Alheri danko ne…

Shekaru ka]an da su ka gabata, wani hamsha}in ]an kasuwa ]an Nijeriya ya samu ribar zunzurun ku]i har dalar Amurka biliyan ]aya a wata harkar kasuwanci da ya yi. Sai ya ]ebi rabin ku]in ya tsara rayuwar sa ta hanyar sayen kayan alatu da ajiya a asusu. A }arshe, ya na da rabi, wato dala miliyan 500. Sai ya kasance wannan mutum ya rasa yadda zai yi da wa]annan ku]i da su ka rage a hannun sa. A ganin sa, ko a banki ya aje su, ba su tsira ba; bankin na iya rugujewa ko kuma gwamnati ta fito da wata doka da za ta iya sa ya yi asarar ku]in. Sannan wani abin ban-haushi shi ne, ’ya’yan sa za su iya yin rigima da juna kan ku]in idan ya kwanta ya mutu. {a}a tsara }a}a!

Wannan mutum dai ba wani ba ne illa Leftana-Janar Theophilus Yakubu [anjuma (ritaya), wanda ya ta~a ri}e mu}amin Hafsan Hafsoshin Rundunar Sojan Nijeriya a zamanin mulkin Janar Olusegun Obasanjo daga 1976 zuwa 1979. Ya yi ritaya daga aikin soja ya na da shekara 41 kacal, lokacin da su ka mi}a mulki ga gwamnatin farar hula ta Alhaji Shehu Shagari. Bayan ya yi ritaya, sai ya shiga harkar jiragen ruwa, wadda a cikin ta Allah Ya tarfa wa garin sa nono, ya ku]ance.

A lokacin da Janar Sani Abacha ya ke shugaban }asa ne ya ba T.Y. [anjuma kadadar man fetur a Fatakwal, Jihar Ribas, shi kuma ya shiga aikin ha}a a filin, aka yi rijiya. A }arshe, bayan shekara goma sai aka samu ]imbin man fetur a wannan rijiya. Da T.Y. [anjuma ya ga haka, sannan ga fetur ya na tsada a kasuwar duniya, sai ya yi dabara, ya yi wuf ya sayar da rijiyar ga wani kamfanin }asar waje. Aka biya shi ku]in da ya wazgi wannan ribar ta dala biliyan 1 da na ke magana.

T.Y. [anjuma ya saba da samun ku]i; hasali ma dai biloniya ne a naira, to amma sai da ya sayar da wannan rijiyar fetur ]in sannan ya zama biloniya a dala. Kamar yadda na fa]a maku, ya rasa yadda zai yi da sauran ku]in da ya samu, wato dala biliyan 500. To, da ya ke Allah Ya yi shi mai hangen nesa, sai ya yanke shawarar kafa wata cibiya don taimakon jama’a. Tashin farko, ya ba cibiyar zunzurutun ku]i har dala miliyan 100.

A wata hira da aka yi da shi a jarida a bana, Janar [anjuma ya ce dalilin sa na yin haka shi ne babu yadda za a yi gwamnati, “komai kyakkyawan nufin ta, ta magance dukkan matsalolin jama’a ita ka]ai. A gaskiya, a dukkan }asashen da su ka ci gaba, yi wa jama’a aikin kyautata rayuwa bai ta~a kasancewa aikin gwamnati ita ka]ai ba; a koyaushe ana yin ha]in gwiwa ne da kamfanoni masu zaman kan su.”

T.Y. [anjuma, wanda ya ta~a ri}e mu}amin Ministan Tsaro a lokacin gwamnatin Cif Obasanjo, tsakanin 1999 da 2003, mutum ne da ya kamata a ce mai daskararriyar zuciya ne, maras tausayi, ba domin komai ba sai saboda shi soja ne wanda har ya}i ya yi a lokacin ya}in basasar Nijeriya. To amma sai ga shi ya kafa cibiya mai suna T.Y. [anjuma Foundation (mai gidan yana kamar haka a intanet: www.tydanjumafoundation.org) wadda ta sa ya kasance ]aya daga cikin manyan masu taimakon marasa }arfi a }asar nan. Manufar wannan cibiya tasa ita ce ta “agaza wa yun}urin gina Nijeriya inda kowane ]an }asa zai samu ingantaccen kiwon lafiya, ilimi da dama daidai wa daida wajen cin moriyar rayuwa.” Cibiyar ta na aikin hai}an, musamman a jihar su shi T.Y. ]in, wato Taraba, har ma da sauran wurare, a kan wannan manufar tata. Ta na aiki a ~angarorin kiwon lafiya, samar da aikin yi ga matasa da kuma harkar ilimi. Ta na yin aikin ne tare da ha]in gwiwa da wasu }ungiyoyi masu zaman kan su don warware matsalolin da su ka addabi jama’ar yankin. Wani aboki na da ya ziyarci ]aya daga cikin asibitocin da cibiyar [anjuma ]in ke ]aukar nauyi ya fa]a mani irin aikin ban-mamakin da ake yi wa jama’a a wajen. Ya ce har aikin fi]a likitoci ke yi wa majinyata a wurin, kuma kyauta. Sannan idan yau ka je Jami’ar Jihar Nasarawa da ke Keffi ka ga aikin da cibiyar ta yi, sai ka ri}e baki.

Mu kula, ba fa T.Y. [anjuma ka]ai ba ne ya ta~a samun }azamar riba daga wata harkar kasuwanci a }asar nan. Hasali ma dai, ’yan kasuwa da dama su na soke irin wannan ribar a aljihun su, su yi ta cin duniyar su da tsinke har }arshen ran su, ba tare da sun yi tunanin taimaka wa talakawa ba. Kafin mutum ya yi tunanin yin abin da T.Y. ya yi, sai ya kasance mai halayya tagari, mai gwarzantaka, da tausayi da yin amanna da yanayin da mu ke ciki, da kuma yin aiki da fasaha.

Kyautata wa jama’a ya na daga cikin manyan ayyukan gwarzantaka da ke nuna cewa mutum, mutum ne. Kafin ka yi kyauta, sai ka kasance ka yi }arfin halin yarda da rabuwa da wani abu da ka ke muradi, musamman ku]i ko dukiya. Kyautatawa kuma mutunci ce. Shi ya sa ba wanda zai iya yin ta sai mai jin }an ’yan’uwan sa mutane, wanda ya fahimci cewa sauran jama’a sun fi shi kasancewa cikin hali na bu}ata. Sai wanda ya gane bu}atar da ke akwai ta inganta rayuwar al’umma, wanda ya yarda da magance matsalolin da su ka yi wa duniyar mu katutu, zai iya motsawa don yin abin da ya dace.

Kyautata wa jama’a kuma aikin addini ne. Kafin ka yi tunanin taimakon wani mabu}aci, sai ka yi amanna da cewa haka Allah da Manzo su ka ce a yi. Har sai ka yarda da cewa haka ya dace a yi, tare da cikakkiyar yarda da cewa idan har an yi abin da ya dace a yi, to za a warkar da damuwar wani mutum, a sa shi ya yi murmushi don murna.

Kyautata wa jama’a fa fasaha ce. Fasaha ce ta sauke kan ka daga wata }ololuwa da ka ke a kai a cikin al’umma, ka yarda da cewa kai ba kowan kowa ba ne, domin fa ko me ka tara a duniyar nan wata rana sai dai labarin ka, ka tafi ka bar shi. Sai ka yi fasahar cewa ka yarda dukiyar ka za ta ragu idan ka cire wani abu, ka]an ko mai yawa, daga ciki ka kyautar da shi ga wani mabu}aci. A wannan fasahar, ka na kuma kambama kan ka, domin fa ka zama babban yaya ga mabu}ata, mai shau}in taimakon su.

Wannan duniya tamu ta zama tamkar wata dokar daji inda mai }arfi ke la}ume maras }arfi. A irin wannan duniya, ba kowa ba ne ke da irin halayen na da mu ka lissafa a sama. Wannan ne ya sa ake da }arancin mutane masu taimakon marasa }arfi a yawancin al’ummomin bil’adama. Mu a nan arewacin Nijeriya, a yayin da mu ke da ]imbin gajiyayyu da fa}irai, sai kuma ya kasance masu bayarwar sun yi ka]an. Yankin mu inda fatara ta yi katutu ya na bu}atar agaji a sassa daban-daban, kamar su ~angaren kiwon lafiya, ilimi, aikin yi, al’adu, da sauran su. Saboda haka a duk lokacin da ka ji wasu mutane su na yin ho~~asa don inganta rayuwar al’umma, tilas ne ka ji ka na son cira masu hula.

T.Y. [anjuma, wanda ]an shekara 72 ne a yau, a yi nisa wajen taimakon jama’a domin Allah Ya ba shi zuciyar yin hakan. In da ya ga dama, to da ba za mu ta~a sanin yadda ya ke samun ku]i ba. Ba mu san yadda wa]anda su ka fi shi ku]i su ke samun ku]in su ba, ballantana kuma yadda su ke kashe ku]in. Don haka, maganar ba ma ta yawan ku]in da mutum ya mallaka ba ne, a’a magana ce ta niyyar taimakawa da kuma alherin da taimakon ke jawowa.

Mu a nan }asar, idan mutum ya yi maganar taimakon jama’a ta hanyar kafa cibiya ta musamman don hakan, yawanci akan tuno da Turawa masu wannan halayyar ne, irin su Bill Gates, Ba’amurken nan wanda ya kafa cibiyar Bill & Melinda Gates Foundation, wadda ta fi kowace cibiyar agajin jama’a mai zaman kan ta girma a duniya. Shi Bill da matar sa Melinda Gates ne su ka kafa cibiyar, kuma su ka ba da dala biliyan 33 da rabi gare ta don inganta kiwon lafiya da kuma rage fatara a duniya. Akwai kuma attajirin nan Warren Buffet. Ko fitaccen mawa}i mai suna Bono. Ko kuma mawa}in nan marigayi Michael Jackson wanda ya rabar da yawancin dukiyar sa ga }ungiyoyi har 39 masu taimakon gajiyayyu kafin ya mutu. To, mu ma yanzu ga su T.Y. [anjuma nan sun fito da zummar taimakon jama’a.

’Yan Nijeriya dai mutane ne masu son addini sosai, don haka sun yarda da yin sadaka daga abin da Allah Ya hore masu. Za ka iya ganin haka in ka je masallatai da majami’u, ko wurin bikin saukar karatu ko taron }ungiyar tsofaffin ]alibai. Akwai kuma ]imbin masu ba da kyauta ko sadaka wa]anda ke yi a ~oye ba tare da son a yayata ba. To amma akwai masu ba da kyauta don kawai a gani a yabe su, wato kyautar ganin ido don cimma wata manufa ta siyasa ko ta wani abin daban. Irin wa]annan, ba a jimawa sai ka ji an daina labarin su, sun ~ace ko sama ko }asa.

Yanzu akwai bu}atar a kafa }ungiyoyin agaji, su kasance kamar manyan kamfanoni a }asar nan. Ya kamata masu ku]in mu su kafa cibiyoyi irin ta T.Y. [anjuma. Shin kuma ko kun lura da cewa yawancin manyan cibiyoyi irin wa]annan duk ana kafa su ne da sunan wasu tsofaffin hafsoshin soja? Kun ga dai ga Murtala Muhammed Foundation, da Shehu Musa Yar’Adua Foundation da TY [anjuma Foundation, da kuma Yakubu Gowon Foundation. Sannan kada mu manta akwai Cibiyar Inganta Harkar Shugabancin Afrika ta Janar Obasanjo (wato Africa Leadership Forum). Idan aka kafa manyan }ungiyoyin agaji kamar kamfanoni, za a samu babbar hanyar inganta rayuwar bil’adama. Kuma kamar yadda Janar [anjuma ya fa]a a makon jiya a lokacin bikin bu]e taro na farko a }asar nan kan harkar agaza wa mabu}ata, wanda cibiyar sa ta shirya, ya kamata Majalisar Tarayya ta kafa dokar da za ta saka harkar bisa turba tsararriya. Bari in }ara da cewa yin hakan zai sa a tabbatar da cewa kowace cibiya da aka kafa ta ci gaba da ]orewa har bayan rasuwar wanda ya kafa ta ]in, sannan kuma agajin da cibiyar ke bayarwa ya isa ga mabu}atan, ba kurum ma’aikatan cibiyar ko abokan su ko ’yan’uwan su ba.

Mu kan mu ya-ku-bayi, ya dace mu ci gaba da kamanta kyautatawa da taimakon mabu}ata. Ba wai sai kai attajiri ba ne. An san cewa in ka na rarar ku]i, zai taimaka maka wajen yin kyauta, to amma fa mu sani cewa wa]anda su ka fi kyauta ba su ne su ka fi kowa ku]i ba. Ka tambayi kan ka: shin ka na ba da sadaka ko ihsani da nufin agaza wa mabu}ata? Idan ka duba da kyau, kila ka gano cewa akwai wasu takalma ko tufafi a gidan ka wa]anda ba ka yi amfani da su ba a tsawon shekara ]aya. To, a zahiri fa ba ka bu}atar irin wannan kayan. Ka kyautar da su don Allah. Idan har ka na yin haka, to wata rana za ka gan ka bisa hanyar zama mai son taimakon al’umma da ma}udan ku]i kamar yadda su Janar TY [anjuma ke yi. Hausawa sun ce alheri dan}o ne, ba ya fa]uwa }asa banza. Kuma sun ce aikata alheri ga kowa, sakayyar ka ta na wurin Allah.

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *