waɗannan abubuwa biyu da su ka faru gare ta, waɗanda duk na alheri ne.

Wani abu da ya kamata ku sani shi ne, Hajiya Hafsatu ta na daga cikin manyan mutanen ƙasar nan. Na farko, ita jinin Mujaddadi Shehu Usmanu Ɗanfodiyo ce. A Jihar Zamfara kuma, fitacciyar ‘yar siyasa ce, domin a zaɓen 2003 da aka yi, ta yi takarar zama gwamnar jihar. Ta na da ‘ya’ya maza da mata; babba daga cikin ‘ya’yan ta, Hajiya Ƙadaria Ahmad, ta taɓa aiki a gidan rediyon BBC a London, yanzu kuma babbar ma’aikaciya ce a wani kamfanin kula da filayen jiragen sama a Legas. Haka kuma wata ɗiyar ta Hajiya Hafsatu, wato Hajiya Asiya, ta na auren tsohon Ministan Abuja, Malam Nasir Ahmad El-Rufa’i. Hasali ma dai, mun yi wannan tattaunawar ne da ita a gidan shi Malam Nasir da ke unguwar Jabi, a Abuja, kwana ɗaya bayan an karrama ta. To bugu da ƙari kuma Hajiya Hafsatu ta kafa tarihin kasancewa mace ta farko da ta wallafa littafin hikaya a Arewa.

IBRAHIM SHEME: Ran ki ya daɗe, ki na daga cikin marubuta na Arewa waɗanda aka karrama su da lambar girma a Minna. Yaya ki ka ji a kan wannan karramawa da aka yi maki?

HAFSATU AHMAD ABDULWAHID: Alhamdu lillahi, na ji daɗi sosai. Sai dai baƙin ciki na kawai shi ne, uba na da uwa ta da miji na ba su da rai, balle su san abin da na samu. Amma murna kam na yi murna ƙwarai da gaske. Alhamdu lillahi.

SHEME: Wannan shi ne karo na farko da aka karrama ki a kan harkar rubutu?

HAFSATU: E, an taɓa yi a Kano, har su ka ba ni kamar lambar girma haka. Amma gaskiya na manta lokacin. Ina jin bara ne ko bara waccan.

SHEME: Su waye su ka yi waccan karramawar?

HAFSATU: Wata ƙungiya ce ta matasa marubuta.

SHEME: Yaya ki ke ganin batun karrama marubuta, wanda ba a cika yi ba, yanzu ga shi ana yi? A farkon shekerar nan an yi a Abuja, sai kuma ga shi an yi a Minna. Shin wannan ya fara sauya tunanin mutane ne game da marubuta?

HAFSATU: Ina ganin ’yan Arewa sun fara gane muhimmancin marubutan su. Ka san a da mutanen mu ba su damu da marubuta ba, musamman ma dai mata, ba a cika gane muhimmancin mu sosai ba, saboda an ɗauka rubuce-rubucen mu shirme ne; na soyayya kawai. To, ina ji yanzu lokaci ya zo da aka soma gane muhimmancin mu. Saboda haka aka ƙirƙiro wannan. Ya yi daidai, kuma ya kamata a ci gaba da yin haka ɗin.

SHEME: A wurin bikin wannan karramawar a Minna, lokacin da ake karanta taƙaitaccen tarihin ki, an nuna cewa ke jikanya ce ko jinin Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodiyo ce. Mutane za su so ki yi ƙarin bayani a kan wannan salsala taki.

HAFSATU: To, ni dai sunan uba na Alhaji Abubakar Garba, sunan baban sa Sa’idu. Sa’idu kuma Hayatu ne ya haife shi. Hayatu kuma Sa’idu ne ya haife shi. To, shi kuma Sa’idu, Muhamman Bello ne ya haife shi. Muhamman Bello kuma ɗan Shehu Usmanu Ɗanfodiyo ne. Saboda haka ya zamana ni jikanyar jikanyar Shehu ce.

SHEME: To, ko daga nan za ki ba mu taƙaitaccen tarihin ki?

HAFSATU: An haife ni a 1952 a Kano, cikin unguwar Ƙofar Mata. Kuma na yi karatu a Shahuci da Provincial Girls School da Shekara Secondry School. Bayan nan na yi aure, inda miji na a da shi ne manajan John Holt a Kano, daga baya aka mayar da shi Gusau. Bayan nan na yi ‘enrolling’ a Beneth Correspondence College, London, inda na ɗan ƙoƙarta na sami difloma. To, bayan nan dai na ci gaba da rubuce-rubuce. Na yi ɗan aiki taƙaitacce a Kano, kamar ‘part-time’ haka, a gidan Rediyon Kano, amma ban daɗe ba, saboda ban daɗe da somawa ba na koma Gusau ɗin. To, bayan nan dai sai rubuce-rubuce kawai da na ci gaba da yi a gida.

SHEME: A binciken da na yi na fahimci cewa ke ce mace ta farko a Arewa da ta fara wallafa littafin ƙirƙira, wato littafin ki ‘So Aljannar Duniya’. Shin ki na da masaniyar cewa mata sun yi rubutu kafin ke ko kuwa a iyakar sanin ki ke ce ki ka fara ɗin?

HAFSATU: To, gaskiya ni dai ban taɓa ganin littafin wata ba ko da a jarida ko a wani guri da aka ce ta yi rubutu, sai da nawa ya fito tukunna. To, kuma bayan nawa ya fito – ina ji da kusan shekara 12 ma – na Zaynab Alkali ya fito. Koda ya ke akwai bambanci tsakanin nawa da ita, don ita na Turanci ta yi, ni kuwa da Hausa na yi.

SHEME: Ko za ki gaya mana tarihin rubuta ‘So Aljannar Duniya’? Na farko ma dai, menene ya fara ba ki tunanin rubuta littafi a lokacin da mata ba sa yi?

HAFSATU: To, gaskiya a makarantar da na yi an ɗan ba mu ƙarfin gwiwar rubuta ’yan labarai a aji, har mu kan karɓi ’yan kyautuka a kai. A lokacin da na rubuta wannan ma da Turanci na soma rubuta shi duk da cewa Turancin nawa bai nuna ba, saboda yaya ta da ta auri Balaraben Libya ta sami ’yan tangarɗoɗi wajen dangi, haka da iyaye, waɗanda ba su so ta auri wani baƙo ba. To, daga baya kuma bayan na rubuta wannan sai na zo na auri wani Balaraben Yemen. To, sai labarin ya zamo kusan iri ɗaya ne. To, da na rubuta shi da Turanci ban sami bugawa ba har lokacin da kamfanin NNPC Zaria ya yi gasa ɗin nan, sai na fassara shi da Hausa na shiga gasar. A 1970 kenan. Na sami zuwa ta biyu a matsayi na na mace kaɗai da ta shiga wannan takara. To, bayan nan ne aka buga shi a 1972.

SHEME: Tunda da Turanci ki ka fara rubuta shi, da yaya sunan sa?

HAFSATU: Wallahi a lokacin ban sanya masa suna ba, don ɗaya daga cikin abin da su ka hana ita yayar tawa a buga littafin shi ne mu na ta ƙoƙarin mu ga wanne irin suna ya kamata a sanya masa. Saboda haka a lokacin ban sanya masa suna ba. (Murmushi) Amma dai Malam Sheme ya sanya masa suna a jarida (Weekly Trust); na gani. To, ina jin idan za mu yi shi da Turanci abin da za mu kira shi kenan!

SHEME: Akwai yiwuwar za a fassara shi ne nan gaba?

HAFSATU: E. An ma fassara shi da Turanci da Filatanci, kuma Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sokoto, sun yi shi da Arabiyya. To, amma dai duk da haka har yanzu babu wanda aka rubuta a ciki.

SHEME: Me ya tsayar da aikin bugun?

HAFSATU: Gaskiya rashin kuɗi ne a lokacin. Amma shi na Arabiyyar na samu wani mutumin Saudiyya da ya ce zai buga. To, amma abin baƙin ciki na yi gobara a 1995, saboda haka wannan kwafen na Arabiyya ɗin ya ƙone, kuma na yi ƙoƙarin samun kwafe a hannun jami’ar ta Sokoto, don in kwafa, ban samu ba. Amma yanzu wani yaro ya sake buga shi da Larabci ɗin. Saboda haka yanzu ina da rubutun hannu na Larabci ɗin.

SHEME: Labarin ‘So Aljannar Duniya’ labari ne na Fulani, ku kuma ga shi a gari ku ke. Me ya ba ki tunanin ki rubuta labarin Fulani maimakon labarin Hausawa wanda ki ka fi sabawa da shi?

HAFSATU: To, ai ni Bafillatana ce, kuma duk da yake mu na cikin Hausawa, gidan mu ba mu zubar da yawancin al’adun mu na Fulani ba, domin ba a ma Hausa a gidan mu. Idan yaro ya tashi ba ya yin Hausa sai ya kai irin shekara bakwai ɗin nan; sannan ya soma fita waje, ya koyi Hausa. Saboda haka ba wai wani abin a zo a gani ba ne don na rubuta al’adun mu.

SHEME: Bayan wannan littafi sai aka ɗauki tsawon lokaci ba ki yi wani littafin ba har zuwa lokacin da ki ka yi ‘’Yar Dubu Mai Tambotsai’. Me ya sa aka samu wannan tsawon lokaci, kuma shekara nawa aka yi a wannan tsakanin?

HAFSATU: Gaskiya ban san yawan shekarun ba, amma ina da littattafan da ma a rubuce; bugawa ne kawai ba a yi ba, saboda yanayin yadda babu kuɗin da mutum zai buga ɗin.

SHEME: Wani abu da mu ka yi la’akari da shi shi ne, a matsayin ki na wacce ta soma rubuta littafin ƙirƙira a Arewa, sai ya kasance ƙwaya biyu kaɗai ki ka rubuta, ban da littattafan addini da mu ka san kin rubuta daga baya. Me ya sa ba ki rubuta littattafai da yawa ba kamar yadda sauran marubuta su kan yi?

HAFSATU (murmushi): A’a! don littattafai ina da littattafai da dama; matsalar dai yadda na gaya maka ita ce bugawa. Domin ni ina ganin in buga su da ƙarko sosai, wato abin da Bature ya ke cewa da ‘quality’, ya fi in buga su irin yadda sauran mutanen mu su ke yi da araha ɗin nan su shiga kasuwa. To, shi ne kawai matsalar da ta hana ni bugawa da yawa, su fito. Amma akwai su nan a ajiye.

SHEME: Ki na ta kukan rashin kuɗi, amma wasu za su kalle ki a matsayin attajira, saboda ’ya’yan ki manya ne; an san su na auren manyan mutane da sauran su, kuma ke ɗin ma dai babba ce. Anya za a yarda da maganar rashin kuɗin nan, na dai a buga ɗan littafi?

HAFSATU: A’a, to ai kamar nawa da na ke yi su na da tsada da yawa. Ka ga kamar wanda za a fitar wannan watan – ‘Saba Ɗan Sababi’ – na ƙirƙirarrun ƙananan labarai, abin da na biya mai bugawar shi ne N200,000 a kan kwafe 1,000 kacal. To, ka ga kuwa kuɗin ba kaɗan ba ne kenan. Kuma yara su na yin iyakar gwargwadon iyawar su, amma kowa ya na da iyali na kan su; ba za ka ɗauki nauyin da ya fi ƙarfin mutum ka ɗora masa ba, ballantana tun da baban su ya rasu. Kuma duk ba su daɗe da kawo ƙarfi ba ai, saboda ba su daɗe da gama makaranta da kama aiki ba. To, ka ga akwai matsaloli da yawa a irin wannan.

Sannan kuma kallon kuɗi da ake yi min, to alhamdu lillahi, sai in ce Allah ya ƙara min! Amma dai suna ne. Sarakuta kuma da masu kuɗi, wannan ba hujja ba ce ta mutum ya na da shi. Domin sai surukin ya bayar sannan za ka karɓa. To, saboda haka ana dai ƙoƙartawa. Yanzu dai mun yi da su za a tara duk ’yan rubuce-rubucen a tsinci wanda za a tsinta, su haɗa kuɗi su buga, wanda su ka ga ya dace da wanda za su iya.

SHEME: Yanzu kin nuna mana cewa ana aiki a kan sabon littafin ki. Shi ma na ƙirƙira ne kenan?

HAFSATU: E, na ƙirƙira ne. Wato na rubuta ƙananan labarai guda 46, waɗanda mu ka ce za mu kasa su kamar kashi uku ko huɗu. Ya danganta da dai yadda abin yake. To, kashi na farko ne zai fito; ya kamata ma a ce tun bara ya fito. To, harkar masu bugawa ɗin ce…, sai dai ya yi min alƙawari, ya ce ƙarshen watan nan idan Allah ya yarda zai fito. To, akwai kuma da yawa littattafan ai. Akwai biyu ma da Hukumar A Daidaita Sahu ta Jihar Kano su ka ɗauka za su buga, wanda na yi a kan mu’ujizojin Alƙur’ani mai girma. Sannan akwai ɗaya da na yi kan wani labari na gaskiya da na ƙirƙiro na rubuta, na sanya masa suna ‘Aibun Doka’. To, sun ɗauki waɗannan biyun za su buga.

SHEME: Akwai yiwuwar ki rubuta waƙoƙi ko wasan kwaikwayo?

HAFSATU: E to, biyu daga cikin ƙananan labaran nawa na mayar da su wasan kwaikwayo, sannan kuma ina da rubutattun waƙoƙi – amma na Turanci – da yawa, domin gaskiya na gwada rubutawa da Hausar, na kasa!

SHEME: Ashe ki kan yi rubutu da Turanci? Amma har yanzu ba a ga ko guda ɗaya ba!

HAFSATU: Wallahi ina yi, amma duk dai harkar idan aka juya ta batun dai bugawa ɗin ce. Har yanzu ban samu wanda zai ɗauki nauyin bugawar ba. Ni kuɗin ba su dame ni ba, amma dai a ce aikin ya fito, shi ne muhimmanci a wuri na, amma har yanzu ban samu wanda zai ɗauki nauyin ba. Amma na Turancin dai a kwanan nan mu ka zauna da yara mu ka tsinci waɗanda za a buga ɗin. To, ban san dai abin da su ke ciki ba dai yanzu, amma sun yi min alƙawarin za su buga, to amma ban san lokacin ba.

SHEME: Me ya sa kamfanin Gaskiya Corporation ko NNPC Zariya ba su buga littattafan ki da yawa ba, musamman tunda a wancan lokacin su na cikin aikin buga littattafai da yawa, ba kamar yadda daga baya su ka durƙushe ba?

HAFSATU: Wallahi ni dai abin da su ka gaya min shi ne ba su da kuɗi. Duk dai magana guda ce a lokacin da na kai masu nawa guda biyu, waɗanda har da ma na ‘Dare Dubu Da Ɗaya’ da na rubuta yadda yara za su iya karantawa, saboda na farkon nan bai kamata yara ƙanana su karanta shi ba. To, na rubuta daga na 1 zuwa na 5 kamar yadda aka yi shi na Hausa ɗin nan. Har yanzu ma kwafin ya na hannun su, ba su dawo min da shi ba, don sun ce min yanzu su na ‘yan shirye-shiryen soma buge-bugen littattafai.

SHEME: Yaya ki ke ganin harkar wallafa a Arewa?

HAFSATU: To, gaskiya abin ya na da ciwo. Kuma duk a wasu taruka da aka yi na marubuta na kan bayar da shawarar cewa su kan su marubutan su na da laifi, saboda za a iya haɗin gwiwa, a saka ‘yan kuɗaɗe; kowa ya bayar da gudunmuwar sa, a haɗa kuɗin nan a ajiye. Idan marubuci ya rubuta littafi a duba, idan ya cancanta a buga shi, sai a ɗauki nauyin bugawar. In ya so bayan an buga, an sayar ko an ƙaddamar, abin da aka sayar, sai a mayar a ajiye. Kuma nan gaba sai a sake samun wani ya yi. Amma duk shawarwarori na da na ke bayarwa, har yanzu babu wacce ta samu shiga.

SHEME: Ita gwamnati da masu hannu da shuni fa?

HAFSATU: To, gwamnati dai ba ta san da zaman marubuta ba, sai dai kwanan nan da ake ta abubuwan nan na ga gwamnatin Neja ta ɗauki nauyi. To, kuma gwamnatin mu ma ta Jihar Zamfara ta yi alƙawarin za ta buɗe mana wani asusu wanda idan an yi littafi, a bincika shi a gani; idan ya cancanta, a buga. Sai mu yi fatan sauran gwamnoni za su yi koyi da su.

SHEME: Wane kira za ki yi ga marubuta waɗanda ke kasa fito da littattafan su, har ma wani sai ya yi fushi ya daina?

HAFSATU: Bai kamata mutum ya yi fushi ya daina ba, domin idan Allah ya ba ka basira, ka daina amfani da ita, kamar ka yi masa butulci ne. Shi kuma rubutu ko da mutum ba shi da rai ya na da amfani. Kamar yadda mu ka ga littattafan Shehu da Asma’u ɗaruruwan shekaru ga su nan yanzu ana morar su. Saboda haka kada mutum ya bari. Kada rashin bugawar nan ya karya masa gwiwa; ya yi ta rubutun ya na ajiyewa har Allah ya kawo wanda zai zo ya buga masa. Saboda komai ya na da lokaci. Idan lokacin abu bai yi ba, babu yadda za a yi ka tilasta lokacin ya yi.

SHEME: To, Hajiya, mun gode, ƙwarai.

HAFSATU: To, madalla. Ni ma na gode.

(An ciro daga mujallar Fim ta watan Yuni 2008)

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *