Damina ta iso Kano

Allah mai iko! A yau dai an kwarara ruwan sama na farko a birnin Kano. An soma ruwan ne jim kadan bayan magariba kuma an yi shi har zuwa wajen bayan isha’i. Ni kai na na sha dukan ruwan duk da yake a mota na ke (na bar gidan su marubuciya Maryam Ali Ali tare da aboki na Isiaka Aliagan, wanda ya wallafa mata littafin ta na “Faces of Naira,” na tafi in kai shi Unguwa Uku shi da wani kanen sa. Tilas ta sa mu ka rika bude gilashin motar, ruwa na dan shigowa).

Kai! Amma dai mazauna birnin Dabo sun sha zafi a cikin ‘yan kwanakin nan. Har ina cewa rabo na da jin zafin gari irin na bana, an dad’e! Kusan kowa a Kano addu’a ya ke yi Allah ya kawo ruwan sama. Kuma an shafe kwanaki da dama mu na jin labarin cewa an yi ruwa a gari kaza ko a gari kaza (misali, an yi ruwa mai yawa a Kaduna jiya). A Kano, da kyar mutum ke iya yin barci da dare saboda matsanancin zafi. Wani aboki na marubuci cewa ya yi shi dai duk da yake ba mai son esi ba ne, to amma zai yi kokari ya sayi esi don magance wannan d’an karen zafi da ake yi. Ni ma a yau da rana, lokacin da na ke cin abinci, na fad’a wa maidaki na cewa, “Sam ba na jin dadin cin abinci cikin ‘yan kwanakin nan, duk na yi losing appetite. Na kan dai ci abinci ne kamar wani patient!”

Wani abin mamaki shi ne, Kano ta samu sanyin yanayi sosai. A yanzu haka da na ke wannan rubutun, ina d’an yin rawar d’ari. Ina jin ba zan ma iya barci ba sai na d’an sha shayi. Dan’adam kenan! Allah ba ya iya masa! Sai ka ce ba ‘yan awoyi kadan da su ka gabata ba ne mu ke kukan zafi, yanzu kuma za mu fara kukan sanyi ya yi yawa! Allah, ka gafarce mu.

Ko banza dai a yau mutum zai kwanta ya yi barci a cikin sakewa. Kila har da minshari da tattake mayafi.

Ya Allah! Yadda mu ka ga farkon wannan damina, Ka sa mu ga karshen ta lafiya, amin. Ka sa wannan damina ta kasance mai albarka ga kasar mu baki day, amin.

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *