GASAR N300,000 GA MARUBUTAN HAUSA

AN dad’e ba a samu tagomashi a fagen rubutun Hausa ba, musamman na k’irk’ira. An bar marubuta kowa tasa ta fisshe shi. Hakan yana tattare da matsaloli da dama, ta yadda littattafan mu sun kasance cikin k’ask’anci, babu inganci, kuma babu k’ok’arin kawo sabon abu. Idan ba a yi wankiyar finafinan Indiya da na Turawa da na ’yan Kudu ba, to kuwa za a d’auki littattafan su a fassara, a sata, a ce na Hausa ne.

To, da alama zamanin ci-gaba ya fara kunno kai a fagen rubutu. Wata mata da ke zaune a Abuja, kuma babbar ma’aikaciyar gwamnatin tarayya, ta d’auki nauyin shirya gasar rubuta littattafan Hausa daga bana, kuma za ta ba da zunzurutun kud’i har naira dubu d’ari uku (N300,000) ga zakarun gasar a kowace shekara.

Wannan mata dai sunan ta Hajiya Bilkisu Abdulmalik Bashir, kuma ita ce Babbar Sakatare ta Hukumar Kula da Aikin Shari’a ta Tarayya (Executive Secretary, National Judicial Service Commission). Ta d’auki nauyin gasar, abin da a Turance ake kira endowment, a dalilin son tunawa da mijin ta, wanda Allah ya yi wa rasuwa a ran 18 ga Oktoba, 2006. Mijin nata dai shi ne Injiniya Bashir K’araye, wanda ya tab’a zama Kwamishinan Albarkatun Ruwa na Jihar Kano, sa’annan ya tab’a zama Kwamishinan Yad’a Labarai, Matasa da Al’adu da Wasanni na jihar. Can a baya kuma ya tab’a zama shugaban Hukumar Muhalli ta Jihar Kano.

Rasuwar Injiniya Bashir ta girgiza iyalan sa da masoyan sa matuk’a, musamman da yake ta zo ne ba zato ba tsammani; cikin awoyi kad’an ya kwanta ciwo, kafin ka ce kwabo ya ce ga garin ku. Shekarun sa 56 a duniya.

A ranar Talatar nan da ta wuce, Hajiya Bilkisu ta fad’a wa membobin K’ungiyar Marubuta ta Nijeriya (Association of Nigerian Authors, ANA), reshen Babban Birnin Tarayya, da manema labarai, a ofishin ta a Abuja cewa marigayin mutum ne mai k’aunar harkar adabi da inganta harshen Hausa matuk’a. Don haka abin alfahari ne da farin ciki a gare ta a ce ta karrama shi ta hanyar saka gasar rubuce-rubucen Hausa da sunan sa.

Sunan wannan gasa dai Engineer Bashir K’araye Memorial Prize in Hausa Literature.

K’ungiyar ANA reshen Abuja, a k’ark’ashin jagorancin shugaban ta, Dakta Emman Usman Shehu, ita ce ta rubuta wa Hajiya Bilkisu takarda, ta buk’ace ta da ta d’auki nauyin gasar bayan sun fahimci cewa a shirye take da ta karrama marigayi ta kowace kyakkyawar hanya. Wani ma’aikacin hukumar, Inyamiri, mai suna Mista Patrick Oguejiofor, wanda shi ma marubuci ne, shi ne ya yi wa ’yan k’ungiyar hanya ya sada su da Hajiya har wannan al’amari ya tabbata.

A ranar Talatar makon jiya, an taru ne a ofishin Babbar Sakataren domin a k’addamar da fara wannan gasa. ’Ya’yan ANA a wurin sun had’a da shi Dakta Shehu da sakataren k’ungiya Mista Kanico da lauya Ahmed Maiwada da Mista Oguojifor da kuma Ibrahim Sheme, wanda ya tab’a zama sakataren yad’a labarai na k’asa na k’ungiyar ANA.

Ba wani shagali aka yi ba. An dai yi bayanai da kuma mik’a takardun da ke nuna cewa Hajiya ta d’auki nauyin wannan gasa.

Hajiya Bilkisu ta ce Mista Oguojifor ne ya ba ta k’warin gwiwa ta d’auki nauyin shirya gasar. Ta ce duk da yake ita ba marubuciya ba ce kuma ba ta samu isassshen lokacin karanta littattafai a yanzu, a shirye take ta yi dukkan abin da ya dace don tunowa da Injiniya Bashir. Ta ce, “Na kuma samu k’arin farin ciki da na ji cewa ba ku da wani wanda ya d’auki nauyin shirya gasa don hab’aka adabin Hausa. Sai na ga wannan babbar dama ce a gare ni in taimaka a hab’aka Hausa, wato harshen da shi (Injiniya Bashir) yake matuk’ar so.”

Ta k’ara da cewa Hausa harshe ne mai albarka. “Na yi mamaki da na ji cewa wai babu wani wanda ya d’auki nauyin hab’aka shi ta irin wannan hanyar. To, na yi murna da cewa ina daga cikin wad’anda za su taimaka wajen d’aukar nauyi irin wannan.”

A wajen amsa tambayoyin da ’yan jarida suka yi mata, Hajiya Bilkisu ta bayyana cewa ita kan ta dai ba Bahaushiya ba ce (an ce ’yar Jihar Kogi ce), to amma tana da kishin Hausa matuk’a, kuma mijin ta ya sha ba ta k’warin gwiwa wajen fahimtar harshen. Ta ce, “Duk da yake ni ba k’wararriya ba ce wajen magana da Hausa, amma dai na iya Hausa sosai.”

Cikin alhini, har ta kusa fashewa da kuka, Hajiya Bilkisu ta k’ara da cewa Injiniya Bashir mutum ne mai son karanta Hausa, kuma ya kan ba iyalan sa – daga matan sa har ’ya’yan sa – k’warin gwiwar su rik’a amfani da harshen. “Na tabbatar kowa da kowa (a gidan) zai ji dad’in cewa za a iya yin wani abu wanda marigayi ke so ko da bayan ran sa,” inji ta. “Shi ba marubuci ba ne, amma yana son inganta harkar rubutu. Duk wad’annan abubuwan su ne suka ba ni tunanin cewa lallai ya kamata in yi wannan abu.”

A yanzu dai ba a bayar da sanarwar fara gasar ba. To amma shugaban ANA na Abuja, Dakta Shehu, ya d’an nuna yadda gasar za ta kasance. Na farko dai k’ungiyar za ta zauna ta fito da k’a’idojin gasar, sannan za ta nad’a alk’alan gasar; za a bayar da sanarwa a kafafen yad’a labarai ana kira ga marubuta da su shiga gasar. Ya ce za a shigar da littattafan hikaya wad’anda aka buga su daga shekaru biyar da suka gabata zuwa yanzu a gasar. A cikin littattafan, za a zab’i guda uku a matsayin zakaru, za a shirya k’warya-k’waryar walima a Abuja wajen watan Nuwamba mai zuwa inda za a mik’a wa zakaru kyautar da suka ci ta wad’annan kud’i da za a karkasa masu.

“A bana, za mu fara ne da littattafan hikaya,” inji Dakta Shehu, “sannan a bad’i za mu saka gasar rubutattun wak’ok’i, sannan a shekara ta gaba kuma za mu yi gasar wasan kwaikwayo.”

“Muna kuma fatan fito da wasu abubuwan da za su k’awata gasar,” inji shi.

Wakilin mu ya fahimci cewa idan Hajiya Bilkisu ta ba da mak’udan kud’in shirya gasar, za a saka su a wani asusu na musamman a banki, inda a duk shekara za a ciri _300, 000 na zakaru, kuma akwai yiwuwar cewa kud’in za su k’aru a nan gaba.

Marubuta sun yi farin ciki da wannan abu da ya faru. Dakta Emman Shehu ya bayyana cewa wannan ba k’aramin k’ok’ari ba ne Hajiya Bilkisu ta yi.

Shi ma tsohon shugaban k’ungiyar ANA reshen Jihar Kano, wanda kuma fitaccen marubuci ne kuma malami a Jami’ar Bayero ta Kano, wato Dakta Yusuf Muhammad Adamu, ya yaba da k’ok’arin da Hajiya Bilkisu ta yi. A hirar da ya yi da Leadership Hausa shekaranjiya, malamin ya ce an jima ba a samu irin wannan lagwada ba a fagen rubutu “duk da k’ok’arin da muka sha yi na neman wanda zai d’auki nauyin irin wannan gasa.”

Ya yaba wa k’ungiyar ANA ta Abuja saboda hob’b’asan da suka yi na samun wannan taimako ga marubuta. Ya yi nuni da cewa shirya gasar zai ba da gagarumar gudunmawa ga k’ok’arin da ake yi na inganta rubutun Hausa.

Dakta Yusuf Adamu ya kuma ba da shawarar cewa ya kamata a d’auki alk’alan da suka dace don yin hukunci a gasar, ya ce “kada a d’auki wad’anda suke da wani ra’ayi na son rai.” Ya kawo misali da malamai a jami’o’in Bayero, A.B.U. Zariya da kuma Danfodiyo Sakkwato, wad’anda suka jima suna koyar da adabi tare da yin nazarin sa. Ya ce kuma a had’a da tsofaffin marubuta maza da mata don a tabbatar da adalci a gasar.

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *