Bayan Shekara 27: Me Ya Sa Aka Manta Da Abubakar Imam?

A bana, littafin Magana Jari Ce, wanda Alhaji Abubakar Imam ya rubuta, ya cika shekara 80 cif da wallafawa. Sannan a jiya Alhamis, 19 ga Yuni, 2008 Imam, wanda shi ne kakan marubutan Hausa, ya cika shekara 27 da rasuwa. Wannan sharhin ya na yi mana hannun-ka-mai-sanda kan yadda mutane su ka yi watsi da juyayin Imam da ayyukan sa, ciki kuwa har da wad’anda nauyin yin ayyukan tunawa da Imam da karrama shi ya fi rataya a wuyan su.

A wata ranar Asabar a cikin shekara ta 2004, na yi wani sharhi kan marigayi Alhaji Abubakar Imam, ya fito a filn adabi na jaridar Weekly Trust, wanda na ke gabatarwa a lokacin. Sharhin, kwaskwarima ne na wani sharhin da na tab’a yi a Majalisar Marubuta ta Intanet, inda na nuna cewa ba a yi wa Alhaji Imam adalci ba wajen ayyukan tunawa da shi, musamman a hanyoyin sadarwa na zamani. Na yi nuni da cewa idan mutum ya yi amfani da na’urar Google ta intanet, zai gano cewa babu wurare da dama da aka ambaci wannan hazik’i, fasihi, kakan marubutan Hausa a intanet. Har na ce idan a misali ka kwatanta Imam da ni d’in nan Ibrahim Sheme, za ka taras da cewa an ambace ni a intanet sau ninkin baninkin fiye da Imam – ga shi kuwa ni ba kowan kowa ba ne a fagen adabin Hausa, idan ana maganar gagarau irin su Imam!
Na d’ora laifin a kan mutanen da ya kamata a ce sun karrama Imam, sun tabbatar da cewa ya na da cikakken wakilci a yanar gizo da duk wani dandali da ya kamata a ji amon sunan sa. Wad’annan mutane sun had’a da marubutan Hausa, da malaman makarantu tun daga firamare har zuwa jami’a, da su kan su iyalan marigayin.

Shi dai Imam, haifaffen Kagara ne a Jihar Neja. An haife shi a 1911. Asalin asalin sa Babarbare ne, amma kakan kakan sa ya yi hijira zuwa k’asar Kwantagora, daga nan ya tafi Sakkwato a zamanin Shehu Usmanu D’anfodiyo, ya zauna a k’ark’ashin Shehu. A can aka haifi mahaifin Imam, wato Malam Shehu Usman, wanda daga baya ya dawo Kagara bayan ya yi yawon malanta a k’asar Katsina da ta Kano.

Imam ya yi makaranta a Katsina, inda daga bisani ya zama malamin makaranta. A nan ne ya had’u da Dakta R.M. East, Baturen nan jami’in ilmi wanda ya jagorance shi wajen rubuta wasu daga cikin littattafan sa, ciki har da Magana Jari Ce da kuma K’aramin Sani K’uk’umi. Har ila yau Imam shi ne editan Hausa na farko na jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo. Ya rasu a ranar Juma’a, 19 ga Yuni, 1981 a Zariya, ya na da shekara 70 a duniya. Ya bar matar sa d’aya, da ’ya’ya 14, da kuma jikoki 42.

Imam ya kasance jagaba a harkar rubuce-rubucen hikaya na Hausa, ta yadda a yau da wuya a ce ga wanda ya fi shi. To amma ban da rubutu, ya na daga cikin ’yan kishin k’asa na farko da su ka nemi mulkin kan Nijeriya daga hannun Turawa ’yan mulkin mallaka. Haka kuma ya taka rawa k’warai a harkokin addinin Musulunci.

Rasuwar Imam ta gigita jama’a, musamman saboda gagarumar gudunmawar da ya bayar a fagage da dama na rayuwar jama’ar Arewa. Tun daga lokacin da ya mutu ake ta tunanin hanyoyin da za a bi a karrama shi, a rik’a tunawa da shi a kai a kai. Abin mamaki, har yanzu ba a gama tunanin ba, don haka ba a yi wani abin kirki a kan haka d’in ba – shekaru 27 bayan rasuwar sa!

Sakamakon rubutun da na yi a Weekly Trust, wanda babban k’alubale ne a gare mu duka mu masu hank’oron son Imam, an samu yunk’uri mai alfanu daga wasu sassa. A Jami’ar Bayero ta Kano, Farfesa Abdalla Uba Adamu ya yi wuf ya k’irk’iri dandalin tattaunawa (chat group) kan Imam a intanet, wanda ya sa wa suna [email protected] An samu membobi a wannan dandali, to amma yawan su bai taka kara ya karya ba.

Yunk’uri mafi girma da aka samu na karrama Imam ya fito ne daga iyalan sa. Sun kira mutanen da abin ya shafa, ciki har da Farfesa Abdalla da Dakta Ibrahim Malumfashi na Jami’ar Usmanu D’anfodiyo da kuma ni. Shi Malumfashi, ya yi digirin sa na dakta ne a kan rubuce-rubucen Imam kuma tun tuni ya nad’a kan sa Sarkin Yak’in Imam a fagage da dama. To amma a yayin da mu ka amsa gayyatar iyalan Imam mu ka je Zariya wurin taro na farko don tattauna hanyoyin da za a bi a karrama Imam, a ranar 29 ga Agusta, 2004, Malumfashi k’in zuwa ya yi. Bai kuma aika da sak’on uzuri ba. Zargin da mu ke da shi shi ne, adawar da ya ke yi da wasu daga cikin mu ce ta hana shi zuwa. A gani na, ya na ganin cewa tun da ba shawarar sa ba ce tun farko, ba zai shiga ciki ba. Ka ji halin Bahaushe – mai ban haushi, na Tanko mai kan bashi!

Duk da haka, taron ya yi albarka. Akwai dattawa da dama a taron, kuma yawancin ’ya’yan Imam maza, da wasu jikokin sa, duk sun halarta. An tattauna kan hanyoyin da za a bi a karrama marubucin, musamman ma yadda za a sa a rik’a jin amon sunan sa a k’asar nan kwatankwacin yadda ake jin na gwaraza irin su Janar Murtala da Janar Yar’Adua.

Bayan wannan taron, an sake yin wasu tarurrukan a wasu ranakun. A k’arshe, an yi abubuwa biyu. Na d’aya, an gina gidan yana a intanet mai suna www.abubakarimam.com, wanda Dakta Haroun Adamu, mamallakin makarantar nan Zaria Academy, ya d’auki nauyin gina shi. Wani masanin intanet da bai dad’e da dawowa daga Amerika ba inda ya yi tsawon shekaru, wato Malam Salisu U. D’anyaro, shi ya yi gidan yanar kuma ya ke gudanar da ita. Na biyu, an kafa cibiyar tunawa da Imam, wadda a Turance za a iya kiran ta Abubakar Imam Documentation Centre. Ta na cikin wani gidan sama da ke kallon randabawul na Babban Dodo a Zariya.

A yayin da gidan yanar ya ke d’auke da tarihin Imam da rubuce-rubucen sa, a ita cibiyar kuma an adana wasu kayan tarihi da su ka jib’inci marubucin, ciki har da samfurin rubutun sa na hannu, da takardun sa, da littattafan sa, da lambon girma da ya samu, da hotunan sa, kai har ma da rigunan sa!

Wad’annan abubuwa uku, babu shakka, manyan hanyoyi ne na karrama Imam. To amma a yau, idan na waiwaya baya, sai in ga ai ba su isa ba. Kuma ma tuni an yi watsi da su. Na farko, dandalin tattaunawar da Malam Abdalla ya bud’e a intanet, bai hab’aka ba. Mutane k’alilan ne a ciki. Kuma babu sak’wanni a kai a kai a ciki. Don haka dandalin bai cimma nasarar bud’e shi. Mai yiwuwa dalilin shi ne saboda Malam Abdalla ya gina wani dandalin tun da fari mai suna [email protected] wanda ya shafe na Imam d’in. Yawancin marubuta ma ba su san da dandalin Imam d’in ba.
Ta b’angaren gidan yanar da Malam Salisu D’anyaro ke gudanarwa kuwa, ya yi kyau k’warai, domin hatta littattafan Imam za ka iya sauko da su kyauta. Sai ai ya kamata a ce ana saka sababbin abubuwa a cikin sa, kamar labaran marubuta da mak’aloli kan harkar rubutun Hausa. Kafin a yi hakan tilas sai an samu ’yan rahoto ko marubuta da za su rik’a aikawa da sak’wannin da za a rubuta.

amma mu “ninanci” (kamar yadda Malam Abdalla ke cewa) ya yi mana tarnak’i. “In ba ni na yi abu ba, babu wanda ya isa ya yi shi,” ko kuma “Wane ai ba fagen nazarin sa ba ne wannan, da har zai zo ya na yi mana shiga-sharo-ba-shanu.”

Mu sani cewa idan fa ba mu karrama gwarzayen mu da kan mu ba, babu wanda zai karrama ma mana su. Su dai sun taka rawar su sun tafi, sun bar mu a fagen. Don haka, hak’k’in tunawa da su ya rataya a wuyan mu, ba a wuyan kowa ba. Kamar yadda marigayi Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato ya tab’a fad’a, idan har ba mu buga tambarin kirakin kan mu ba, babu wani bare da zai zo ya buga mana shi. Kukan kurciya jawabi ne, mai hankali ke ganewa!

—–
An buga wannan sharhin a jaridar LEADERSHIP HAUSA ta ranar Juma’a, 20 ga Yuni 2008.

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *