Daga ‘Mace Mutum,’ Sai Me?

Fitacciyar marubuciya Rahma A. Majid ta yi mani bayani kan sakamakon da ta gani bayan fitar jibgegen littafin ta a kasuwa. Ina ta sa gaba yanzu?

KWANAN nan ne fitacciyar marubuciyar nan Rahma Abdul Majid ta fitar da sabon littafin ta mai suna ‘Mace Mutum.’ Ƙaton littafi ne, domin rabon ka da ganin littafin hikaya mai yawan shafukan sa tun ‘Ƙarshen Alewa Ƙasa’ na marigayi Bature Gagare; shafi 520 ne, don haka ya ma fi ‘Ƙarshen Alewa Ƙasa’ yawa kenan.

Jigon littafin shi ne yadda ba a yi wa mata adalci a zamantakewar yau da kulluma a ƙasar Hausa, saboda irin danniyar da maza ke yi masu.

Mun tattauna da marubuciyar kan littafin, da kuma inda ta sa gaba bayan fitar sa. Bismillan ku:

IBRAHIM SHEME: Kwanan nan littafin ki, ‘Mace Mutum,’ ya shiga duniya. Yaya ki ka ga karɓuwar sa a wurin jama’a?

RAHMA A. MAJID: Alhamdu lillah wa shukrallah! Gaskiya batun karɓuwar wannan littafi sai godiya ga Maiduka, domin kamar yadda mu ka zata littafi mai yawan shafuka da yawan farashi kasuwar sa na tafiya ne a hankali, don haka ne ma a lokacin da na ke ganawa da wasu cikin dilolin mu na yi ta yi masu matashiya kan yadda za su jure wa wannan kasuwa mai tafiyar hawainiya. Amma cikin ikon Allah sai ga shi littafi a satin farko an soma neman sa a wasu guraren, ya ƙare. Sannan ina mai tabbatar maka da har yau bai gama karaɗe inda ake neman sa ba saboda saurin tafiyar da ya yi a wasu wuraren da aka fara ƙaddamar da shi. Gaskiya makaranta sun yi rawar gani, sai godiya gare su da Ubangijin mu.

SHEME: Ba a taɓa yin littafin hikaya na Hausa wanda farashin sa ya kai yawan na ‘Mace Mutum’ ba. To akwai tsoro a zukatun marubutan Hausa cewa wai idan marubuci ya “tsuga” kuɗi, ba za a saya ba. Ke ya abin ya shafe ki?

RAHMA: Kamar yadda na gaya maka a tambayar farko, ni da kai na ina cikin masu irin wannan tsoro, musamman ma da na lura da cewa mafiya yawan makaranta matan cikin gida ne, sannan ga littafin ya yi kuɗin wata atamfar biki, don haka na zaci kowa ya zo saye zai ce ya yi tsada, amma sai ga shi mafi yawa na cewa ai ma ya yi arha. Wataƙila wannan ne ya sanya wasu dilolin su ka dinga zabga kuɗi bayan da su ka fahimci cewa za a saye shi a ko nawa ne. Don zan iya tunawa cewa an kawo min kukan an sayi littafin a Gombe kan farashi N1,500, saɓanin kuɗin bai-ɗaya da ake sayar da shi, N820.

SHEME: Jigon littafin ya ta’allaƙa ne kan wahalhalun da mata ke sha a ƙauyuka da birane, ta yadda har a kan ga cewa kamar mace ba bil’adama ba ce. Ki na ganin matan Hausawa sun shirya karɓar wannan saƙon?

RAHMA: E, daga yadda na ke hange ko fata, matan mu na Hausawa za su so karɓar saƙon littafin, sai dai ba zan yi wa kai na alƙawarin cin karo da zafafan ƙalubale ba, ba ma daga maza ba har matan da ake yi wa yaƙin. Domin bayan na kammala rubutun ‘Mace Mutum,’ na lura da cewa akwai dubban mata da su ka fi gwammace wa rayuwar da mu ke yaƙa fiye da wadda mu ke son ganin su a ciki. Wannan ba zai rasa nasaba da imanin su kan maganar nan mai cewa bayan wuya sai daɗi ba. Don haka ‘Mace Mutum’ na iya samun karɓuwa ko tirjiya daga waɗanda ake abin domin su.

SHEME: Shin ki na ganin cewa kin fice daga ƙangin “adabin kasuwar Kano”, ko har yanzu ki na ciki?

RAHMA: Da cewa ka yi na fita ko ina cikin adabin kasuwar Kano? da na ce ina ciki, domin ba na ƙyamar adabin wanda shi ya haife ni ni da alƙalami na. Amma tun da ƙangi ka ce, ina jin zan iya cewa na kama hanyar fita daga ƙangin ci-baya da adabin namu ke fama da shi. Kamar yadda hasashe ya nuna, marubuta da dama sun yunƙuro don ficewa daga wannan ƙangi. Kada ka manta, daga cikin littattafan da su ka ci gasar Abuja akwai adabin kasuwar Kano, wanda hakan ba ƙaramin ci-gaba ba ne ga wannan adabi ba. Don haka ina jin wannan adabi da kan sa ya na jajibirin ficewa daga ƙangin da ya samu kan sa ba ma mu ’ya’yan sa kawai ba.

SHEME: Shin wannan littafi ƙirƙira ne gaba ɗaya ko kuwa akwai wasu sassa da ki ka ɗauko kai-tsaye daga rayuwar zahiri taki ko ta wasu mutane da ki ka yi bincike a kan su?

RAHMA: Labarin ‘Mace Mutum’ ƙagagge ne, sai dai halin da mata ke ciki a wannan littafi gaskiya ne, don haka labarin na iya yin saurin kama da rayuwar wata ko wasu gungun mata.

SHEME: Littafin ya fito da kurakurai na ɗab’i inda za ki ga wasu shafukan babu rubutu ko kuma wasu kwafen littafin ba a yanke gefe-gefen ba. Me ya faru?

RAHMA: Lallai an samu matsaloli wajen aikin wannan littafi. Ina ga wannan bai zai rasa nasaba da gaggawar da mu ka yi a kusan ƙarshen aikin ba, domin a yayin da mu ka zaƙu da mu biya haƙƙin masu jiran wannan littafi da su ke ta sauraro su na ƙorafi kan daɗewar sa bai je kasuwa ba. Amma cikin ikon Allah mun shawo kan kashi 90 cikin ɗari na wannan matsala domin mun bi kasuwa mun karɓi mafi akasarin waɗannan littattafai da su ka samu matsala don a mai da su kamfani a sake masu aiki. A halin yanzu akwai aƙalla kwafe 288 da aka dawo mana da su don mu sake mai da su cikin mahaifiya.

SHEME: Bayan ‘Mace Mutum,’ sai me kuma zai biyo baya? A wata hira da ki ka taɓa yi da mujallar Fim a cikin 2005 kin nuna cewa za ki riƙa fitar da littafi makamancin wannan aƙalla guda ɗaya a shekara. To, za mu sa ran ganin wani littafin nan da 2009 kenan?

RAHMA: Lallai zan iya tuna wannan alƙawari nawa a can baya, kuma ina da niyyar tabbatar da shi, sai dai kowa na nasa Allah na nasa. Dubi ‘Mace Mutum,’ tun 2005 ake fama da matsalar da ba ta fi ƙarfin mu ba, amma har sai da ya kai 2008. Don haka in har na kasa cika wannan alƙawari sai na yi fatan samun uzuri daga makaranta don sanin ba da niyya ba ne.

SHEME: Wane kira za ki yi ga marubuta kan batun yin littafi mai inganci, mai yawan shafuka, mai jigon da ba na soyayya ba, da sauran su?

RAHMA: A kullum kira na ga takwarori na kuma ’yan’uwa na marubuta shi ne mu daina tunanin abin da za mu kashe da wanda za mu samu a wannan aiki, domin muddin za mu riƙe wannan tunani ba za mu iya yin aiki mai inganci ba. A ƙasa irin tamu babu abu mai riba kamar abu mara inganci, don haka in fa mu ka zaɓi inganci dole mu ajiye tunanin riba, ita ce kan sanya mu jin babu wani jigo ga labari sai wanda kwastamomin mu su ka zaɓa. Sannan mu tuna iya zubi da salo wajen bayar da labari na iya jan hankalin makaranci, ba sai jigo ba. Don haka kada mu ji tsoron zaɓen jigo kowane iri muddin mun iya zubi da salo.

Sannan batun yawan shafuka, kada wani ya ga ‘Mace Mutum’ ya je ya takura kan sa da cewa sai ya haɗa labari mai yawa ko da ba ma’ana sai surutu da maimaici. Kada mu manta, ingancin labari da ma’ana ya fi yawan shafuka amfani.

Don haka kira na a nan shi ne in za a yi littafi mai yawan shafukan a tabbatar yawan mai amfani ne ba haihuwar yuyuyu ba. Sannan mu sani, akwai bambanci tsakanin yawan labari mai amfani da ƙarami mara amfani. Akwai wasu littattafai da mu ke yi da ba su fi shafi arba’in ba, ba wai don labarin ba zai iya kaiwa shafi ɗari biyu ko ɗari uku in an buɗa shi ba sai don tsoron yawan kuɗin aiki da ƙarancin riba. Mu tuna, bai wa labarin haƙƙin sa na cika shi shi ma wata riba ce. Allah ya sa mu dace.

——————–

An buga wannan hirar a mujallar Fim ta watan Afrilu 2008, shafi na 60-61. Haka kuma an taɓa buga wata cikakkiyar hirar da na yi da Rahma A. Majid kan littafin ‘Mace Mutum’ a mujallar Fim ta Nuwamba 2005 da Disamba 2005.

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *