Ashe Narambad’a Bai Mutu Ba!

Wani manazarcin adabin Hausa ya na nan ya duk’ufa kan tattara kammalallen tarihi da wak’ok’in d’aya daga cikin shahararrun makad’an Hausa, wato marigayi Ibrahim Narambad’a

Duk wanda ya san abin da ake kira “wak’ar Hausa,” to ya san Makad’a Ibrahim Narambad’a. Hasali ma dai akwai muhawara k’wak’k’wara kan waye ya fi fasaha tsakanin Narambad’a da marigayi Alhaji Mamman Shata. Yayin da wasu ke cewa Shata ya fi Narambad’a yawan wak’ok’i ne kurum amma Narambad’a ya fi zalak’a da fasaha, wasu na cewa ai shi Shata ya kere Narambad’a, musamman da yake shi wak’ok’in sa kowa zai iya fahimtar su – Basakkwace da wanda ba Basakkwace ko Bazamfare ba.

A bara, wasu matasa sun k’addamar da kammalallen tarihin Shata, wanda hakan ya k’ara taimakawa wajen fahimtar ko waye mawak’in. Shi kuwa Narambad’a, yawancin wad’anda suka san shi, sanin shanu suka yi masa. Kuma yawancin Hausawa sukan kasa gane wasu kalamai na wak’ok’in sa, musamman wad’anda ba su fito daga tsohon yankin k’asar Sakkwato ba. Bugu da k’ari, in ban da tak’aitaccen tarihin sa da Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau na Jami’ar Bayero ta Kano ya rubuta a littafin sa Makad’a Da Mawak’an Hausa, ba kowa ba ne zai ce maka ya san tarihin wannan fasihin mawak’in.

To, yanzu dai an taki sa’a, domin kuwa aiki ya yi nisa wajen tattara kammalallen tarihin Narambad’a. Kuma sai aikin ya fad’a a hannun d’an gida, wanda ya san kan al’amarin, wato Farfesa Aliyu Bunza.

Shi dai Farfesa Bunza, fitaccen manazarci ne a k’asar Hausa. Ya yi rubuce-rubuce kan adabi da kuma al’adun Hausawa, har ma da wasu wak’ok’i na baka da kuma rubutattu. A yanzu shi ne ke rubuta tarihin Makad’a Narambad’a.
Shin yaya wannan aiki nasa yake ciki? A ranar Lahadi da ta wuce, an yi hira da Farfesa Bunza, wanda babban malami ne a Jami’ar Usmanu D’anfodiyo da ke Sakkwato, a sashen Hausa na gidan rediyon BBC. Wakilan gidan rediyon sun zanta da shi lokacin da ya je London kwanan nan. Mu a an Leadershi Hausa mun kalato muku wasu muhimman bayanai daga cikin wannan zantawa tasu ta musamman kan aikin da yake yi na rubuta tarihi da wak’ok’in marigayi Alhaji Ibrahim Narambad’a.

Tun da farko sun sako wak’ar Narambad’a mai taken, “Masu gari mazan gabas tsayayye, Sarkin Rwahi ya wuce a ram mai.” Idan kun tuna, a wannan wak’ar ce makad’in ke cewa, “Ga wani d’an sarki da kunnuwa da hwad’i…”

An tambayi Malam Bunza ya fad’i wani abu kan wak’ar. Sai ya amsa, “Sarki ne aka wa wak’ai na Kuryar Dambo, ba Kurya ta Madaro ba. Ma’ana, kurya guda biyu muke da su a Zamfara: akwai wannan Kurya ta Madaro, akwai waccan Kuryar Dambo. To hakimin Kuryar Dambo ne ya ka wa wak’a. Kuma wannan cewa ‘Da takobi da garkuwa da yak’i,’ daga cikin k’a’idar nazarin wak’a, “lugude” muke kiran sa, luguden tarihi. Wani tarihi ne ya narke wurin, tarihin wani sarkin d’an tauri ne da aka yi a Kurya mai suna Mamman Ina, da ya kashe wani Bature. To shi ya sa ya ke cewa ‘Kurya akwai mazan hwad’a da arna.’

BBC: Abin da ya sa na yi maka wannan wak’a, a da a Zariya idan muka ji wannan wak’a akwai wani gari Kauru a kusa da Zariya, mun d’auka shi ake wa wak’ar da ya ke cewa Makauru. Ashe ba Kauru ba ne. Wai me ake cewa ne a wurin? Ka san wani d’an sark’e-sark’e ne.

BUNZA: Ai da yake cewa ya ke yi, “Ai Kurya ta Dambo ta Makauru an nan, / Zamfara babu makaye kama tai.”

BBC: Za mu so ka d’an ba mu tarihin Narambad’a, watak’ila mutanen zamani ba su san ko wanene ba.

BUNZA: Marigayi Narambad’a shahararren mawak’i ne a duniya. Kuma idan za a yi tarihin Ibrahim Narambad’a, bisa k’a’idar ilmi sai an wa mutane da yawa tambaya wad’anda suka gabace ni a cikin wannan fagen, kamar Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau, ya yi bincike musamman a kan Narambad’a; Bello Sodangi ya yi bincike musamman a kan Narambad’a; Sama’ila Yawuri Mazawaje shi ma ya yi bincike musamman a kan Narambad’a.

To sunan Narambad’a na yanka Ibrahim. Sunan uban sa Maidangwale, shi kuma Maidangwale mutumin Nijar ne, cikakken d’an kokawa ne. Amma Narambad’a ya gaji kid’i wajen uwar sa. Don haka shi karen makad’a ne kenan. Uban sa bai yi kid’i ba. An haife shi a garin Tubali, ya yi karatu a nan, ya rayu a nan, ya tashi a matsayin ba d’an gadon wak’a ba. Ya iske kayan kotson kid’in kakan sa na wajen uwa a d’akin mahaifiyar sa. Mahaifin sa mutumin k’asar Filinge ne, ya zo a garin Tubali, ya auri uwar Narambad’a. Kuma ga shi shahararren d’an kokawa ne.

Sai Narambad’a ya d’auki kayan kid’in mahaifin sa ya fara kid’an noma. To, wata shekara a fadar Sarkin Gobir na Isa ya yi kid’in noman k’auyen su. Da jin yadda dad’in wak’a ya ke da zalak’a da k’warewa, suka ce ya fi k’arfin k’auye, sai aka mai da shi birni. Ya tashi daga mawak’in noma ya koma makad’in Gobir. Ka ji tarihin zuwan sa.

BBC: Wato wannan ne kenan ya sa ya koma makad’i na fad’a, na sarakuna.

BUNZA: Gaba d’aya saboda an ga hikimar ta hi k’arhin ta manomi, dole sai an maida shi fada. Don haka ya dawo ya ci gaba da yi wa Amadu Sarkin Gobir wak’a.

(BBC sun sako wak’ar “Ya ci maza ya kwan yana shiri, uban zakara, dodo na Ummaru”)

BBC: To Farfesa Bunza, me za ka ce dangane da wannan wak’a?

BUNZA: Wannan wak’a ta Sarkin Gobir ta na cikin manya-manyan wak’ok’in da ya yi masa. Kuma wannan wak’a ce wasu suke ganin gabanin Narambad’a ya yi Bakandamiyar wak’ar sa. Don a ciki har Narambad’a na cewa duk abin da zai fad’a ga Sarkin Gobir daidai ne, ba kure ba ne:

“Na aje k’arya ko ina kid’i,
Na bar k’arya ko ina kid’i,
Nai sittin, saba’in ni ka hwad’a,
Mai saba’in yai k’arya ana ta zund’e nai,
Ko yaran da ag garai duw wawwatse mashi su kai,
Ya na yawo shi d’ai baram-baram.”

Saboda haka a cikin wannan wak’ar ba mu zaton mu ji abin da ya sab’a wa gaskiya. Don haka ne mu ke ganin wannan wak’a ta Sarkin Gobir na cikin manyan wak’ok’in sa. Amma dab baya da yai Bakandamiya, sai ta shahe hasken ta.

(BBC sun sako wak’ar “Batun da akai na yau babu Sarki yau irin ka,/ Jikan Bello arna suna shakkak ka”)

BBC: Farfesa, ko wanda bai san Narambad’a ba, ya san mutum ne wanda Allah ya ba basira. To amma kuma kamar yadda kowa ya sani, akwai shahararrun mawak’a wad’anda su ma sun yi suna. Ko dai kamar Narambad’an ko kusa da shi. Me ya sa ka d’auki Narambad’a a matsayin wanda za ka yi bincike akai?

BUNZA: Akwai dalilai da yawa. Na farko shi ne, fitattun mawak’an Hausa da mu ke da su k’asar Hausa an fara bincike a kan su – ko bincike ne na jami’a, ko ma na gida ne, duk dai an yi. Shata an yi aiki a kan sa. Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau ya yi bincike kan Salihu Jankid’i. To, na ke ganin a dukkanin k’asar Zamfara ba a yi mawak’in da ya kai Narambad’a ba. Kuma ba a k’asar sa kawai ya ke wak’a ba. Ma’ana, duk duniyar k’asar Hausa. Amma abin takaici, idan an zo neman wak’ok’i nai babu, sun wawwatse, ba a samun su.

Ba a san tarihin sa ba, ba a san ina ya hito ba, ba a san hikimar sa da zalak’ar sa ba. Sai na ga ya na da kyau a yi wani aiki da ak’alla zai fito da shi, zai fito da falsafar sa, zai fito da wak’ok’in sa, da wad’anda ya yi wa wak’ok’in, shi ma ya kasance wani taska daga cikin taskar adabin Hausa da za a aje.

BBC: Ban tari numfashin ka ba. Wasu kalmomi da Narambad’a ke amfani da su a cikin wak’ok’in sa, idan ba fassara wa mutum aka yi ba, ba a fahimtar abin da ya ke fad’i. Ina ganin wannan ma ya na da mahimmanci a yi irin wannan bayani da ka yi. To zuwa yanzu ka rubuta wak’ok’in sa guda nawa?

BUNZA: Sai dai in ce na samu wak’ok’i guda nawa? In na samo su sai in rubuta su…

BBC: Ban tari numfashin ka ba, rubutawar ka na rubuta duk abin da aka ce a cikin wak’a?

BUNZA: E, zan yi k’ok’ari duk abin da ya ce, zan yi k’ok’ari in rubuta kuma a irin lafazin da ya fad’a. Kamar Sarkin Rafi, ai Sarkin Rwahi ya ke cewa. Ni ma Rwahi zan rubuta.

BBC: Wak’ok’i nawa ka samu zuwa yanzu?

BUNZA: Wasu su kan ce ya yi wak’ok’i sun kai d’ari ko d’ari da wani abu, amma iyakar binciken da mu ka yi, kusan sama da shekaru ashirin da wani abu, gaskiya ni hamsin na samu, wad’anda na rubuta da kai na, na saurara, na tabbatar sun rubutu, na ajiye.

BBC: Wad’anda aka d’auke su da faifai kenan?

BUNZA: Ma’ana, shahararrun wak’ok’in da aka sani a kaset, ba dab bakin wani aka ji su aka rubuta ba.

BBC: Dangane da wak’ok’i ko mawak’an Hausa, kamar Alhaji Mamman Shata ana cewa ya na tsayawa nan take ya yi wak’a, don an sha gwada shi, ba tare da ya zauna ya shirya ta ba. Shin Narambad’a ya yake tsara wak’ok’in sa?

BUNZA: Wato ko wane irin mawak’i da irin fasaha da hikima da zalak’a da Allah ya hore masa. Allah ya hore masa wak’a, amma shi (Narambad’a) ba a nan take ya ke yin ta ba. Idan zai yi maka wak’a, zai je gida ya tsara ta; a yinin da zai yi wak’ar, ba zai yi huld’a da kowa ba. Haka wasu yaran sa su ka shaida mana. In ya k’are tsara ta, sai ya kira yaran sa, sai su rera. Wak’ar Narambad’a in zai yi ta, zuba wak’a ake zube-ban-k’warya.

BBC: Kamar yadda ya ce ta Alfazazi…

BUNZA: Cewa ya yi:

“Kullum ji ni kai azanci na hudo min,
Sai zuba wak’a ni kai kama da ta Alfazazi.”

BBC: Rubutawa ya ke yi?

BUNZA: Narambad’a ba ya rubuta wak’a, sai ya samu gindin wak’a ya fara. Da ya k’are abi nai cikin zuciya, sai ya kira yara nai ya ce, “To, ga amshin wak’a kaza,” su rik’a yi a sannu ana maimaitawa. Sai ya k’are sai aje a yi ta.

BBC: Wak’ar Alk’ali Abu fa? Shin wanene Alk’ali Abu d’in nan?

BUNZA: Alk’ali Abu asali mutumin K’auran Namoda ne, alk’alanci ya kai shi Moriki, kuma daga cikin ’ya’yan sa akwai wanda ke raye a Sokoto yanzu. Amma dai zuri’ar na can a K’aura. Ba Alk’ali Abubakar Mahmud Gumi ba ne kamar yadda mutane su ke zato. Ya yi masa wannan wak’a a kan irin adalcin sa, gogewar sa da sanin shari’a.

(BBC sun sako wak’ar “Alk’alin Alk’alai ta aiki nai da tsari…”)

BBC: To amma akwai inda yake cewa “Narambad’a ba ya zuwa lahira…,” kamar ya bugi k’irji…

BUNZA: Ya ce ko ya je dawowa ya kai. Ya na da hujja a wannan wurin. Sai an kamo kan wak’ar za a gane me ya sa ba zai je lahira ba! Ya ce:

“Hwad’awa ku bugan in buge ku
Mui ta fad’an mu gidan duniya,
Kun san ba a hwad’a lahira,
Kun san ku ka zuwa lahira,
Narambad’a ba ya zuwa lahira,
Ko ya je dawowa ya kai,
Gama kun san d’auke mai akai.”

Maganar sa ta tabbata: fadawa ke mutuwa; da bafade ya mutu, a fada an manta da shi. Da Sarki ya mutu, a fada an manta da shi, an yi wani. Amma idan zakaran mawak’a ya mutu, ba mutuwa ya yi ba. Har yanzu ga Narambad’a ba shi duniya, ana maganar sa, ana jin maganar sa. Ina fadawa su ke? Saboda haka duk wani mawak’i da ya san kan sa, ya yi luguden wak’ar, to bai mutu ba, ya na nan a raye!

BBC: To, Farfesa Aliyu Bunza, mun gode k’warai.

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *