Bashir Sanda, sabon jagoran tace finafinai a Zamfara

Gwamnatin Jihar Zamfara ta nada sabon Babban Shugaba (wato Executive Chairman) na sabuwar Hukumar Tace Finafinai da Dab’i ta Jihar Zamfara. Wanda aka nadan shi ne wani abokin mu, marubuci, mai suna Alhaji Bashir Sanda Gusau.

Wasun ku za su tuno da cewa Bashir marubucin littattafan hikaya ne, wadanda su ka hada da “Auren Zamani.” To kuma ya k’ware a fagen aikin jarida, inda har ya kai matsayin Manajan Darakta a kamfanin jarida mallakar jihar su, wato “The Weekly Legacy.”

Can kwanan baya Gwamna Mahmud Aliyu Shinkafi (MAS) ya tsige Bashir a kan dalilin wai ya yi rubutu a jaridar inda ya soki Shugaban Kasa Yar’Adua. Hakan ya bakanta ran ‘ya’yan kungiyar mu ta editocin Nijeriya (wato Nigerian Guild of Editors) inda mu ke ganin an yi haka ne don a hana Bashir fadin albarkacin bakin sa.

To yanzu dai Gwamna MAS ya gane kuskuren sa, ya dawo da Bashir a jikin sa, ya dora shi kan sabuwar kujera. Sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Mamman Bawa Gusau, shi ne ya sa hannu a takardar nad’in Malam Bashir. To, addu’ar mu ita ce: Allah Ya taya riko, kuma Ya kad’e fitina, sannan Ya hana sabon shugaba aikata duk wani nau’i na zaluntar bayin Allah, amin summa amin.

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *