Hausa Write-ups

Alh. Muhammadu Gambo Fagada (Gambu)

Tudu Tsoho: Tunawa da Gambu Mai Waƙar Ɓarayi

A yau ne Alhaji Muhammadu Gambo Fagada (wanda ake kira Gambu Mai Waƙar Ɓarayi) ya cika shekara biyar da rasuwa. Ya rasu a ranar 18/8/2016 ya na da shekara 67 a duniya. Domin tunawa da shi a daidai wannan rana, na rubuto baitukan farko na ɗaya daga cikin manyan waƙoƙin sa daga faifai, wato waƙar …

Tudu Tsoho: Tunawa da Gambu Mai Waƙar Ɓarayi Read More »

Alhaji Garba Bichi tare da Ibrahim Sheme

Yau shekara 21: Tunawa da Garban Bichi da Shata

A YAU, 24 ga Satumba, 2020 Alhaji Garba Bichi, MON, ya cika shekara 21 da rasuwa. Fitaccen ɗan kasuwa ne, mutumin garin Bichi ta Jihar Kano. Duk da yake sanannen mutum ne a harkar kasuwanci da kuma taimakon jama’a, waƙar da Alhaji Mamman Shata ya yi masa a cikin 1972 da taken ‘Haji Garban Bichi …

Yau shekara 21: Tunawa da Garban Bichi da Shata Read More »

Alhaji Bawa Ɗan'anace ya na rera waƙar Shago

Taken Shago Wanda Makaɗa Bawa Ɗan’anace Gandi Ya Yi Masa

Wannan waƙa na ɗaya daga cikin waƙoƙin Ɗan’anace waɗanda su ka sa na haƙƙaƙe da cewa har ƙasa ta naɗe babu makaɗin dambe irin shi. Ko ita kaɗai ya rera, ta isa ta ɗar ma sa’a! Saboda ita kaɗai, ni idan mutum ya ce akwai makaɗin dambe da ya zarce Ɗan’anace sai in ji kamar …

Taken Shago Wanda Makaɗa Bawa Ɗan’anace Gandi Ya Yi Masa Read More »

Kyaftin Adamu Suwa Ɗanbaba

‘Saja-Manja Adamun Panshin’ – Shekara 50 Bayan Rasuwar Kyaftin Ɗanbaba

A rana irin ta yau a cikin 1969, wato 24 ga Satumba, Allah ya ɗau ran Kyaftin Adamu Suwa Ɗanbaba, wanda aka fi sani da suna Samanja Adamun Pankshin saboda fitacciyar waƙar da Alhaji Mamman Shata ya rera masa mai taken ‘Saja-Manja Adamun Panshin”. Wataƙila masu bibiya ta a Facebook za su tuna da cewar …

‘Saja-Manja Adamun Panshin’ – Shekara 50 Bayan Rasuwar Kyaftin Ɗanbaba Read More »

Sabuwar Dokar Cire Ko Saka Kuɗi A Banki

Na lura akwai rashin fahimta game da sabuwar ƙa’idar cire kuɗi ko saka kuɗi a banki wadda Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya fito da ita kwanaki kaɗan da su ka gabata. Mutane sun yi ta yaɗa labarin ƙanzon kurege game da dokar. To, Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya yi bayani a Twitter kan sabon tsarin …

Sabuwar Dokar Cire Ko Saka Kuɗi A Banki Read More »

Alhaji Hassan Wayam Maikukuma

Taƙaitaccen Tarihin Alhaji Hassan Wayam Maikukuma

An haifi Alhaji Hassan Wayam a wani gari mai suna Gwadda, wanda kuma ake kira Bakin Ruba, a ƙasar Maradun ta Jihar Zamfara, a cikin 1956. Mahaifin sa, Mal. Muhammadu, Babarbare ne. Mahaifiyar sa, Halima, Bafulatana ce. Sana’ar mahaifin ita ce sassaƙa, amma wani lokaci ya kan yi wa Fulani kiɗan kotso jefi-jefi. Ya na …

Taƙaitaccen Tarihin Alhaji Hassan Wayam Maikukuma Read More »