Bilkin Sambo ta Mamman Shata!

Ana yi wa Dakta Mamman Shata kirargamsu

“Sarkin waƙar Kanawa,
Duna na Bilkin Sambo.
Warga-wargan namiji

Mai ɗaci kamar guna…”

Wai shin Bilkin Sambo, matar sa ce, ko kuma ƙanwar sa ce? Kuma meye tsakanin su da Yalwa? Wannan ita ce tambayar da Fatuhu Mustapha ya yi a Majalisar Marubuta kwanan nan. Ni kuma na ba shi amsa kamar haka:

Malam Fatuhu,
Lallai ka yi tambaya ga ɗan gida.
Tambayoyin ka su ne:
1. Wai shin Bilkin Sambo, matar Shata ce, ko kuma ƙanwar sa ce?

2. Kuma meye tsakanin su da Yalwa?

BILKIN SAMBO

Wata mata ce a garin Funtuwa, Jihar Katsina, wato garin da Shata ya yi rayuwar sa, inda iyalin sa su ke. A farkon zuwan Shata Funtuwa, bayan ya taso daga Bakori (wanda shi ma gari ne kusa da Funtuwa) sai su ka shaƙu da Alhaji Nagoya, wani ɗan kasuwa mai cinikin auduga. Nagoya ya ɗauki Shata kamar ɗan sa. Don haka ne ya haɗa shi da wasu ‘ya’yan sa biyu mata, Indon Dutsen Reme da ƙanwar ta Bilki.

Akwai kuma Sambo, wanda shi ne babban ɗan Nagoya ɗin. Sa’ilin da duk aka yi haihuwa a gidan Alhaji Nagoya, ya kan kirawo Shata ya ce, “Ga uwargida!” ko “ga ubangida na yi maka!” Da aka haifi Bilki, Shata ya na makaɗin gidan, sai maigidan ya ce masa, “To ga sabuwar uwargida na yi maka.” Daga nan ne ita Bilki, wadda a kan kira Bilkin Sambo, ta zama Bilkin Shata, sa’annan shi ma Shata ana ce masa Na-Bilkin Sambo (har maroƙan sa su kan yi masa kirari da “Mai tambura Na-Bilkin Sambo!”).

Abin mamaki, Shata bai yi Bilki waƙa ba (a iya sani na), amma kuma ya waƙe Indo da waƙar “Indon Dutsen Reme Lambawan.” A yanzu ita Indo ta na auren Magajin Garin Musawa, Alhaji Abdullahi Inde. Ita kuma Hajiya Bilki, ta na nan da ran ta a Funtuwa, inda ta yi aure har ta hayayyafa. Ga hoton ta nan tare da ɗan ta (amma tsohon hoto ne, domin na ke jin kila ma wannan yaron ya girme ka!)

2. YALWA

Akwai Yalwa guda biyu a rayuwar Shata. Ta farkon ita ce ƙanwar sa mai bi masa, wadda ta rasu tun tuni. A garin su Musawa ta yi aure, har ta haifi ɗa wanda ake kira Umbaje (ka san ana yi wa Shata kirari ana cewa “Uban Umbaje”).

Yalwa ta biyu kuma ita ce Hajiya Yalwa Bature, wadda matar sa ce da ya fi so a rayuwar sa. Sun daɗe da rabuwa, har ta auri wani yaron sa a harkar roƙo, wato Alhaji Bature Sarkin Magana (wanda shi ma ya daɗe da rasuwa, tun kafin Shata ya rasu). Hajiya Yalwa ta na nan zaune a Kaduna tare da ‘ya’yan ta, cikin su har da ‘ya’yan da su ka haifa da Shata (Umma, matar Kanar Bala Mande wanda ya taɓa yin gwamna a zamanin Abacha, kuma ya yi ministan Obasanjo), da Bilkisu Shata wadda ɗaliba ce a fagen Political Science a Jami’ar Abuja, da kuma Nura).

Da ka ji ana kiran Shata, “Shata na Yalwa”, to ƙanwar sa ɗin nan ake nufi, ba matar ba, domin tun kafin ya auri Yalwa ake ce masa hakan.

Da fatan ka gamsu.

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *