A jiya Asabar aka cika shekara 50 da zuwa duniyar wata da ɗan’adam ya fara yi. Kumbon Apollo 11 mallakar ƙasar Amurka ya sauka a kan farin wata a ranar 20 ga Yuli, 1969.
Na ga tashoshin talbijin irin su BBC World da CNN su na gabatar da shirye-shirye a kan cika shekara hamsin da zuwa kan wata.
Tun a wancan lokacin, mawaƙan Hausa sun shiga cikin ruguntsimin maganganun da aka dinga yi kan wannan al’amari. Na farko shi ne Alhaji Mamman Shata, wanda ya shirya waƙar nan ta “Kumbo Apollo Eleven” inda ya yabi wannan nasara da ƙasar Amurka ta samu. Waƙar ta nuna cewa lallai Shata ya na “tafiya daidai zamani”, wanda hakan ne ya sa zaren sa bai tsinke ba.
Na biyu, idan kun tuna, shahararren mawaƙin nan ɗan ƙasar Nijar, marigayi Alhaji Muhamnadu Gawo Filinge, shi ma ya yi waƙa kan zuwa duniyar wata da ma binciken sararin samaniya da Amurka da Rasha ke tseren yi a lokacin. Waƙar sa, wadda raddi ce ya yi wa Shata, amshin ta shi ne “Ya Rabbi Sarki Mai Juma’a, Taimakan Mu Don Ranar Juma’a”. Dalilin waƙar shi ne kasa zuwa duniya da kumbon Apollo 13 ya yi saboda bayan an harba shi a ranar 11 ga Afrilu, 1970, tilas ya juyo ya dawo gida bayan kwana shida saboda fashewar da takin iskar oksijin ya yi a jirgin. Hakan ya faru ne watanni tara bayan nasarar Apollo 11. Gawo Filinge na ganin cewar ai ga irin ta nan, Allah ya hana su yi masa kutse a cikin sirrikan sa. A waƙar da ya yi, Filinge ya soki lamirin zuwa duniyar wata da sauraren wurare da Allah ya girke a sama. A ganin sa, kamata ya yi ɗan’adam ya zauna a inda Allah ya aje shi, ya daina karambanin shiga cikin sararin samaniya.

Amma Shata ne ya ci gari a wannan saɓanin ra’ayi na mawaƙan, domin kuwa masana kimiyya a ƙasashe da dama sun ci gaba da zurfafa bincike kan sama’u domin fahimtar yadda ta ke.
Lokacin da su Alhaji Shata su ka ziyarci Amurka a watan Mayu na shekarar 1989, sai da aka kai su wajen wannan kumbo ɗin na Apollo 11, su ka gan shi, su ka taɓa shi da hannun su.
Ga hoton Shata da na Filinge a nan, Shata ya na kallon kumbon Apollo 11, na turo su domin tunawa da wannan babbar nasara da ɗan’adam ya samu, da kuma nuni da cewa mawaƙan mu na Hausa sun taskace tarihin wannan hoɓɓasan da Amurka ta yi na harba ‘yan’adam zuwa kan farin wata.