AN SAKO IYAN-TAMA

Malamai,

Idan kun tuna, a ranar Litinin da ta wuce kotu ta sa aka kama furodusan nan Hamisu Iyan-Tama, a kan lafin wai ya k’i zuwa kotu a kan shari’ar da su ke tafkawa da Hukumar Tace Finafinai da Dab’i ta Jihar Kano. An sako shi a yau Laraba bayan lauyan sa ya rubuta takardar neman a ba da beli a karo na biyu. Wasu kuma sun ce manya ne su ka sa baki!

Shi dai Iyan-Tama, abin da mu ka ji na kusa da shi na fad’a shi ne, ko kadan bai k’i zuwa kotu ba. Hasali ma dai ya je kotun da ke Railway har karfe 12 ba su ga alkali ko lauyan gwamnati ba; sai ya wuce kotun Normansland, a can ne ya samu labarin cewa alkalin ya na kotun hanyar Airport. Sai ya tafi can. To amma kafin ya je, ashe har an kira k’arar sa, ba ya nan, sai kawai aka ba da odar a kamo shi a kan laifin wai ya karya belin da aka ba shi tun da farko.

Yanzu dai ya na nan a gidan sa. Za a koma shari’ar a ranar 20 ga Agusta.

Allah Ya kai mu, amin.

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *