Bikin ƙona littattafai a Kano

Jami’an gwamnatin Kano tare da Sarkin Kano Ado Bayero su na cinna wa tarin littattafan Hausa wuta (Hoto: Ado Ahmad Gidan Dabino)

Kamar mako biyu da su ka gabata na je sayen jaridu a bakin Post Office na Kano, sai na ga babban labarin jaridar SUNDAY TRIUMPH ta ranar ya na cewa Gwamnatin Jihar Kano ta yi bikin ƙona littattafan Hausa a wata makarantar sakandare ta ‘yan mata. Na sayi jaridar saboda wannan labarin, a matsayi na na marubuci.

Hukumar A Daidaita Sahu ta Jihar Kano, wadda ke aikin tsaftace halayyar al’umma, ita ce ta shirya bikin ƙona littattafan. Kuma Gwamnan Kano da Sarkin Kano duk sun halarta.

Washegari, mun tattauna al’amarin da Dr Yusuf Adamu, wanda ya ce ya aika da saƙon rashin amincewa da wannan matakin ga shugaban A Daidaita Sahu ɗin, wato Malam Bala Muhammad. Daga bisani, mun kuma tattauna al’amarin da wasu marubutan, waɗanda su ka haɗa da Maje El-Hajeej Hotoro.

Ita hukumar ta ce ta ƙona littattafan ne saboda a ganin ta su na gurɓata tarbiyyar yara, musamman ‘yan makaranta, domin akwai batsa a cikin su. Kada a manta, hukumar ta taɓa shirya taron marubutan Hausa na zamani da ke Kano, a otal ɗin Tiga, aka yi musu jawabai kan al’amarin adabi. Tare da haɗin gwiwar Ƙungiyar Marubuta ta Nijeriya (ANA) reshen Jihar Kano, aka yi taron. An kuma biya marubutan ladar rubuta wasu ƙananan littattafai a bisa ruhin adabin da A Daidaita Sahu ta ke son a riƙa rubutawa. Tuni aka buga littattafan, aka raba su.

Shin ƙona littattafan ya dace? Me hakan zai haifar a nan gaba? Shin ya kamata marubuta su goyi bayan ƙona littattafai ko kuma su nuna rashin amincewa?

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *