Ashe Narambad’a Bai Mutu Ba!
Wani manazarcin adabin Hausa ya na nan ya duk’ufa kan tattara kammalallen tarihi da wak’ok’in d’aya daga cikin shahararrun makad’an Hausa, wato marigayi Ibrahim Narambad’a Duk wanda ya san abin da ake kira “wak’ar Hausa,” to ya san Makad’a Ibrahim Narambad’a. Hasali ma dai akwai muhawara k’wak’k’wara kan waye ya fi fasaha tsakanin Narambad’a da …